Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Hanyoyin kayyade iyali da illolinsu ga rayuwar al'umma

Hanyoyin kayyade iyali da illolinsu ga rayuwar al'umma

 • Kayyade iyali ko tsara Iyali: na nufin tsara haihuwa, musamman matan da suke saurin daukar ciki, da kuma marasa lafiya. Rashin lafiyar da ake dauka wanda kan iya samun jariri, da kuma mutane da suke dauke da nauyi mai girma a kansu ba su da mai taimaka masu wajen warware matsalarsu. Wannan tsarin ya shafi mutum daya ne da iyalinsa a kankansa. Dubi: Rage farashin aure a kasar Hausa: Gyara ko batawa

  Akwai hanyoyi ko dabaru da dama da ake bi wajen hana haihuwa ko kayyade iyali, daga ciki akwai:

  • Kwayoyin magani na hana haihuwa
  • Allurar hana haihuwa
  • Zaren  mahaifa
  • Robar mata
  • Robar maza (kororo roba)

  Kwayoyin magani masu hana haihuwa (Oral Contraceptives (PILLS)

  wadannan kwayoyi ne da ake amfani da su don hana haihuwa. Asalin irin wadannan kwayoyi suna yin tasiri ne ga maniyyin mace su hana su aiki. Daga cikin  Wadannan kwayoyi akwai wanda ake kira "ancullor" akwai "lyndiol" akwai kuma "liynovlor" da sauransu.

  Allurar hana haihuwa (Projestin Injection)

  Ita kuma wannan allura ce da akan yi don hana haihuwa. Daga cikin alluran da aka fi amfani da su don wannan aiki akwai kamar su "Depo-provera medroxy progestere Actate (DPMPA), da "Nokethindrone Enonthate (NET) da sauransu. Ita wannan allurar tana hana ciki ne ta wajen danne karfin kwayoyin maniyyin mace. Tana kuma kade jikin mahaifa ta yadda ko da ba ta yi tasiri ba kwan maniyyin ba zai sami inda zai makale a mahaifa ba, tana kuma tara majina mai kauri a hanyar da maniyyi kan wuce zuwa mahaifa, don kada ya samu wucewa.

  Zaren mahaifa (Intra Uterine Devices (IUD)

  Ita ma wata hanyar ce ta hana haihuwa wadda Richter da Graefenberg suka kago a shekarar 1909. Wani zare ne na roba wanda akan sanya a mahaifa a bar shi sai zuwa wani dogon lokaci. Ba za a cire ba sai sanda matar ke son ta sake haihuwa. Wannan zare yana hana maniyyi kuzari ya kuma kashe kwayoyin maniyyi na mace da kwaroron da sukan bi zuwa mahaifa.

  Robar mata (Diaphragms and Cervical Caps)

  Ita kuma wata roba ce mai tattausan baki. Wani likita ne a Kasar Jamus mai suna Ferick wilde ya kago shi a shekarar 1838. Ana sa wannan roba ne a cikin farji kafin saduwa ta yadda zai je ya toshe kofar mahaifa. Ana kuma shafa wani mai wa roban kafin a sa.

  Wadannan kadan kenan daga cikin dabarun da akan yi amfani da su don hana haihuwa. Ba a ma yi maganan riga ba, wato kororon roba, wanda maza kan yi amfani da (condoms) da kumfa wanda mata kan sa, (foams). Akwai kuma hanyoyi da ake bi a dakatar da haihuwar gabadaya, wanda ake kira "Sterilization".  

  Duk wadannan dabaru da muka ambata dabaru ne wadanda ilimin likitanci ya kago, wanda imma dai su zama na sha, ko kuma na sanyawa da wani abu, ko ta hanyar allura.

  Wadannan dabarun kenan, a danna wannan wuri don karanta makala ta gaba akan illolin dabarun.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Kansar mafitsara na daga cikin ire-iren kansa da su ka yawaita a cikin al’umma. Ita kansar mafitsara kamar yadda sunanta take ta na farawa ne daga cells din mafitsaran mutum. Mafitsara dai kamar yadda muka sani wani ma’aji ne a can kasan cikin mutum wadda amfaninsa shi ne adana fitsari. ...
 • Kansar mama ko cutar daji cuta ce ta kansa da take yaduwa a cells din nonuwar mace (breast). Baicin kansar fata (skin cancer), kansar mama ita tafi ko wacce irin kansa da mata ke dauke da ita a kasar Amurka. Kansar mama na iya kama mace ko na miji amma ta fi kama mata nesa ba kusa ba akan maza. Yad...
 • Bismillahir Rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai juya zukata yadda Ya so. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya kwadaitar kan hadin kai, kuma ya hana rarrabuwar kawuna. Kuma ina shaidawa lalle Annabi Muhammad bawan Allah ne, kuma manzonsa ne, wanda y...
 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
View All