Makalu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Tarihin makadan Hausa: Salihu Jankidi (1852-1973) rayuwa da sha

Tarihin makadan Hausa: Salihu Jankidi (1852-1973) rayuwa da sha

 • An haifi Salihu Jankidi ne a garin Rawayya ta kasar Bungudu ne a yanzu cikin kararnar Hukumar Gusau, wajejen shekara ta 1852. Sunan mahaifinsa Alhassan dan Giye dan Tigari mai abin kidi. Salihu shi ne sunansa na yanka, amma kanen uwarsa Kardau ya yi masa lakabi na Jankidi saboda jan da Allah ya ba shi wanda ya bi shi har bayan rasuwarsa.

  Alhassan Giye Dan Tigari

  Mahaifin Jankidi Alhassan Makadi ne na kalangu kuma mai yawan yawace-yawace don kida. Yakan bar garinsu Rawayya ya shiga uwa duniya don sana’arsa ta kida. Shi kuma makadi ne na lokacin kidan yaki. Ya je Argungu da Bida da Kwantagora da Kotonkoro da sauransu, amma yana komawa gida Rawayya. Daga baya ya tashi zuwa Kotonkoro, sai kuma ya tare Kwantagora wurin sarkin Sudan Ibrahim. Ya yi masa wakoki da yawa, amma wadda ake iya tunawa ita Ce:

                 Namiji kamar maza ya kai.

                 Jikan Shehu na tsaye.

                 Na Garba waiwaya bayanka,

                 Ka hi damben juya da kahirai.

  Kuruciyarsa da tasowarsa

  Salihu Jankidi ya bude idonsa a Kwantagora a nan ne ya yi rayuwarsa ta kuruciya. Ya tashi yana yaro mai karfi da kurari, da kwarjini a tsakanin jama’a, sannan ja ne kamar tsada, tsaka-tsaki ne a wajen kirar jikinsa dangane da tsawo da baga. Jankidi ya yi dambe da kokawa da sauran wasu ayyukan samartaka na sha’awa. Saboda kasancewar Salihu ya tashi cikin yake-yake kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka duk kusan abubuwan da ya yi na yarinta na nuna karfi da bajinta ne. Ya yi karatun allo inda har ya sauke Alkur’ani mai tsarki ya kuma karanta wasu daga cikin kananan littattafan addinin Musulunci kamar kawa’idi da Ishmawi da Kurdabi da sauransu. Amma fa bai yi ilimin addini na littattafai mai zurfi ba.

  Koyo da fara wakokinsa

  Makadi Alhassan shi ne ya fara koya masa kida da waka inda ya soma bin sa kida har ya fara kada kuntakuru watau kanzagi. Daga nan kuma ya shiga cikin yayensa mata masu amshi. Lokacin masu yi wa mahaifin nasa amshi, su ne:

  • Umma Tsohuwa
  • A’ishatu
  • Halimatu Bakabai

  Salihu Jankidi — daga baya ya soma. Haka kuma mahaifinsa Alhassan ya taba ba da shi riko ga dan’uwansa makada dan Yawuri don ya koyi kidan kalangu sosai da sosai,

  Bayan rasuwar Alhassan, sai Salihu Jankidi ya dauki shugabancin kida a nan Kwantagora tare da wadannan mataimaka:

  • Alhajiya — ‘Yar Halimatu Bakaba
  • A’ishatu
  • Halimatu Bakaba

  Koyo da fara wakokinsa

  A lokacin da ya fara kidan, sai ya hada kidan noma da kidan fawa a lokaci guda yana ta yi duk wanda ya samu a yi. Kuma da dai kalangu gadon gidansu yake wannan nau’in kida. Daga cikin yaki  da ya yi na farko-farko, akwai wannan:

              Yo gaba dai salsalon nibatau,

              Sanda mazan burdumi da galma.

             Mai son noma da dan magaji,

             Sai shi bido sulkuna da gari,

             Don a yi kwanan wata gudane

  Bayan da Turawan mulkin mallaka suka fara yake-yakensu da kasashen Hausa har lokacin da suka zo ita Kwantagora suka yi yaki da ita, sai Kwantagora ta fashe. A wannan halin ne Salihu Jankidi da sauran iyalinsa suka koma Kotonkoro. Daga nan sai Bagega cikin kasar Talatar Mafara, sai zuwa Kanoma, sai Bungudu, sai ya sake komawa Kwantagora bayan kare yaki.

