Makalu

Blogs » Kiwon Lafiya » Illolin da hanyoyin kayyade iyali ke haifarwa ga rayuwar mace da kuma iyali

Illolin da hanyoyin kayyade iyali ke haifarwa ga rayuwar mace da kuma iyali

 • Kamar yadda na bayanna a makala ta farko kan ‘Hanyoyin kayyade iyalimun fahinci cewa hanya ce ta tsara haihuwa da mutane ke bi don gudun daukar ciki. To shi wannan tsarin aiki ne na zabi ta wasu hanyoyi na musamman wadanda mutane ke bi wadanda suka dace da wadanda ba su dace ba domin samun tazara ko tsayar da haihuwa da yaduwar dan adam. Wadannan hanyoyin sukan haddasa illa ga masu yi, ko da kuwa an samu dacewa. Sau da dama mutane da suka tsunduma cikin wannan al’amari suna tsintar kansu a wasu matsaloli da ba sa iya fahimtar abin da ya jawo musu hakan.

  Wasu daga cikin illolin da hanyoyin ke haifarwa  ga rayuwar al’umma

  Yana hana su haihuwa kwata-kwata a rayuwarsu

  Duk macen da ta tsayar da haihuwarta na wani lokaci zuwa gaba, tana aukawa cikin wannan matsala. Domin a yawa-yawan lokaci bayan ta huta sannan tana son haihuwa, yana iya zama mata matsala cikin ya ki shiga ko kuma in ya shiga din ya ki zama.

  Yana kawo musu rikirkicewar jinin al’ada

  Jinin al’ada da mata suka saba yi bayan kowane wata, ida mace ta yi amfani da abubuwan hana daukar ciki yana haifar masu da matsalar rikecewar jini. Wanda zai rika zuwa masu a kowane lokaci da ba ta zaton zuwansa. Sannan wani lokacin yakan iya zuwa ya dauke bayan kwana biyu ya dawo.

  Yana haifar masu da cutur kansar mahaifa

  Wannan ya tabbata cewa wani lokaci bayan mace ta yi amfani da wannan hanyar, matsala cutar kansar mahaifa na iya afka mata, kasancewar ta lalata mahaifar da wasu sinadarai da za su iya haifar wa mahaifar matsala.

  Yana kawo musu yawan kasala ba tare da sun yi wani aiki na gajiya ba

  A yawa-yawan lokaci kasala na kama irin wadannan mata wadanda kuwa ko da ba su yi wani aikin ba. Hakan ba zai sa su fahinci abin da ke kawo masu wannan kasalar ba. Illa kawai su je asibiti a ba su magunguna.

  Yana haifar masu da cutar hawan jini

  Masana sun tabbatar cewa yana daga cikin illolin dakatar da haihuwa mace ta kamu da cutar hawan jini.

  Yana kuma dauke masu al’adar gaba daya, sannan ya rika sa musu yawan ciwon ciki

  Wannan na daga cikin irin rikice-rikicen da shan ko amfani da kwayoyin dakatar da haihuwa ke haifarwa. Sai ka ga al'adar mace ya dauke gaba daya kuma takan samu kanta cikin yawan ciwon kai. 

  Wannan ke nan. Maikaratu na iya karanta: Illolin da shafe-shafen mayi mai canja launin fata (bleaching cream) ke haifarwa ga masu yi

Comments

0 comments