Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Tubalan salo a wa?o?in baka na Hausa

Tubalan salo a wa?o?in baka na Hausa

 • Sa?o shi ne ginshi?in gina wa?a, ita kuma wa?ar hanya ce ta isar da sa?on, sannan wannan hanyar cike take da wasu dabaru daban-daban wajen isar da wannan sa?on ga jama’a da ake ?ira salo. Ganin muhimmancin wannan dabarar ce ya sanya wannan aiki nawa zai yi bayani kan muhimman tubalan salo a wa?a, musamman ma wa?ar baka, tare da kawo misalai masu daidaita mizanin wa?annan dabarun cikin wa?o?in mawa?an baka na Hausa.

  Bisa ma’ana, salo kalma ce ta fannu wadda za a iya fassarawa ta hanyar lugga da is?ilahi, wato fannin ilmi. Alal misali, a ma’ana ta lugga ?amus na Abraham (1962) ya bayyana salo ta hanyoyi iri-iri, akwai salo da yake nufi ?ir?iro hanyar yin wani abu ko yanayin wani abu. Akwai kuma salo mai ma’anar dabara ko fasaha, ko wayo, ko hazi?anci, ko gwaninta.

  Dangane da ma’anar salo ta is?ilahi wato ta fannin nazarin wa?a. Masana Adabin Hausa sun bayar da ma’anoni daban-daban.

  Sa’id (1981) ya bayyana salo ta fuskar nazarin wa?a rubutacciya kamar haka.

  Salo shi ne yadda mawa?i ya zana tunaninsa a takarda za a dube shi a gani shin yana da manufa, kuma bayaninsa yana da ?arfi ko rarrauna ne? Ana kuma fahimtarsa cikin sau?i ko kuma sai an yi wani lalube a gane manufarsa? Haka kuma za a dubi ?warewarsa da gwanintarsa wajen sarrafa harshe da ya yi amfani da shi. (Sa’id (1981:35)

  ?angambo (1981) shi kuma ya ce:“shi ne hanyoyi ko dabarun isar da sa?o, ya da?a fa?a?a tunaninsa da cewa lalle ne salo ya ?unshi za?i, kuma kyan salo ko muninsa ya danganta ga yadda kowane mutum ya za?i abubuwan da ya yi amfani da su cikin rubutunsa ko tunaninsa don isar da sa?onsa, kuma salo yakan ta’allaka ne dangane da yadda mutum yake tunani cikin dacewa. Domin haka salo wata hanya ce da ake bi a nuna gwaninta a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da za?an abubuwan da suka dace game da abin da yake son bayyanawa. Daga nan ne za a iya tantance salo mai sau?i ko mai tsauri, mai da?i ne ko mai armashi ko kuwa mai kashe jiki ne, maras ?arsashi mai ?osarwa, da dai sauransu.

  Salo a wa?o?in baka: wata hanya ce wadda maka?i ke kyautata zaren tunaninsa, ya sarrafa shi cikin azanci don ya cimma burinsa na isar da sa?o a wa?a. Abu ne wanda yake da?a fito da ainihin kyawunsu ko muninsu, ta haka ake iya gane wa?o?i masu ?arsashi masu hikima da balaga da kuma wa?o?i marasa ma’ana, marasa inganci. Ashe kenan ma’auni ne na rarrabe za?in wa?a ko ?acinta.

  Kamar yadda masana suka nuna, yana da wuyar a gane salo a bisa kansa, sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa. Bisa jimla muna iya cewa salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da sa?o. Za a iya fassara salo kamar haka:

  1.     Wani abu ne da ya ?unshi wani zaa?ii cikin wa?a. Wannan yana nufin yin amfani da wata kalma, lafazi da sauransu, maimakon wani.

  2.     Wani ?aarii ne na daraja a cikin wa?a ko rubutu wanda ba lallai ne a same shi a cikin kowace wa?a ko rubutun ba, wato ana iya samun wasu wa?o?i lami marasa salo.

  3.     Ya shafi kauce wa wata daidaitacciyar ?a'ida musamman cikin wa?a.

  4.     Wani harshen wani mutum ne, wato yadda salon Isa ya bambanta da na  Bello.

  Salo sun rabu kashi biyu kamar haka:

  1.     Salo na gaba?aya

  2.     Salo na filla-filla.

  Amma ba zai yiwu na bayyana ma’ana da sharhi kan wa?annan ire-iren-iren salon ba, domin masu iya magana suna cewa “inda baki ya karkata ta nan nyawu ke zuba”. Saboda haka a wannan aikin bayani zan yi kan tubalan salo a wa?ar baka, wa?annan tubalan gas u kamar haka:

  1.     Mallakar kalmomi

  2.     ?irar jimla  

  3.     Nau’o’in jimla

  4.     Siffantawa

  5.     Rauji

  6.     Tsarin tunani

  7.     Jaddadawa

  8.     Dangantakar tsari.

  Dubi makala ta gaba, don samun cikkaken bayani kan wadannan tubalan salon a wakokin baka na Hausa.

Comments

0 comments