Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Bunkasar Daular Usumaniyya: Tun Mujaddadi Danfodiyo zuwa yau

Bunkasar Daular Usumaniyya: Tun Mujaddadi Danfodiyo zuwa yau

 • Tarihin Daular Usumaniyya ba za ta cika ba matukar ba tabo tarihin Mujaddadi Shehu Usman Fodiyo ba. Saboda haka ga takaitaccen tahirinsa nan kamar haka:

  An haifi Shehu Usman Dan Fodiyo a ranar lahadi karshen watan safar, shekarar hijra ta 1168 wanda ya zo daidai da (December 1754) a wani kauye mai suna Maratta. Daga baya iyayensa suka tashi zuwa Degel a kasar Gobir. A yau babu wannan gari na Gobir kodayake an yi shi ne kusa da sabon birni a jihar Sokoto, iyaka da kasar Nijar. A halin yanzu kauyen da aka haifi Shehu yana cikin kasar Nijar. Shehu ya yi wayo da bude idonsa a cikin gidansu, a kuma kauyensu wato Degel. Mahaifinsa Muhammadu Fodiyo, shi ne ya rada masa suna Usman (wato sunan kakansa kenan). Muhammadu Fodiyo. Wanda Fodiyo a harshen Fulatanci na nufin Faqihi masanin Fiqihu.

  Nasabar Shehu shi ne dan Usman dan Salihu dan Ayuba dan Haruna dan Muhammad Gwandu dan Jubo dan Muhammadu Sambo dan Ayuba dan Masirana dan Baba dan Musa Jakullo. Musa Jakullo shi ne wanda ya yi hijra da mutanensa daga Futa Toro (Senegal a yanzu), a kan hanyarsa da nufin yin hijira zuwa Hijaz (Makka a yanzu). Amma sai ya sami tsayawa da mutanensa a kasar Hausa (kwanni). Sun zauna har suka kuma sadar da dangantaka ga Hausawa, har zuwa haihuwar Shehu Usman. Sauran mutane kuma suka zarce da hijra har suka isa zuwa Furo da Sinar. Mahaifiyar shehu ita ce Hauwa'u ta fito daga zuriya daya da Mahaifinsa. Ita ce Hauwa'u bint Muhammad bint Usman bint Hamma bint Ali. Wanda ya ke kaka ne na biyar ga mahaifin Shehu.

  Ita kuma mahaifiyarta ita ce Ruqayya diyar wani mashahurin malami mai suna Muhammad bin Sa'ad bin Dadani bin Idris bin Idris bin Ishaq bin Masirana. 

  Yadda Daular Usumaniyya ta bunkasa

  Sheikh Usmanu Bin Fodiyo wanda aka fi sani da ''Dan Fodiyo'' ko “Shehu Dan-Fodiyo” yana da ‘ya’ya 17 ko 18 ne, 5 daga cikin ‘ya’'yan nasa su suka kafa masarautun daular usumaniya ta Sokoto. Canjin tsarin addini, da mamayar da ya yi, da koyarwarsa  da kuma jagoranci da shugabancinsa ya ratsa duk sassan kasashen Hausa/Fulani, kama daga arewacin Najeriya har zuwa yankin Nijar, Burkinafaso, Mali, Northern Cameroon, da wasu bangare na Chad, da sashen Senegal, Gambia da Gabon. Bayan jihadinsa a 1804 shiyoyin nan suka tabbatar masa da ‘Amir-ul Mu’minin’ (kwamanda mai aminci), wanda daga bisani aka mayar da taken ya koma SULTAN. Sai bayan da turawa suka mallaki kasashen Hausa suka mamaye Afirka ta kudu ne sannan ikonsa ya takaita ga arewacin Najeriya. Ga kuma jerin ‘ya’yansa guda biyar (5)  da suka yi sarautar wasu garuruwa a kasar Hausa.

