Makalu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Dangantakar halayyar haihuwa da dabi'a cikin al’umma

Dangantakar halayyar haihuwa da dabi'a cikin al’umma

 • Sanin yanayin lafiyar mutum da cutar da ta shafe shi ba sa wadatarwa wajen tantance hakikanin ?abi'un mutane da halayyarsu a al’adar Bahaushe. Al’ada ta tanadi cewa halayyar da aka haifi mutum ita kanta tana da dangantakata da ire-iren halayyarsa, da dabi’unsa da makomarsa. Bahaushe ya yi imanai da wanna sosai, har yakan yi duba zuwa gare su wajen yanke wani hukunci nasa na al’ada. Ga kadan da ckin irin wa?annan misalan.

  1.     Dan fari

  2.     Dan tsoffi

  3.     Dan wabi

  4.     Dan auta

  5.     'yan biyu

  6.     Namata

  7.     Mata-maza

  8.     Shege da sauransu.

  Dan fari

  Kamar yadda Hausawa ke kula da ranar haihuwar mutum, ko yanayin haihuwarsa su rada masa sunan gargajiya (lakabi), haka suke kula da yanayin haihuwar mutum wajen tantance dabi’unsa. Ga al’adar hauswa, iyaye (uba da uwa) bas a ambaton sunan dan fari, ba a hira das hi ba a koya masa wasu abubuwa, ko yana goye a bayan mamarsa  aka ce wa mamar, me kika goya a bayanki? Takan kwance zani ya fado. Rashin samun cikakkiyar kulawa gad an fari shi ya sa ake kais hi wajen kakani, a can kuwa kara shagwabewa ma yake. A madubin al’ada, dan fari bai cika wayo ba, wawa ne kuma dambalele. Da wuya a samu dan fari wayayye, amma akan same su masu basiru da saukin kai wajen fahimta idan aka yi masu bayani. Karanta: Al'adar haihuwa a ?asar Hausa

  Dan tsofaffi

  Hauswa kan ce, “barewa ba za ta yi gudu dan ta ya yi rarrafe ba”. Yadda tsofaffi ke hangen nesa da sanin ya kamata, da tattali da dabara, musamman idan sun kai shekarun dattaku daga hamsin da biyar zuwa sama, duk yaron da suka Haifa cikin wannan shekarun dan tsufa ne, za a same su da cikakken hankali, da wayo da basira da hangen nesa, sai dai da wuya a same shi da kazar-kazar da himma. Dalili kuwa shi ne, ko da aka haifi shi karfi ya riga yak are dabaru kawai aka bari. Ba abin mamaki ba ne ya gaji wayo da dabara, amma ya rasa kuzari da karfi.

  Dan wabi/gwanne

  Dan wabi shi ne dan da Haifa bayan an haifi wasu suna mutuwa. Bahaushe ba ya tabbatar da wabi sai ansamu kamar haihuwa biyar zuwa sama suna mutuwa sannan zai ce wabi ya tabbata. Daga wannan zai fara daukan dukkan matakin fada da wabi. A al’ada, ?iyar wabi, an jarrabe su da tsautsayi, da fadawa cikin kaddarori na jimuwa, da miki iri-iri. Akan yi taka tsantsa da dan wabi kamar yadda ake yin taka tsantsa da mai fade.

  Dan auta

  Wanda duk aka Haifa daga baya, bayan an cire tammani sake samun wani ciki saboda suffa shi ake kira dan auta. A wata fadar kuma, duk wanda ya makaro cikin ‘ya’ya ya zama shi ne karami, ana kiransa dan auta. A al’ada dan auta za a same shi mai wayo, da basira da sanin ya kamata a wasu lokutan yakan zamo mai tausayi da farin jinni a idon jini.

  ‘Yan biyu (tagwaye)

  Wa?annan su ne tagwaye, maza biyu, ko mata biyu, ko namiji da mace. Idan suka wuce biyu to ba 'yan biyu ba ne, ba kuma tagwaye ba ne, ga al’adar 'yan biyu suna da tsotsayi da kohi sosai, shi ya sa ake tsoron fada da su ko a yi musu wani laifi. An zargi cewa, idan suka fadi wani abu zai auku, lallai zai auku. Idan suka yi wa mutum baki zai iya kama shi.

  Namata

  Yaron da aka haifa bayan an haifi mata biyu ko fiye, to shi ake kira namata. Al’ada na kallon cewa namata zai zama cewa mai shagwaba, wawa-wawa kuma mai son jiki da kwalisa irin ta mata. Wasu akan same su hatta da maganarsu irin ta mat ace da sauran ?abi'u.

  Mata-maza

  Yaron da aka haifa da farji da kuma zakari shi ne mata-maza a Hausa. A wata fadar kuwa, ko an haife shi babu wata daga cikin al’aurar (ba farji ba zakari) ga al’adar Hausawa masu irin wannan sifa ba a cika samunsu da hankali. A mafi yawan lokuta abin na zamo musu kamar tabuwan hankali, wasu ma su yi hauka tuburan.

  Shege

  Abin da wasu suke fassara shege shi ne, wanda aka haifa ba tare da samun uba da aka daura aure da mamarsa ba. Binciken al’adun Hausawa ya sha bayyanawa cewa, akan same su da basira da abin a zo a gani. Akan same su masu yawan kawaici da hanakali da natsuwa. Watakila irin halayyar da suka fito ke sa su wannan ladabi domin Karin maganan Hausawa cewa ya yi “abin ya yi yawa, shege da hauka”. 

  Sannan za a iya duba: Hanyoyin kayyade iyali da illolinsu ga rayuwar al’umma

Comments

0 comments