Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Illolin da amosani ke haifarwa ga rayuwar bil'adama

Illolin da amosani ke haifarwa ga rayuwar bil'adama

 • Amosani wani irin saba ne da kan faru a fatar kai wanda yake karkashin suma. Sannan kuma ba ciwo ba ne, wato ba cuta ba ce wadda wata kwayar cuta ke iya sa wa, kamar matsalar saba ta sauran fatar jiki da wasu suke ganin kamar ciwo ne. To idan yana barbashewa za a ga fari-fari na zuba kamar gari, musamman idan an zo tace kai ko kwance kitso ko an zo yi wa mutum aski. Dubi: Sunayen wasu cututtuka daga turanci zuwa Hausa

  Duk da cewa amosani ba ciwo ba ne, to amma yana daya daga cikin abin da kan sa mutane da yawa damuwa musamman ma mata. Matsalar kan shafi kusan rabin mutanen duniya, ba bambanci a tsakanin jinsunan duniya. Wasu lokuta yakan sa kaikayi, mutum ya yi ta sosa kai, wanda wannan ma idan a cikin mutane ne sai kunya ta fara kama shi. Idan ana sosawa kuma barbashin kan biyo kai a gan shi a saman suma ko a kafada.

  Wasu na ganin cewa babu abin da zai warkar da amosanin kai, tun da ba ciwo ba ne, sai dai abin da zai rage shi. Sai dai yanayin abinci da yanayin wuri suna taimakawa wajen rage shi, haka ma man wanke kai wadanda ga su nan birjik a kasuwanni da manyan shaguna ba sai a kyamis ba. Da mutum ya je ya ce a ba shi maganin shamfo na amosani za a ba shi mai kyau. Mutane da dama sun fi ganin amfanin wani wai shi head and shoulders fiye da sauran. A mafi yawan lokuta da an fara amfani da shi za a fara ganin saukin barbashewar suma da kuma kaikayi. Ba wai hana fatar marmashewa yake ba, a’a yakan ba fata laushin da ba za a san lokacin da ta canza ba, tunda dole ne duk bayan ’yan makonni sai ta sama ta marmashe ta karkashi ta tofo. Ka ga ke nan babu tabbas din idan ka daina amfani da shi ba zai dawo ba.

  To sai dai, a wata ganawa da wakilin Bakandamiya ya yi da wani mai ba da magungunan gargajiya, wato Baba Baushe ya shaida masa cewa” Amosani na daya daga cikin abin da ba a ?auka ciwo ba amma illarsa ga rayuwar bil’adama na da yawa. Da farko muna da amosanin kai, wanda shi ne in ya yi yawa yakan sauko ya shafi ido. Da zarar ya taba ido in ya ?auki lokaci yakan makanta mutum in ba a dauki mataki ba.

  Sai na biyu kuma shi ne amosanin mara, wanda shi kuma a mara a ke samu gad a namiji in ya yi yawa yakan kashe masa ?arfi maza, sannan shi yake zame wa yaran da aka Haifa iyayensu na da shi ya haifar musu da kaikayi.

  Hanyoyin magance amosanin kai

  1. A samu tafarnuwa a daka sai a hada da ruwan lemon tsami a juya su gaurayu.
  2. A shafa a kan dake dauke da amosanin natsawon minti 30.
  3. Ruwan lemon tsami nafitar da bawo-bawon da kan taso a kai na amosani.
  4. Tafarnuwa kan yaki duk wasu kwayoyin cututtukan bacteria din dake haifar da amosanin ka.
  5. Bayan minti 30 din sai ayi amfani da man shampoo da ruwan dumi wurin wankewa.
  6. A saske samun albasa a dan daka, sannan a shafa a kai na tsawon awa daya sannan a wanke daruwan dumi.
  7. A samu ganyen darbejiya mai kyau kuma danye, a daka a shafe kan da shi bayan maganin amosani da yake yi hatta kwarkwata da sauran cututtukan da kan damu fatar kai.

  Mai karatu na iya duba: Kiwon lafiya: Bayanan kwararru kan namijin goro

Comments

0 comments