  Daga nan kuma sai Salihu Jankidi ya koma gida Rawayya. Da yaki da Turawa ya kare, watau sun kama dukkan kasashen Nijeriya sosai, suka kuma shimfida mulki irin nasu wanda suke bukata, sai sarakunan da Turawan suka tabbatar (sababbi da tsoffafi) suka ci gaba da mulkin kasashensu. Daga wannan lokaci ne fa Salihu ya Jefar da kalangu ya kama taushi (tafashe) gadan-gadan yana yi wa sarakuna wakoki. To, sai daga Rawayya ya koma Tsahe wurin ‘Yandoto Muhammadu (1897—1924) da ‘Yandoto Ibrahim Maikano (1926—1928) ya yi musu wakoki. Sai kuma Salihu Jankidi ya kwashe iyalinsa ya koma Gusau da zama wajen sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai’akwai (1929—1943). Daga Gusau Salihu Jankidi bai koma cirawa zuwa wani wuri da nufm ya zauna ba, sai dai ya je ya kai kida ya dawo Gusau din. A cikin wata waka da ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai’akwai yana cewa:

                Ni Jankidi ba ni zuwa ko’ina,

                Kwadai na ba shi wucewar Gusau.

                Lalle ba mu zuwa ko’ina

                Kwadai na ba shi zuwa ko’ina

  Bayan da aka fitar da sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai akwai aka nada Shehu dan Sama’iIa sarkin Kudu (1943—1945), sai Jankidi ya koma wurin Sarkin Musulmi Abubakar III (1938—1988) ya zama ubangidansa. suna zaune tare da sarkin Musulmi har zuwa lokacin da ya nada shi sarkin taushinsa. A wajen nadin nasa an yi gagarumin buki inda makada yan’uwansa suka hadu, aka yi masa tattaki, magaji mai farai shi ne ma ya yi busar nadin don sheda wa jama’a.

  A cikin wata waka da ya yi wa sarkin Musulmi, Salihu Jankidi ya yi godiya ainun. Yana cewa:

             Godiya mu kai wa sarkin Musulmi,

             Da yai ma sarkin taushi,

             Yau batun Allah ya tabbata,

             Babu sauran mai wata gardama.

                      (Jankidi: rika girma ka isa Bubakar)

  Yaran Salihu Jankidi (‘Yan karbi)

  ‘Yan karbin Jankidi na farko na lokacin kidin noma da fawa da na samartaka su ne:

  • Aishatu
  • Halimatu Bakaba
  • Muhammadu
  • Alhajiya
  • Bahago
  • Ajiya

  Yan karbin Jankidi na fada

  • Makada Ibrahim dankaro  dansa ne
  • Mal. Abdullahi shi ma dansa ne.
  • Musa Dangaladirna Labbo: dansa ne.
  • MuhammaduTambai: Yaronsa ne.
  • Hassan : dansa ne,
  • Abduhlahi Jan Darno (Kaka): Yaronsa ne
  • Na Goje : Yaronsa ne
  • Umaru Kwairo: Yaronsa ne

  Yawace-yawacensa

  Salihu Jankidi ya yawata mafi yawan kasashen Nijeriya, musamman bangaren Arewa. Ya zagaya dukkan manyan garuruwan jihar Sakkwato da wasu kananan garuruwan. Haka kuma ya je Kano da Hadejiya da Daura da Katsina da Mani da Zariya da Kaduna da Bida da Ilorin da Minna da Ibadan da Lagos da Inugu kai da dai sauran kasashe.

  Shirya waka

  Da farko Sahihu Jankidi yakan sami labarai da bayanan da yake sa wa a waka ta hanyar fadawan sarki da hira da sarakuna kansu da ta bangaren hakimai da masu unguwanni. Kuma yana sane da abubuwan da yake gani suna gudana a fada da kuma cikin gari.

  Salihu Jankidi mafi yawa ya fi tsayawa gida ya shirya wakokinsa, kodayake yakan yi wasu wakokin nan take inda duk suka samu. Amma wakar da ya tsaya gida ya tsara ita ta fi dadi da kayatarwa da kunsar abubuwan ban sha’awa.

  Rasuwarsa

  Salihu Jankidi ya rasu ranar Juma’a 13 ga watan Oktoba 1973 a lokacin yana da shekaru dari da ishirin (120) a duniya. Allah ya gafarta masa, amin.

  Kuna iya latsa NAN don sauraron wakokin Jankidi. Sannan maikaratu na iya karanta: Tarihin makadan Hausa: Alhaji Sa’idu Mai daji Sabon-Birni da shahararsa da kuma Tarihin makadan Hausa: Ibrahim Gurso (1794-1814)

Comments

0 comments