Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Al'ada: Hasashe kan asalin samuwar camfin Hausawa na gargajiya

Al'ada: Hasashe kan asalin samuwar camfin Hausawa na gargajiya

 • Gabatarwa

  Kamar yadda bayanai suka nuna, abu ne mawuyaci a fadi lokacin da al’ummar Hausawa suka fara wasu daga cikin al’adunsu da dabi’unsu, domin abu ne wanda yake da makusanciyar dangantaka da kafuwar al’umma. Al’adar camfi ma na daga cikin al’adun da ba za a iya tantance lokacin da aka fara su ba. Da haka ne Bunza, (2006) ke cewa “ana jin cewa camfi ya samo tushe ne tun lokacin da dan-Adam ya fara tunanin lalle akwai wasu abubuwa da ke da tasiri a kansa da harkokinsa da rayuwar da ke kewaye da shi. Ta haka ne yakan kagi gurbataccen tunani na yanki-fadi, ya shirya wani bayani, ya dauki wasu abubuwa ya jingina su da tasirin wani abu.

  Yahya da wasu (1992:18-19). Suka ce ga alama wajen kokarin samar da ingantacciyar al’umma ta yin horo da hani, al’ummar Hausawa suka kagi dabarar camfi ta neman taimako daga wani abu wanda ya fi karfinsu don tsayar da ka’idoji da dokokin samun zaman lafiya. Dubi: Tasirin camfe-camfen Hausawa cikin tarbiyyarsu (Na daya)

  Bello (2004) kamar yadda yake cewa dangane da asalin samuwar camfi “Yana da wuya mutum ya ce ga lokacin da dan-Adam ya fara yin camfi  da kuma dalilin yin su a duniya, amma ta hanyoyin nazarce-nazarce da tarihin rayuwar dan-Adam dangane da al’adunsa, a iya kafa hujja dangane da wasu abubuwa da ake ganin su ne kila masomin camfi da kuma lokacin fara su”.

  Hasashe kan samuwar camfin Hausawa

  Akwai hasashe-hasashe da yawa da masana al’ada ke yi kan tarihin samuwar camfi a al’adar Bahaushe, idan aka yi la’akari da ma’anoni da magabata kuma masana al’ada suka bayar game da camfi za mu ga cewa akwai tazarar hasashen camfi kamar haka:

  Hasashe na daya

  Ibrabim, (1982) Ya ce “tun lokacin da mahiccin halitta ya halicci halittu, Hausawa sun tarar da sama da kasa a shimfide, yanayin da Bahaushe ya samu kansa a farfajiyar duniya ya taimaka wurin haifar da camfe-camfen Hausawa. Tsarin sararin samaniya da kawace-kawace da ke tattare da ita irin su rana, da wata da sauyawar dare, da rana, ya ba wa Bahaushe damar gina camfe-camfe da dama bisa abubuwan da ya ga sun wakana a ciki. Idan ana laluben tarihin camfin Bahaushe, dole ne a yi la’akari da wadannan abubuwa ta fuskar nazari, musammam ta fuskar camfe-camfe da aka gina a kansu. Misali.

  • Idan rana ta kama wata wani abu babba zai faru
  • Hazo alama c eta yanayin daminar da ke tafe.
  • Kwanciya a hasken farin wata na debe budurcin mace.
  • Idan hasken wata ya bayyana da dare ko akwai hadari ba a ruwa.
  • Idan zunni (bakan-gizo) ya bayyana a hadari ba a ruwa rannan
  • Ruwan kankara alama ce ta samun wake wannan shekara

  Idan aka dubi wadannan misalan, za a ga cewa Bahaushe ya gina camfinsa ne akan wadannan yanayi saboda ganin akasarin lokaci hakan na kasantuwa gare shi, wannana ma shi ne asalin abin da ya sanya shi yin amannah da hakan.

  Hasashe na biyu

  Bunza (2006) ya ce “Tarihin samuwar camfi yana da alaka ta fuskar da Bahaushe ya kiyaye fasulan shekara kamar: Rani, da Damina, da Bazara, da Hunturu. A cikin wadannan lokuta wasu abubuwa muhimmai suna aukuwa kuma Bahaushe yana kiyaye su, da yanayi da suke faruwa, da kuma dalilin da ke sa su faruwa. Da haka ne Bahaushe ya gina wasu camfe-camfe kamar haka: Misali

  • Kashe kwaron damina yana kawo fari.
  • Idan shamuwa ta zo cikin gari, damina ta kusa.
  • Idan ana ruwa ba a son ana surutu.
  • Iskan hunturu ne ke motsa haukar mahaukata. Da sauransu

  Hasashe na uku

  kamar yadda bincike ya bayyana dangantakar Bahaushe da tsirarrai, da itacen magani na gargajiya, yana da muhimmiyar rawar da ya taka wajen tarihin samuwar  camfi. Ga alama, Bahaushe shi ya tarar da tsirrai, bas u suka tarar das hi ba. To yanayin itace da tsirran magani musamman kan mahadinsu, da yadda ake sarrafa su, ya yi naso sosai ga tarihin samuwar camfin Bahaushe idan aka dubi wadannan mislan kamar haka:

  • Shan itacen shashatau na haifar da mantuwa.
  • Shan tsimin gawo na bushe zuciya da kore tausayi a cikinta.
  • Ba a kwance laya, idan an kwance ana yin hauka.
  • Ba a yin jima’i da guru, in an yi ya lalace.
  • Ba a dariyar maras lafiya cutar za ta koma kan mai dariyar.

  Hasashe na hudu

  Yanayin lafiyar jikin Bahaushe, da huldarsa a duniyan mafarki, na daga cikin abubuwa da ya kyautu a kula idan ana son a kwakulo tarihin samuwar camfi. Bahaushe ya kiyaye da wasu abubuwa dab a sa shafa wa lafiyar jikinsa lafiya, wasu kuwa suna razana lafiya, wasu na karfafa lafiya wasu kuma kashe jiki suke. Daga nan ne ya gina mafi yawa daga cikin camfe-camfensa.

  • Cin naman akuya na kara harzuka cutar kuturta.
  • Cin kwayar takiyar tsakiyar goruba na sa makoko.
  • Kwana da wando yana raunana karfin namiji.
  • Ketara wando na sa mata mafarki.
  • Yawan cin waina na haifar da mura.
  • Cin dawa na kara karfin gabobi.
  • Cin dankali na rage karfin namiji.
  • Cin aya na kara karfin gani.

  Mai karatu kar ka gaji, dubi makala ta gaba don ganin matsayin camfi a al’adar Bahaushe.

Comments

0 comments