Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Tarihin makadan Hausa: Ibrahim Gurso (1794-1814)

Tarihin makadan Hausa: Ibrahim Gurso (1794-1814)

 • An haifi Ibrahim Gurso a (1794-1814) a garin Tunfafiya wurin da mutanen Mafara suka zauna da ake kira tsohon zama, amma bayan Sarkin Mafara Muhammadu Dangarji  ya je ya kafa sabon zama na Talatar mafara.

  Haihuwarsa ta kasance ne a shekara ta 1794. Kakannin Ibrahim Gurso mata suna yi masa lakabi da Gurso kalmar da take ma’anar mutum maras kyau watau mutum wanda bai da kira da fasali mai ma’ana da ke jan hankulan mutane har a ga sha’awarsa. Sunan mahaifin Ibrahim Gurso shi ne Makada Tsoho wanda aka fi sani da Makada Dan Inda.

  Shi Makada Dan Inda makadi ne na noma wanda yake kidan kuwazu watau tuzu. Ya yi wakokin nomad a dama masu ma’ana da kayatarwa. Haka kuma Ibrahim Gurso yana da wani wa (yaya) da ake kira “makada Muhammadu Buwai” makadin noma.

  Lokacin da Ibrahim Gurso ya fara koyo da yin waka

  Ibrahim Gurso ya koyi waka a wajen wansa Muhammadu Buwai makadin noma. Ya fara koyon kidan noma ne ta amfani da kayan kidan kuwaru wanda ya tarar wansa Buwai Dangula yana yi. Daga cikin yaran Buwai akwai: Ibrahim Gurso wanda kanensa ne da Umaru Borin kida shi ma kanensa ne.

  Bayan da Buwai ya rasu ne, sai Ibrahim Gurso ya dauki shugabancin kidan nasu nag ado, wato kidan noma. Daga cikin farko-farkon wakokinsa na kidan noma, akwai wadda ya yiwa sarkin noma Barmo Shahe na Bagega ta kasar Talatar Mafara. Sai kuma wanda ya yi wa sarkin noma Gaka da Marake. Da kuma ta Goje Tudun Danbaba.

  Bayan wakokin noma sai Ibrahim Gurso ya juya ga wakokin sarauta. Wanda ya soma yi wa wakoki na sarauta shi ne Magaji Babba Danhutsaye jikan sarkin Talatar Mafara, Aliyu Dangwarno (1897-1916) lokacin yana hakimin cikin garin Talatar Mafara. Daga nan kuma sai Ibrahim Gurso ya zama makadin sarkin Mafara Abubakar Barmo (1916-1931).

  Lokacin da Ibrahim Gurso yake yaro ya tashi ya tarar da durdushin yake-yake da ake yi tsakanin masu jihadi da sarakunan Habe na Hausawa. Domin haka zamani ne na nuna jaruntaka da sanin dabarorin neman rayuwar duniya don kare kai. Sannan kuma ana gudanar da wasannin juriya gadan-gadan kamar kokawa da dambe da sauransu.. Ana kuma tsakiyar wasannin hawan doki da koyon sukuwa da guje-guje da sauran ayyukan motsa jiki.

  Gurso ya yi karatun allo har in day a kai zangon ya kusa sauke Al’kur’ani. Kuma a zamanin rayuwarsa ya fi son ya yi hulda da malamai, yakan halacci zauren malamai don tattauna matsalolin addini da sauraren hirarsu ta malanta. Wannan shi ya janyo ya dinga yin tambayoyi da fatawa da suka shafi addininsa. Watau yana cikin rukuni na uku na mutane da ake ce a zama malamai ko almajirai ko mai tambaya.

  Iyalin Ibrahim Gurso

  • Hassi manga              -           ta haifi Alhaji Aliyu
  • Azumi                        -           ta haifi Makada Muhammadu
  • Gado                         -           ta haifi Abu na-wazir
  • Ta Annabi                  -           ta haifi Ahmadu

  Rasuwar Ibrahim Gurso da wanda ya gaje shi

  Gurso ya rasu a Mafara (1953-1956) cikin shekara ta 1954.lokacin sarautar sarkin kudu Muhammadu Maccido. Bayan rasuwar Ibrahim gurso, babban dan sa Makada Alhaji Aliyu ya gaje shi, amma dama can ya koma Maru wurin Banaga na Maru. A Mafara kuma Makada mamman na kaka ya gaji Gurso, sai dai dukkansu sun rasu. Yanzu Makada Habu Dan kurma Dan Makada Alhaji Aliyu jikan Gurso shi ne yake rike da ragamar gidan guda biyu na Talatan Mafara da na Maru, amma yana zaune ne a garin Maru in  da mahaifinsa Alhaji Aliyu ya zauna.

  Mai karatu na iya duba: Tarihin makadan Hausa: Alhaji Sa’idu Mai daji Sabon-Birni da shahararsa da kuma Tarihin makadan Hausa: Salihu Jankidi (1852—1973) rayuwa da shahararsa.

Comments

0 comments