Makalu

Yadda wakokin yara ke gina tunanin rayuwar al’ummar Hausawa (na uku)

 • Fadakarwa

  Kalmar fadakarwa na nufin farkarwa ko lurarwa. Wato a lurar da mutum game da hadarin wani abu da ake ganin kila bai san da shi ba. Hausawa kan tsara waka domin fadakar da ‘yayansu a kan wani abu mai muni da ke iya faruwa gare su idan suka yi sakaci da kansu. Misalin haka a cikin wakar “Mai Nakiye” wadda ake rerawa kamar haka: 

  Amshi: Mai nakiye, Mai nakiye,

  Mai nakiye ta kofar Marke.

  Mai nakiye shigo daka dari.

  Bayarwa: Ban yarda ba, ban yarda ba,

  Ban yarda ba a lalata ni.

  Ban yarda ba a muzanta ni.

  Wanna waka gargadi ce ga yan mata musamman masu talla, ake nuna masu hanyoyin da mutanen banza kan bi su lalata su. A cikin wakar an nuna yadda ake jawo hankalin irin wadannan ‘yan mata ta hanyar Jan hankalinsu zuwa wurin da za a iya kauce wa idon Jama’a domin samun damar lalata su. sai aka nuna kada su yarda da irin haka, duk kuwa wadda ta yarda da wannan shigo-shigo ba zurfi, to karshenta a lalata ta. Wannan fadakarwa ba ga yan mata masu talla ba har ma masu karatu dasauran wasu huldodi a cikin jama’a tana fadakar da su.         

  Koyar da kimiyya

  Hausawa na amfani da waka su fara koyawa da gabatar da ilmin kimiya ga yaransu tun suna kanana. Misalin haka shi ne wata waka a cikin tatsuniya mai nuna dangantakar tsiro da ruwa da taki da dabba da kuma nuna yadda kowanensu ba y a yi sai da wani. Ga wakar:

  Yarinya:         Baure, Baure, gare ka na zo,

  Baure: Yarinya na ba ki me?

  Yarinya:         Na zo ka ba ni ya’ya,

  Baure: ‘Ya’ya ki kai ma Wa?

  Yarinya:         'Ya'ya in kai ma iya,

  Baure: Iya ta ba ki me?

  Yarinya:         Iya ta ba ni zane,

  Baure: Zane ki je ina?

  Yarinya:         In je ni wasa tsara duka sun tafi.

  Sai Baure ya nemi ta je ta kawo masa taki. Ta je wajen saniya, saniya ta nemi haki, shi kuma haki ya nemi ruwa, sai ta je ga girgiji ta samo ruwa. Duk wanda ta je wajensa sai ta rera wannan waka ya tambaye ta ta yi masa bayani kafin ya tura ta zuwa ga wani. Wannan wata koyarwa ce ga yara ta yadda za su san cewa kowane abu na samuwa ta hanyar wani abu. Misali, yaro zai san ba a samun amfani mai yawa daga tsirrai sai an saka ma shuka taki. Taki ba ya samuwa a wancan lokaci sai ta hanyar dabbobi. Dabbobi ba sa iya samar da taki sai sun ci ciyawa wadda ita ko ba ta samuwa Sai da ruwa, wadanda ke zuwa daga sama. Wannan kuwa wata kimiya ce ta dangantakar abubuwa a rayuwa ta zahiri.

  Kimiyar da yara ke iya koya daga wannan shi ne sanin cewa, kashin dabbobi shi ne abincin da tsiro zai ci ya ba da amfani. Haka ma za su koyi sanin yin kashi na da dangantaka da cin abinci, kuma abubuwa da yawa suna da danganta da juna wajen samuwarsu kamar yadda aka nuna a cikin wakar.

