Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Tarihin wakokin baka na Hausa da wanzuwarsu

Tarihin wakokin baka na Hausa da wanzuwarsu

 • Tarihi fanni ne wanda yake bayyana aukuwar wani abu tun wani lokaci dadadde ko makusanci da ya shude. Bin diddigin faruwar abu a dadadden zamani yakan sa a yi gamon katar da ainihin hakikaninsa, ko a samo wani rubabben tushensa, ko a sami sabani a ruwayarsa. Wakar baka dadaddiya ce wadda aka faro ta tun lokaci dadadde mai nisan gaske. Waka ta rayu tana dada bunkasa tana habaka har zuwa yau. To, sai dai da haka ne wasu masana ke hasashen asalin waka ta hanyoyi da dama kamar haka:

  Gusau, (1983)  cewa ya yi “samun asalin yadda aka fara wakar baka a kowace irin al’umma yana da wuya da kuma neman bincike mai zurfi ko kuma dawara da kai-kawon tarihi. Akwai sabanin ra’ayoyi game da asalin wakar baka a rayuwar Bahaushe. Ana jin dan’adam ya kagi waka ne tun lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar “farauta”, daga nan, da mutane suka gano “noma” sai waka ta kara habaka. Wasu kuma sukan ce hanyar bauta ta gargajiya ta dada bayar da haske wajen kyautata sha’anin waka.Dubi: Adabin gargajiya: Irei-ren wakokin baka na Hausa

  Ibrahim, (1983) daga cikin ra’ayoyin da ake bayarwa dangane da asalin waka a kasar Hausa, akwai inda ake ganin waka ta samo tushe ne daga wajen wani maroki ‘Sasana’. Domin haka, a wannan ra’ayi, ana jin makadan Hausa jikokin wannan mutum ne da ake kira Sasana wanda ya rayu a bangaren Asiya, daga baya wasu daga cikin ‘ya’yansa suka yiwo kaura zuwa kasashen Hausa. A wannan ma’ana kalmar ‘Sasana’ tana nufin ‘maroki’ da harshen Faransanci. Har wa yau, wannan ra’ayi yana karfafa cewa, Sasana shi ne mutumin da ya fara yin roko, Wato shi ne wanda ya kago roko, ya fara bude baki da nufin ya yabi wani mutum don ya ba shi samu. Shi ne maroki na farko da aka yi tun a lokacin jahilliyyar duniya. Kamar yadda aka dada ba da labarin maroki Sasana, shi ne shugaban duk wani mai dabara da hikima da fasahar roko. Ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa kasashe da yawa, bai zauna a wuri daya ba kuma ana yi wa zuriyyarsa lakabi da bani-Sasana.

  Shehu Saraki unguwar Makafi Sakkwato ya nuna kalmar ‘bani-Sasana’ tana nufin ‘maroka’ luda ya fadi haka a wata wakar sa ta bege wadda ya ari karin muryar wakar Nana Mai’alkaki ta baka ya tsara ta. Yana cewa:

  Malammai da sun ka malalo,

  Sun saki tazbaha na lilo,

  Sun koma bani-Sasana.

  Marokin Shata ma ya yarda da haka inda ya ce:

  Duna na Balkin Sambo,

  Kafiri kanen Sasana.

  A wani kaulin kuwa an dauki “Sasana” ana nufi da shi wai wani mawaki Balaraben wata kabila ta Madina mai suna Hassanu dan Thabitu wanda ya yi rayuwarsa tun lokacin jahiliyyar Larabawa har zuwa lokacin bayyanar Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Daga nan ya musulunta ya koma yana yi wa Annabin Rahama wakoki har ya zama babban mawakinsa. To, wai jikokinsa ne suka malalo suka fantsama cikin uwa duniya har suka bayyana a kasar Hausa. 

  Ibrahim, (1983) ya ce a ra’ayi na biyu dangane da asalin waka, ana cewa cikin zato “Hausawa sun sami waka ne daga wajen tsofaffin daulolin Afrika ta yamma wato Ghana da Mali da Songhai. Wannan ra’ayi yana ganin lokacin daular Mali akwai su da makadan fada, kuma suna da alaka ta kusa da makadan Hausa, musamman ma makadan fada, da daular Mali ta shude, sai daular Songhai ta maye gurbinta, sai ta gaje irin wadannan kade-kade. A lokacin mulkin Sarki Askiya Muhammadu Ture (1493-1528) ya kwarara da rikonsa har cikin wasu kasashen Hausa. Saboda haka ta nan wasu sarakunan Hausawa suka ga tsarin makadansa suka koya. Sannan za a iya duba: Yadda wakokin yara ke gina tunanin rayuwar al’ummar Hausawa (na uku)

  Ibrahim, (1983). kauli  na uku dangane da asalin waka yana cewa, “waka ta samo hasken faruwa ne daga bautar iskoki ko dodanni. Hausawa lokacin maguzanci sukan yi wa iskoki ko dodannin nan bikin cikar shekara, ko kuma idan wani abu ya faru sukan taru wajen abin bautar nan, su yi masa yanke-yanke da shaye-shaye. A wajen irin wadannan bukukuwa sukan yi wa abubuwan bautarsu zuga da kambamawa da hawar da su ta hanyar kirari ko kada take. Misali a bikin cikar shekara na lokacin Tsumburbura da Barbushe ya yi a Kano akan yi kirari kamar haka:

  Jamuna, akasa, mun gama,

  Ga Tsumburbura Kanawa,

  Ga Magajin dala.

  Barbushe yakan amsa da cewa:

  Ni ne magajin Dala,

  Da kun ki da kun so,

  Ku bi ni ba ra’i ba.

