Makalu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Mutane da ke cikin wani yanayi a rayuwa dake gusar musu da hankali

Mutane da ke cikin wani yanayi a rayuwa dake gusar musu da hankali

 • Kimiyyar al’ada na kallon mutane ba kawai ta fuskar yanayin haihuwarsu kawai ba, hatta da halin da suke ciki na wani dan zamani takan kalla. Ba dole ne kodayaushe a samu mutum cikin halin da yake son ya kasance ba, tlas a wani lokaci ya kasance cikin wani hali na natsuwa, ko rashin natsuwa, ko uzuri da dai makamantarsu. To wannan makala zai yi dubi ne kan mutane dake cikin wani hali na musamman da zai iya ya tabi zurfin hanakalinsu, da tunaninsu na wannan lokaci. Ga irin mutanen da ake kallo cikin wannan hali kamar haka:

  ·        Mai dariya

  ·        Mai jin yunwa

  ·        Mai shan rake

  ·        Mai gudu

  ·        Mai jima’i

  ·        Mai kuka

  ·        Mai rawa

  ·        Fuskantar rubushi

  ·        Tsananin ki

  ·        Tsananin so

  ·        Tsananin tsoro

  ·        Uzurin kasha da sauransu.

  Mai dariya

  Abin da yake sa dariya dole ya hada da abubuwa biyu, ko dai gani da ido, ko tunani a zuci. Wa?annan abubuwa guda biyu duka suna cin zarafin mai yin su. Hausawa na ganin yayin da mutum ke cikin cin dariya, yana yagar hakora yana kyalkyalewa da dariya, to a haka hankalinsa cikakke ba ya jikinsa. Idan mutum na cikin wannan yanayi akan yi masa sata ko sane ko a tura masa wani abu da zai iya cutar da shi, duk ba zai ankara ba. Ashe kenan cikin irin wannan yanayi mutum in ya ture abinbci ko ya kwabe wani abu, ana yi masa uzuri idan aka yi la’akari da halin da yake ciki.

  Mai jin yunwa

  Illar yunwa uku adabin Bahaushe ya ruwaio. Na farko takan tankware dogo ya jicce, ya yi dan doro. Na biyu takan sa gajeren mutum katon kai, fuska ta tamuke ta matse. Na uku takan taba hankalin mai hankali. Hausawa na cewa, ko hauka t asana da yunwa. Da haka ne ma wani mawaki wato ?angoma ke cewa cikin wa?arsa “yunwa ta wuce lahaula sai dai a jika mata dan gari”. Sau da dama akan tarar da mahaukaci a kasuwa yana kuka in yunwa ta dame shi, daga ?arshe in ba a kula bay a ce ga garinku. Yunwa tana sa mai hanakali ya yi aiki irin na marasa hanakali.

  Mai shan rake

  Zaki na daya daga cikin abubuwa da mutane ke ganin suna tafiyar da hankalin masu hankali. A fagen zaki ga Bahaushe babu ya zuma, domin shi ake wa kirari da cewa, ga zaki ga harbi. A wata fadar kuwa y ace zuma sa lasar dau?a. abin da ya sa rake ya fi daukar hankali domin shi sai an hada da aikin tsaga, da na tauna, da jaye zaki zuwa ciki da lasar baki da sauransu. A ganin Bahaushe, mai shan rake bai da hankali sai yak are sha. Idan kana shan rake aka aikata wani aiki gabanka, ba ka iya ?arasar das hi da yadda aka yi shi domin hankalinka na can ga zaki labarin mai neman bataccen jikinsa d ya hadu da mai shan rake ya isa ya zama hujja ga mai marare.

  To kamar yadda muka gani cikin wadannan misalan, haka suke ga sauran, amma a dubi makala ta gaba don ganin bayanan sauran ma. Sannan za a iya karanta: Matsalolin talauci a rayuwarmu a yau

Comments

0 comments