Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Tsagar gado a al'adar Bahaushe

Tsagar gado a al'adar Bahaushe

 • Tsagar gado: ita ce wadda ake danganta ta da jinsi, musamman na wajen uba, Watau irin tsagar da muturn yake da ita za ta zama gado ga dukkan zuriyarsa. Ta hanyar tsagar gado ne za a iya fahimtar irin mazaunan wuri tare da asalinsu. Haka nan tsagar gado ka iya fayyace jinsin ma’abota wasu da ga cikin sana’oin gargajiya irin wadannan tsage-tsagen sun hada da na baka da na kunci, ko kuma ‘yan baka kawai. Sai kuma bille ko fashin goshi da dai sauransu.

  Game da adadin tsaga akan sami bambanci daga waje zuwa waje sakamakon bambancin mazauni. Wasu sukan yi tsaga shida ne, ko uku-uku a dore. Wasu kuma tara suke yi a kan kahon, kamar yadda wasu daga wanzaman sukan yi tsaga goma sha biyu yayin da suka zo yin kahon. Amma wadda ta fi karbuwa a mafiya yawan mazaunan ita ce, tsaga tara bisa tsarin gado uku-uku a sassabe. Dubi:  Ire-iren tsaga a Hahaushiyar al'ada

  Har ila yau, tsaga ce ake dangantawa da asalin gari ko jinsi na ma’abota wata sana’a don haka a iya cewa tsagar gado ta kasu kashi biyu kamar haka wato:

  1. Ta asalin gari
  2. Ta sana’a

  Ita kanta mai nuna asalin gari za a iya kasa ta zuwa gida biyu:

  • Tsaga mai nuna masarautar gari
  • Tsaga ta gama-gari:- Wato tsaga wadda da an gan ta za a iya cewa wannan mutumin gari kaza ne.

  Tsagar sarauta

  Danagane da tsagar masu sarauta akwai irinsu:

  Kutumbanci- Wannan tsaga na daya daga cikin gidajen sarautan babe a garin Kano. Tsaga ce dogaye caba-caba wadanda adadinsu yana fara wa daga takwas, ana yinsa a tsattsaye kuma har iya yadda suka samu. Kuma akwai wasu dogaye guda biyu a giciye da suka raba na kunci.

  Mallanci- Shi kuma wannan tsaga ne guda biyu wanda ake samunsa a masarautan Zazzau. Tsage ne guda biyu kuma masu fadi da ake yi a gefen ido.

  Fetali/Bille- Kamar kutunbanci da mallanci, shi ma fetali daya ne daga cikin tsagun gidajen sarautar Katsina. Wannan tsaga ce ‘yar gajeruwa ba mai kauri sosai ba wadda akan yi a kan taya-ni-muni a bangaren hagu.

  Munganci- Wannan wata ‘yar tsaga ce wadda gidan sarautar Gumel ke yi. Tsagar ana yin ta biyar a kuncin dama, hudu a kuncin hagu. Yakan fara daga tsakanin kunne zuwa gefen baki.

  Tsaga ta gama-gari

  Gobiranci- Wannan tsaga ce da ake yi wa gobirawan asali. Yadda tsagar take kuwa, akan fara daga wajen kunne a hade da gefen baki wato kamar zube kenan sai dai su akan yi shida a daya kuncin sannan a yi bakwai a daya kunci.

  Dauranci- Kamar Gobiranci ita ma tsagar Dauranci tun daga wajen kunne ake dauko ta, ta hade da gefen baki, sai dai ita kowani kunci guda bibbiyu ake yi.

  Katsinanci- Wannan tsaga mai kama da fasalin kalangu wadda wasu suka fi sani da da ‘yar  atsinanci ana yin ta a saman fuska a tsakanin ido da kunne.

  ‘Yar Gwaram- Wannan tsaga ce guda uku-uku a jere a kan taya-ni-muni mutanen gwaram ne ke yinsa.

  Rumanci- Rumanci kusan tafiyarsu daya da mallanci, wato tsaga ce guda biyu masu fadi da ake yi a gefen ido. Mutanen ruma da ke kasar Katsina aka fi sani da wannan tsage (A na kiransu iyalan Jan waire)

  Fetali/Bille- Tsaga ce da yawanci mahauta kan yi wa zuri’arsu. Sai dai wasu kan yi wannan tsage a bangaren dama. Babu shakka a wasu wurare da an ga mai irin  tsagen akan danganta shi da dangin mahauta. Za a iya karanta: Tsagar ado ko shasshawa a al'adar Bahaushe

Comments

0 comments