  Jaruntaka

  Jaruntaka ita ce aikata wani abu wanda ke buakatar sadaukar da lafiya ko ma rayuwa. Hausawa na fara koya wa ‘ya’yansu halayen jaruntaka tun suna kanana ta hanyar yan wake-waken da kan tafi tare da wasanni don ko ta-kwana. Misalin wannan shi ne wakar ‘‘Dan akuyana’. Ga yadda take:

  Bayarwa:         Dan akuyana,

  Amshi:             Damashere.

  Bayarwa:         Ya shiga rumbu,

  Amshi:             Darnashene.

  Bayarwa:         Za a kashe shi,

  Amshi:             Damashere.

  Bayarwa:         Nan da wukake,

  Amshi:             Damashere.

  Bayarwa:         Nan da takobi,

  Amshi:             Damashere.

  Bayarwa:         Nan da su adda,

  Amshi:             Damashere

  Bayarwa:         Wubub na wuce nan,

  Amshi:             Wubub na buge ka.

  Wannan wakar tana tafiya tare da wasa ne. Sai a yi da’ira yaro daya ya shiga tsakiya a rika rera ta. Yaron da ke tsakiyar ake son ya fice ba tare da sauran yaran da ke zagaye da shi sun sami damar yi masa duka ba. Zai dauki hankalinsu ne sadda ake wakar ya yi wuf ya fita. Idan ya yi sakaci a yunkurin fitarsa aka tare shi, to zai dinga shan duka har sai ya kai wani waje da aka kebe a matsayin tudun-na-tsira. Wannan koyar da yadda mutum zai iya kubutar da kansa ko da ya kasance a cikin hadarin abokan gaba.

  Shugabanci

  Bahaushe na son ya ga ya sami shugabanni masu hankali masu taka-tsantsan ga al’amarinsu musamman wajen yanke shawara. Wannan dalili ne ya sa yake kirkiro wasanni da wake-wake masu koyar da haka. Misalin wannan shi ne wasan ‘Shaburburwa”. A wasan ana yin daira ne sai yaro ya duke kai kasa ya rika shiga tsakanin ‘yan uwansa yara da nufin ya gane bagiren da ya taso. A lokacin da yake kukkurdawa tsakanin yara sai a rika  rera waka ana cewa:

  Bayarwa:         Shaburburwa,

  Amshi:             Sha.

  Bayarwa:         Kowa ya bace,

  Amshi:             Sha.

  Bayarwa:         A sha shi da kulki,

  Amshi:             Sha.

  Bayarwa:         Kulkin kira,

  Amshi:             Sha.

  Bayarwa:         Ba na aro ba,

  Amshi:            Sha.

  Bayarwa:         Ku ba shi gidanai,

  Amshi:             Sha.

  Bayarwa:         Har ya kawo,

  Amshi:             Sha.

  A lokacin da yaro ke zagaye yana kokarin   gano wurinsa, masu rera wakar suna yi masa kashedin wahalar da zai sha idan har ya bata gida. A lokaci daya kuma sai a rika zolayar sa ana gaya masa ya tashi ya iso gidansa alhali bai iso ba. Idan ya dauki zancensu ya tashi sai a rufe shi da duka.

  Wannan wakar tana koya wa yara yin taka-tsantsan ga bin shawarwarin mutane barkatai, domin ba koyaushe ne suke gaya ma mutum gaskiya ba. Wannan kuwa koya wa yara iya shugabanci ne tun da kuruciya, domin shugaba ba ya zartar da abu bisa ga ji-ta-ji-ta da shawarwarin mutane barkatai sai bayan ya sa hattara da lura.

  A gefe daya kuma tana koya masu jaruntaka, domin idan yaro ya bata za a rufe shi da duka har sai ya kai wani waje da aka ajiye a matsayin wurin tsira. Wannan na nuna idan har shugaba a bisa kuskure ya dauki shawarar da ta ba shi ruwa, to ba kwance zai yi ba, zai yi duk iya abin da zai iya ne ya ga ya sami mafita.    

  Mai karatu na iya karanta: Wakokin yara a matsayin tubalin gina tarbiyyar Hausawa (na daya) da na biyu

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All