Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Dalilin watsuwar harshen Hausa a kasashen Afirka

Dalilin watsuwar harshen Hausa a kasashen Afirka

 • Akwai dalilai masu dimbin yawa da suka haddasa yaduwar harshen Hausa a kasashen afirka (Afirka ta yamma, Afirka ta tsakiya, da gabashin Asiya da kuma kudancin Afirka) da nahiyar turai da kuma nahiyar Asiya. Wadannan dalilan ba su wuce na kimar harshe ba da al’adu, wato zamantakewa da kasuwanci da kuma wasu dalilai na hijira da kan iya kasancewa dalilai na Hausawa da sarauta da dai sauransu. Dubi: Gudumawar harshen Hausa a matsayin harshen uwa

  Idan aka dubi kasashen Afirka da dama za a ga inda Hausawa suka yi kaka gida da yawa a cikin wadannan kasashen. Wasu daga cikin kasashen kuwa sun hada ne da:

  • Benin
  • Ghana
  • Kamaru
  • Mali
  • Nijar
  • Sudan da sauransu.

  Masana harshen Hausa sun yi hasashen cewa baya ga harshen ksuwahili harshen Hausa shi ne yake da dimbin kalmomi kuma yana iya lamuncewa sabbin kalmomi da wasu harasa su shige mata.

  Kasancewar wannan dalilai ya sanya wasu kabilu ko al’umma suke yin na’am da ita saboda saukin mu’amala da kuma nuna irin kaulin nan na masu hikimar magana da ke cewa kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi, a dangane da al’ada kuwa Hausawa an riga an cire masu hula wajen yarda da al’adunsu kuma da bukukuwa na suna da na auratayya da na shan kabewa da budar daji da wasanni irin na kalankuwa da na mutuwa da na hanyar ilmantarwarsu da na kasuwancinsu duk sukan yi amfani da wadannan damammaki musamman ta wajen sanya suturarsu.

  Hausawa kan baje kolin halayyarsu ne don wadanda ba Hausawa ba su kwaikwaye su tare da inganta wannan dabi’a a duk inda suka sami kansu. Wani abin ban sha’awa a nan shi ne a loton da shi wannan Bahaushe yake baje kolin halayensa wala Allah mai kyau ne ko mara kyau ne baya nuna shayi ko kunya a wannan lokaci sai dai kawai zai nuna wannan al’amari kamar yadda Bahaushe da yake kasar Hausa yake nunawa. Mai karantu na iya karanta: Matsayin harshen Hausa a ilmin ma ana wajen bunkasa kalmomi

Comments

0 comments