  (Ibrahim, 1982)

  Akwai kuma kirarin Dodo na ‘Kyauka” a Kwatarkwashi:

  Dodo maye,

  Dodo na ba kashi,

  Kashe mutum mu tai gida,

  Dodo na ba kashi,

  Dodo dan doguwa,

  Dodo na ba kashi,

  Birkidi ba kyakya.

  (Gusau, 1983)

  Iska Bafulatana ma tana da kirari:

  Mai gambara ina wata kama,

  Mai dan zane ta Baushe,

  Mai dan zane Iya,

  Kaluluwa ta Baushe,

  Shagidai-shagidai na gan ta,

  Mangarai-mangarai na gan ta.

  Karkatai-karkatai na gan ta.

  Dangane da wannan ra’ayi ana jin ta hasken kirari da kada taken wadannan iskoki da dodanni aka sami wanzuwar wakar  baka. Kuma ana ji daga nan ne aka sami makadan garaya na ‘yan bori (Gusau 1983).

  Amma duk da wadannan  ra ‘ayoyi da suka gabata, ana kyautata bincike cewa Hausawa sun kagi waka ne ta hanyar farauta da kirare-kirarenta. Daga nan kuma ta dada bunkasa a sakamakon noma da yake-yake. Ashe ke nan wakar baka aba ce dadaddiya wadda aka faro ta tun lokaci dadadde mai nisan gaske. Don haka, ana kyautata fahimta farauta da noma da yake-yake su ne suka haddasa samuwar waka a kasar Hausa. Dubi: Tasirin zamananci kan sutura da abincin Hausawa

  Tun lokacin da Hausawa suka fara zama waje daya cikin kungiya-kungiya da sunan kauyuka, wakar  baka ta fara ci gaba. A daidai lokacin ne aka soma yi wa sarki waka, sai dai wakokin gajeru ne kuma ba su dauke da wata fasaha ko nuna kwarewa. Irin wadannan guntayen wakoki su ma suna cikin yanayin kirari ne. Ga misalansu:

  Mata: Kai ka taka kashin-shanu,

  Miji:   Na taka kashin-shanu,

  Mata: Halan gidan da sa.

  Miji:   arki dandanin danin,

  Dan-dan dan-dan-dan,

  Sarki dan-dan-dan,

  Mata: Sarki dan zaki,

  Sarki dan zaki,

  Mata: Hayye geza ta rabki ganga,

  Miji:  Ba kidin bane.

  Geza ce ta rabki ganga,

  Lallai ba kidin bane,

  Geza ce ta rabki ganga.

  Mata: Hayye ba kidin ba ne,

  Geza ce ta rabki ganga.

  Miji:  Haba da kanta,

  Ba waka ba ce,

  ina cikin tahiya,

  Sai geza ta rabki ganga,

  Haba da kanta,

  Ba waka ba ce,

  Geza ce ta rabki ganga.

  Mata: kidin ne?

  Miji:  Haba kidin ne

  Bayan bunkasar kungiyoyi na mazaunan farko a kasar Hausa zuwa kauyuka da garuruwa da birane sai wani abu ya haddasu tsakaninsu, shi ne kuwa yaki da kai wa juna hari saboda neman fadada kasa da mulkin danniya. Sai yake-yake kabilanci suka wakana tsakanin Hausawa don son mulki da iko da shugabanci na sarakuna da sauran shugabanni ko don wata husuma ta iyakar kasa ko don wata husuma ta tsakanin ‘yan wannan kungiya da waccan, ko don wani rikici da yakan auku saboda mata da sauran dalilai.

  A sanadiyyar wadannan yake-yake da ke gudana, sai aka sami wasu mutane da ba su da karfi kwarai har da za su iya karawa da dakaru na wata kabila, amma suna da hikima da kwakwalwa. To, irin wadannan mutane ana jin su suka yi ta shirya ‘yan wasu kirare-kirare na yabon sarakunansu da zuga mazajen unguwoyinsu, don su kara zama gwarzaye kuma jarumai wadanda ake tsoron su. Wadannan mutane masu azanci da hikima sukan shirya kirari da fatar baki ne. Wani ra’ayi yana cewa makadan da suke tsara ‘yan guntayen wakoki ga sarakunan garuruwansu kafin a soma yake-yake su ne suka ci gaba da koda sarakunan nasu a fagen daga. Kafin a fita yaki ko bayan an dawo akan yi amfani da wasu kayan kida na musamman da ake kadawa don dakaru da kowa da kowa a shirya a fita fagen daga ko don a sanar da jama’a cewa an dawo daga yaki. Wadannan kayan kida da ake kadawa suna kara wa mayaka kwarin gwiwa da saka masu kuzari da karfafa musu zuciya da saka musu naciya da karfin hali da dauriya. Daga cikin kayan kidan da ake amfani da su a wurin yaki, akwai:

  1. Tambari
  2. Kurya
  3. Jauje
  4. Ganga
  5. Kuge

  Wasu kuma suna ganin a lokacin da ake kada wasu kayan kida na kidan yaki kamar tambari ko kurya, sai danma’abba ya rika yin kirari da zuga sarkinsa. Ta haka har wadannan ‘yanma’abba suka sami damar tanka ganga da nufin idan an je yaki ko an dawo daga yaki su dinga cicciba sarki da jama’arsa. Sun kara da cewa idan za a tafi wajen yaki su wadannan makada ba za a bar su a baya ba, tare da su ake tafiya. Kuma ko da yaki ya rutsa da su ba za a kashe su ba, sai dai su bi sarki wanda ya yi nasara a kansu. Dubi: Tasirin camfe-camfen Hausawa cikin tarbiyyarsu na daya

Comments

0 comments