Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Tubalan salo a wakokin baka na Hausa (na biyu)

Tubalan salo a wakokin baka na Hausa (na biyu)

 • A makala ta da ta gabata na yi bayani kan muhimman tubalan salo a wa?a, inda na jero tubalan. To wannan shi zai yi bayani dalla-dalla kan wa?annan tubalan tare da misali cikin wa?o?in baka na Hausa.

  Mallakar kalmomi

  Kasancewa kowace wa?a tana da sa?o na musamman da take ?auke da shi, sannan kuma mawa?an baka kan tsaya su za?o kalmomi wa?anda suka dace da abin da suke magana a kai. Amfani da ire-iren wa?annan kalmomi kan ?ara wa wa?a armashi tare da ?warjini da kuma nuna ?warewar mawa?i a kan wa?a. Haka kuma mallakar kalmomi a wa?a wata dabara ce ta ?yallarowa tare da fito da haza?ar mawa?i. Kasancewa mawa?i kan iya za?o wa?annan kalmomi da suka dace da wa?arsa, to ya zama tilas ne ya Har ila yau za?en kalmomi da mallakarsu kan fitar da daraja da ?aukaka tare da ?warjinin wanda aka yi wa wa?a, misali, idan aka dubi wannan wa?ar kamar haka:

  Ku dubi idon zaki,

  Ko da gani nai,

  Umaru babu tsoro garai,

  (?an?wairo, wa?ar: Umaru ?an Iyan Sarkin Katagun)

  To, idan aka dubi wannan misalin gunduwa, to lalle za a fahimci cewa mawa?in ya za?o kalmomi domin zuga wannan basarake. Haka kuma wani misalin shi ne yadda ?an Anace ya za?o wasu kalmomi na zuga, ya kuma danganta su da Shago, a cikin wani kirari da yake yi masa kamar haka:

  ‘Yan maza kun ji irin ki?in kantukuru na Bukura,

  Duna mahaukaci na yamma da rimi,

  Rigima aradu mai dume kurma,

  Mutuwa ina ruwanki da tsoho,

  Kai su lahira gidan ?angongu,

  Barundumi abin zuba shara,

  Sauyi irin hakin da ka ramno,

  Lahira a kai miki gawa,

  Yaro gafaranka ga sababi nan,

  Kada aradu ta far ma,

  Halam ba ka san halin ?anen ajali ba,

  Sannu da ?ibar she?a,

  Mutuwa kin da?e kina kashe bayi,

  (?an’anace, wa?ar: Shago).

  Idan aka dubi wannan wa?ar za fahimci cewa mawa?in nan ya yi ?o?arin mallakar kalmominsa ne inda ya za?o kalmomin da suka dace ya yi amfani da su wajen kanbama gwaninsa ta yadda zai ?aukaka kuma yadda zai sa dukkan magab cikinsu ya ?uri ruwa.

  Dangantakar kalmomi cikin wa?ar baka

  Shi wannan wani rukuni ne, inda ake samun dangantaka tsakanin kalmomi da mawa?a ke amfani da su cikin wa?a. To babban abin lura a nan shi ne, a wasu lokuta mawa?an baka kan za?o wasu kalmomi masu dangantaka da juna, sannan su jera su wuri guda a cikin wa?arsa, misali

                 Yaya gari da Fulani,

                 Ban ji ana ce ku sai nono ba,

                 Yaya gari da kwarawa,

                 Ban ji ana ce ku sai suya ba

                 Yaya gari da musulmi,

                 Ban ji ana ta ?iran sallah ba

                 Yaya gari da mashaya,

                 Ban ga ana na?a mandula ba.

                 (Ali Makaho mai mandula, wa?ar: Na?a Mandula)

  To, a nan akwai dangataka kamar haka

  ·        Fulani        –         nono

  ·        Kwarawa    –        suya (suyar kifi)

  ·        Musulmi      –       Sallah

  ·        Mashaya     –       mandula (tabar wuiwui).

  Wani misali kuma shi ne yadda Sa’idu Faru ke cewa:

             Ihihiya da kunkuru shawaru guda sukai,

             Bushiya da beguwa shawaru guda sukai

             Kurciya da hazbiya shawaru guda sukai

             Bubukuwa da jimimi shawaru guda sukai

             (Sa’idu Faru, wa?ar: Muhammadun Muhammadu).

  To a wannan gunduwa ma lalle za a ga cewa akwai dangantaka tsakanin wa?annan tsuntsaye inda mawa?in ya jero su tare.