  1.     Muhammadu Bello: dan Shehu ya mulki; Wurno, Rabah, Dange, Goronyo, da Isa na (jihar Sokoto), Maradun (jihar Zamfara) da Kontagora (jihar Niger)

  2.     Muhammadu Buhari: Ya mulki Tambuwal, Dogon-daji, Sifawa da Bodinga (jihar Sokoto)

  3.     Abubakar Atiku: Ya mulki Gwadabawa, Illela, Gada, Tangaza na (jihar Sokoto)

  4.     Ahmadu Rufa'i: Ya mulki Silame (jihar Sokoto)

  5.     Isah Mai Kware: Ya mulki Kware (jihar Sokoto)

  Sannan kanensa Abdullahi bin Fodiyo wanda aka fi sani da Abdullahin Gwandu, Shehu Usman ya nada shi a matsayin (Amir) wato Sarkin Gwandu, wanda aka mayar da hedikwatanta birnin Kebbi. Sannan kuma aka sa shi shugaba mai kula da harkokin masarautun kudu wato: Nupe da Ilorin. Haka kuma yayansa su ma sun jagoranci masarautar Gwandu, Jega, Kalgo, Bunza, Ambursa, Masama, Makera da gundumar Kambaza dukansu na (jihar Kebbi). Sannan kuma shi kan sa Sultan (Shehu Usman Dan Fodiyo) yana kula da kuma duba duk harhokin da wadannan gundumomi ke tafiyarwa a tsarin mulki karkashin jihar Sokoto da Zamfara na yanzu. Baya ga wannan har ila yau Sultan Danfodio ya zama kwamandan jihadin addinin Islama inda ya jagoranci masarautun yankin arewacin Najeriya. Wanda daga karshe aka daukaka wannan matsayi na Sultan ya samu gindin zama daga gwamnatin Najeriya  wato sarkin musulmi na Najeriya ‘President General of the Supreme Council for Islamic Affairs of Nigeria’ (SCIA).

  Ga kuma jerin wadanda suka yi wannan sarautar tun daga farko daular Usumaniyya zuwa yau. (1804-date)

  1.     Shehu Usman Dan Fodiyo (wanda ya kafa daular) 1804-1817

  2.     Muhammadu Bello (Dan Shehu Usman) 1817-1837

  3.     Abubakar Atiku-1 (Dan Shehu Usman) 1837-1842

  4.     Aliyu Babba-Mai Saje (Dan Muhammad Bello) 1842-1859

  5.     Ahmadu Atiku (Dan Abubakar Atiku-I) 1859-1866

  6.     Aliyu Karami (Dan Muhammad Bello) 1866-1867

  7.     Ahmadu Rufa'i (Dan Shehu Usman) 1867-1873

  8.     Abubakar Atiku-Ii (Mai Rabah)(Dan Muh'd Bello) 1873-1877

  9.     Mu'azu Dan Bello (Dan Muhammad Bello) 1877-1881

  10.   Ummaru Aliyu (Dan Aliyu Babba) 1881-1891

  11.   Abdurrahman (Danyen Kasko)(Dan Abubakar Atiku-I) 1891-1902

  12.   Muhammad Attahiru-I (Dan Ahmadu Atiku) 1902-1903

  13.   Muhammad Attahiru-II (Dan Aliyu Babba) 1903-1915

  14.   Muhammadu Maiturare (Dan Ahmadu Atiku) 1915-1924

  15.   Muhammadu Tambari (Dan Muhammadu Maiturare) 1924-1932

  16.   Hassan Dan Mu'azu (Dan Mu’azu Dan Bello) 1931-1938

  17.   Abubakar Sadiq-III (Dan Shehu Jikan Mu'azu Dan Bello) 1938-1988

  18.   Ibrahim Dasuki (Dan Haliru; Jikan-Jikan Muhammadu Buhari) 1988-1996

  19.   Muhammadu Maccido (Dan Abubakar Sadiq-III) 1996-2006

  20.   Muhammad Sa'ad (Dan Abubakar Sadiq III) 2006-Date.

  Wadannan sune suka jagoranci musulman Najeriya har zuwa yanzu. Fatan wadanda suka rasu Allah ya jikansu, masu rai Allah ya kara masu yawan rai da ikon tafiyar da jagorancin al’umma.

  Mai karatu na iya karanta:Tarihin Najeriya: Irin gwagwarmayar da aka sha daga farko har zuwa yau

Comments

0 comments