Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Sunayen iskoki na zamani a wurin Bahaushe

Sunayen iskoki na zamani a wurin Bahaushe

 • makala ta ta farko kan iskoki na yi bayani ne kan yadda aka raba iskoki a kasar Hausa zuwa na gargajiya da kuma na zamani. Na yi bayani kan na gargajiyar, sannan yanzu kuma wannan zai dubi na zamani ne.

  To kamar yadda Bunza (2006) ya ce “iskoki a wurin Bahaushe wasu halittu ne masu kama da mutane ta fuskar halittarsu, da surarsu da ayyukansu da al’adunsu da dabi’unsu da harshensu da siyasar rayuwarsu da sauransu. Bahaushe ya yi imani da samuwarsu a kowane tudu da rahi na bangon duniya, duk inda ake samun mutane ana samun iskoki”. To tun da mun ga sunayen iskoki na gargajiya a makala ta farko yanzu kuma za mu ga sunayen iskoki na zamani.

  Sunayen da zamani ya haifar kuwa, su ne sunayen da suka yi fice saboda tasirin bakin al’adu cikin gargajiyar Bahaushe. Dukkanin sunayen an same su ne bayan cudanyar Hausawa da Larabawa ‘yan kasuwa da masu yada addinin musulunci. Larabawa ‘yan  kasuwa su suka fara ziyartar kasar Hausawa don cinikin bayi, da hauren giwa da sauransu. Tun gabannin musulunci ya bayyana garesu suna bai wa iskoki muhimmanci. Sun yi imani da su, da musulunci ya zo ya kara tabbatar musu da imaninsu. Daga cikin sunayen akwai:

  1. Aljani: daga kalmar Larabci ‘Aljinnu’
  2. Jinnu: kai tsaye daga kalmar ‘jinnu’
  3. Ibilishi: daga sunan shedan ‘ibilis’I, uban aljanu.
  4. Rauhani: sunan da ma’abota tsibbu ke yi masa. A samo shi daga kalmar Larabci ‘ruh’.
  5. Ira’izai: sunan ya samo asali ne daga harshen Larabci ne.

  Wadannan su ne sunayen da suka yi fice bayan bayyanar musulunci zuwa yau a bakunan Hausawan kasar Hausa. Kowane suna daga cikin sunayen na gargajiya ko na zamani, Bahaushe na amfani da shi. Dubi: Sunayen kabilun iskoki a wurin Bahaushe

Comments

0 comments