  ?irar Jimla

  Jimla cikakkiya kuma kar?a??iya ita ce wadda take da tsari na musammam da bin ?a’idojin Nahawun harshe don samar da ma’ana. To  mawa?an baka ba kasafai suke bin wa?annan ?a’idoji da tsarin ba, domin sukan sauya wa wata kalma ko wata jimla ?ira, walau ta fuskar sifa ko kuma ta fuskar ma’ana don cimma manufarsu. Domin salon wa?a yana kawo kumshiyar magana guda ne cikin tsari day a dace da bu?atun isar da sa?on da yake son isarwa.  Mawa?an kan yi wa?annan hikimomi ne ta hanyoyi da dama, ga misali daga cikin wannan wa?ar.

  (a)  Ku sarakuna duk na zamani,

  Ku ?auki hali irin Umaru Abba

  (b) Ku Sarakuna duk na zamani,

  Ku ?auki irin halin Umaru Abba

  (?an?wairo: wa?ar Sarkin Muri)

  Idan aka dubi wa?annan gunduwoyin nan biyu, za a ga cewa ?ango na biyu a gunduwar farko mawa?in ya ?era wa?annan kalmomi kamar haka:-

  a)     Hali Irin…: wato kalmar hali ne ta fara zuwa kafin kalmar irin. Amma idan aka dubi gunduwa ta biyu kuma a ?ango na biyu mawa?in ya canja sigar jimlar kamar haka:

  b)    Irin Halin…:  a nan kalmar irin ne ya fara zuwa kafin halin. A yayin da ya shafe ba?i ko sautin /n/ wanda shi ne a matsayin madanganci a cikin jimlar.

  Wani misalin kuma shi ne kamar haka:

  a)     Wani ?an sarki da idon kwa?o,

          Kullum shi dai ido nai waje,

  b)    Wani ?an sarki da idon kwa?o,

         shi dai Kullum ido nai waje,

         (?an?wairo: wa?ar Umaru ?an Iyan Sarkin Katagun)

  To a nan kuma za a ga kawai bambanci a ta fuskar yadda aka yi amfani da kalmar kullum a ?ango na biyu na gunduwa ta da kuma yadda a ?ango na biyu na gunduwa ta . domin gunduwoyin sun fara da:

  a.     Kullum …..

  b.     Shi dai …..

  A wasu lokutan kuma juyin da mawa?an suke yi bai tsaya a kan kalma guda ba a’a yakan iya shafar tsarin jimla gaba ?ayanta, kamar yadda za a gani cikin wannan baiti kamar haka: 

                    ?an?wairo sai mu je Borno,

                    Mu sha kaji da shinkafa,

                    Da bourabusko ta furar gero,

                    Haji musa du ana kai man,

                    Don Shehu Abubakar Sarki,

  A gunduwa ta gaba sai mawa?in ya ce:

            ?an?wairo dai mu je Borno,

            Mu sha kaji da shinkafa,

            Da burabusko ta furar gero,

            Don shehu Mustapha Umar,

            Haji musa du ana kai man,

            (?an?wairo: wa?ar Shehun Borno)

  A gunduwa ta farko ?ango na hu?u (4) da na biyar (5) su ne:

  4. Haji musa du ana kai man,

  5. Don Shehu Abubakar Sarki,

  Amma a gunduwa ta biyu ?ango na hu?u (4) da na biyar (5) kamar haka:

  4. Don shehu Mustapha Umar,

  5. Haji musa du ana kai man, 

  A nan mawa?in ya sauya ?ang

  o na hu?u (4) ya dawo na biyar (5) na biyar (5) kuma ya dawo na hu?u (4).

  A wasu lokutan kuma wasu mawa?a kan sauya siffar kalma ita kanta, ta hanyar yi mata ?ari ko ragi, misali.

              Kyawun ?an sarki talatin

              ?an sarki in ya yi sittin,

              Bai gaji gidansu ba ta ?ace mai,

              Sai bi?ar jalli,

              Sai dugun jakka,

              A samu na shan dawo,

              Kar a lalace.

              (?an?wairo: wa?ar Bi da kayan fa?a).

  A nan kalmar dugun a ?ango na (5) ya kamata ya kasance Madugu, wato mawa?in ya sare gabar ma daga kalmar, ta zama dugu. Sannan ya ma?ala ba?in /n/ domin ya zame masa madanganci.

  Mai karatu kar ka gaji, dubi makala ta gaba don ganin ci gaban bayanai kan tubalan salo a wakar baka. Musamman kan nau'o'in jimla.

Comments

0 comments