Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Yadda ake noman albasa da amfaninta ga rayuwar bil'adama

Yadda ake noman albasa da amfaninta ga rayuwar bil'adama

 • Albasa na daya daga cikin kayan lambu wadda take da launin fari da ja amma idan aka yanka dukkansu farare ne tsala-tsala. Tana da zafi a ido musamman in ana yanka ta ruwan ya shiga idon mutum. Ana kuma sanya ta cikin girki don Karin dandano, har ma wurin wasu magunguna.

  Yadda ake noman albasa

  Da farko, da rani ake noma albasa, domin ba ta bukatar ruwa ya mata yawa, musamman lokacin damina, sai ta lalace. Ana noman albasa a kusa da rafi ko kuma koramu ko madutsun ruwa (dam). Ana fara noman albasa da juya kasa, ma’ana za a ta da kasar sama-sama, sannan a tara kasar kusurwa hudu wadda ake kira da suna ‘kome’ a ciki za a watsa irin ba tare da an jika komen ba. Daga nan sai a samu kasa mai laushi a watsa a kan irin saboda kar ruwa ya ja irin domin bai da nauyi. Haka kuma yashin ba ya yin yawa, domin in ya yi yawa zai hana albasar tsira. Za a samu ciyawa a rufe irin, saboda a mataki na farko albasa na bukatar ruwa. Sannan a cikin kwanaki shida ko mako guda ne za ta fara fitar da kai in a lokacin zafi ne. in kuma a lokacin sanyi ne za ta kai kwana goma, daga nan sai a cire ciyawar a zuba taki na zamani ko na gargajiya.

  Irin albasa na daukar kimanin kwana talatin ko arba’in (30-40) kafin a fara cirewa  ko a sayar wa manoma da ke bukata sai su dasa.

  Yadda ake dashen albasa

  Bayan irin albasa ya rika za a juya kasa ta yi laushi, sannan a jika ta. Daga nan sai a rika ciro irin ana dasawa daya bayan daya, ta amfani da wata ‘yar fartanya karama ko a yi amfani da yatsu. Albasa tana daukar kimanin kwanaki 80-100 kafin ta nuna a fara cirewa zuwa kasuwa ko gida.

  Amfanin Albasa a wurin bil’adama

  Albasa tana da matukar muhimmanci ga rayuwar bil’adama. Domin tana kunshe da wasu sinadarai masu yawa, irin Protien, Calcium, Vitamin A, Vitamin B, Vitamin C, Vitamin E, da kuma wani sinadari mai suna Allicin, wanda shi ke haddasa idanun mutum yake hawaye, a duk lokacin da ake yanka albasa.

  • Ana soya ta cikin man gyada ko manja ko man inji domin kashe gafin man.
  • Tana da sinadarin ‘Chromium’ wadda take taimaka wa masu fama da cutar suga.
  • Tana kara karfin sha’awar namiji, idan aka markade albasar aka kuma hada da lemo da cittan munci a rika sha cikin cokali sau uku a rana.
  • Tana kara wa miya dandano
  • Tana kashe karnin nama ko kifi in an tafasa su da ita.
  • Tana kashe kwayoyin cuta dake haddasa warin baki da kuma riga-kafin cutar hakori.
  • Tana kuma riga kafin wasu cututtuka da ke alaka da zuciya.
  • Tana maganin mura, musamman wajen ruba sabuwar mura.
  • Tana maganin sanyi.
  • Tana maganin tari da toshewar makogoro, idan aka hada ta da zuma a sha sau uku a rana
  • Tana taimakawa wajen kashe karfin cutar daji.
  • Sannan man albasa kuma na maganin taushin jiki, sannan yana taimakawa wajen warware jijiyan jikin bil’adama.

  Mai karatu na iya karanta: Bayanai akan dabbobin gona da kuma Samar da aikin yi ta hanyar noma da kiwo.

Comments

0 comments