Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Dangantakar wakar Sa’adu Zungur, Arewa Jumhuriya ko Mulukiya da halin da ake ciki a siyasar Arewacin Najeriya a yau

Dangantakar wakar Sa’adu Zungur, Arewa Jumhuriya ko Mulukiya da halin da ake ciki a siyasar Arewacin Najeriya a yau

 • Kamar yadda aka saba sai mu fara da ?o?arin gane abin da kalmar wa?a ke nufi ga mutumin da ya tashi a ?asar Hausa.  Idan ka ha?u da mutun a kasuwa ko a ba?in titi ko a wani wuri na gargagajiya ka tambaye shi abin da ake nufi wa?a da Hausa abin da zai fa?a maka ba zai wuce yawan son yin abu ba, ko kuma jan magana, ko nanata zance kan wani abu da ake son yi, shi ya sa za ka ji mutum yana cewa kullum ina wa?ar zan zo mu gaisa amma abin ya faskara ma’ana yana ta sa?ar zuci na son zuwa inda wancan abokin na sa yake amma bai je ba kenan. Wa?ar abu na nufin ka yi ta kururuta batu ko jan batu a zuci na tsawon lokaci amma ba a aikatawa.

  Kenan idan aka natsu aka yi nazarin wa?a a zahiri za a ga wani zance ne ko magana ake ta ja a zuci har ta yi tsawon gaske. Amma ga masana, wa?a na nufin abubuwa da yawa.

  ?angambo (2007) wa?a na nufin sa?on da aka gina ne bisa tsararriyar ?a’ida ta baiti ko ?ango ta hanyar rerarawa da kuma samun kari ko bahari da amsa-amo ko ?afiya. Kenan za a iya cewa wa?a ta bambanta da zance nay au da kullum ta fuskar tsarawa da ?a'idoji.

  Takaitaccen tarihin Sa’adu Zungur

  An haifi marigayi Sa’adu Zungura shekara ta alif da ?ari tara da sha biyar (1915). Daga cikin ?abilar Hausawa. Ya samu ilmin boko da na Arabiya, sannan kuma yana da ilmin al?ur'ani mai girma, ya kuma yi aiki da ma’aikatan shari’a. Sa’adu Zungur y gama karatunsa a makarantar kwalejin Yaba dake garin Lagos yana ?aya daga cikin ?alibai ‘yan  Arewa na farko da suka dawo Arewa a matsayin malamai na makaranta a garin zariya sannan ya karantar a Bauchi a shekarar 1940 tare da malam Aminu Kano da Muhammadu Buba, haka kuma wa?annan mutanen guda uku sun yi yun?urin ?afa kungiyarsu ta siyasa a shekarar 1940.

  A shekarar 1950 Sa’adu Zungur ya zama sakatare na NCNC kafin daga baya ya bar wannan jam’iyar Sa’adu Zungur ya zama mawa?i a Arewa akasar Kano. daga baya Allah ya masa cikawa a shekarar 1958.

  Salon Wakar Sa’adu Zungur mai taken Arewa Jumhuriya ko Mulukiya

  Kafin mu yi bayani a kan irin salon da mawa?in ya yi amfani da shi ya kamata mu fa?i ma’anar salo shi kan sa. Salo dai za?i ne na marubuci wajen rubutu, marubuci yana da ‘‘yancin zabeen kalmomi da jimloli. Abubuwan da ake nazarta a ?ar?ashin salo wanda kuma daga kan sa ake yanke hukunci a ce salon marubuci ya kayatar ya y armashi ko ragon salo ne sun ha?a har da kalmomi da ya yi amfani da su wajen gina labarinsa.

  Malam Sa’adu Zungur ya yi amfani da salo mai sau?in fahimta wajen rubuta wa?arsa mai taken Arewa Jumhuriya ko Mulukiya inda ya yi bayani saosai gameda matsayn Arewacin Nijeriya da kuma yadda ‘yan  Arewa suka sa sharholiya a gaba  suka shantake ga kuma maganar ‘yan  daudu da karuwai da yadda sarakunanmu suka saki gaskiya. Misalin ka?an daga cikin baitocin wa?ar.

  Tuna baya wa?ar Sa’adu Zungur mai taken Arewa Jumhuriya ko Mulukiya kamar haka:

  Matukar Arewa da karuwai da,

             ‘yan daudu da su da magajiya.

  Da samari masu ruwan kudi da,

              Maro?a can a gidan giya.

  Matukar 'ya'yanmu suna bara,

              Titi-titi loko-loko Nijeriya.

  Hanyar birni da na kauyuka,

              Allah ba ku mu samu abin miya.

  Sun yafu da fatan bunsuru,

              Babu mai tariyansu da dukiya.

  Babu shakka ‘yan  kudu za su hau,

              Dokin mulkin Nijeriya.

  Inko ‘yan  kudu sunka hau,

              Babu sauran dadin, dada kowa zai sha wuya.

  Arewa zumunta tamu ce,

              Sai karya sai sharholiya.

  Camfe-camfe da tsibbace-tsibbace,

              Malam karyan ‘yan  damfara.

  Sai karyan kambon tsiya’

              Sai hula mai annakiya.

  Ga garin asali da na dukiya,

              Sai ka ce dan annabi fariya.

  Jahilci ya cika lakarmu duk,

              Ya sa mana sar?a har wuya.

  Ya sa mana ankwa hannuwa,

              Ya daure kafarmu da tsarkiya.

  Bakunanmu ya sa takunkumi,

              Ba zalaka sai sharholiya.

  Wagga al’umma mai za ta yi,

              A cikin zarafofin duniya.

  Mu dai hakkinmu gaya muku,

              Ko ku karba ko ku yi dariya.

  Dariyarku ta zam kuka gaba,

              Da kalamar mai kin gaskiya.

  Gaskiya ba ta neman ado,

              Ko na zabin mryar zabiya.

  Karya ce mai kunne bakwai,

              Da fari da baki ga rawaya.

  Ga kore ga kuma algashi,

              Toka-toka da ja sun gauraya.

  Babu shakka wa?annan baitoci sun isa su fargar da ‘yan  Arewa a kan irin abubuwan da suke faruwa a yau, a inda shi Sa’adu Zungur ya yi amfani da kalmomi masu sau?in fahimta tare da jimloli masu armashi wajen rubuta wannan wa?ar tasa, lallai za a iya cewa wannan salon nasa ya yi kyau ?warai da gaske.

  Jigo

  Shi dai jigo shi ne kashin bayan labari, wato shi ne makasudin da aka gina labari a kan sa, a kan sami babban jigo da ?ananan jigogi. To a nan za mu iya cewa jigon wannan wa?ar ta Sa’adu Zungur mai take Arewa jumhuriya ko mulukiya suna da yawa kamar haka:

  1.      Garga?i

  2.      Gaskiya

  3.      Yabo

  4.      Zaman banza ko sharholiya

  5.      Wa’azi da sauransu.

  Marigayi Sa’adu Zungur ya fara wa?arsa ne da yabon Ubangiji mai kowa mai komai, wanda ya yi adukkan halittun duniya. Shi wannan jigon na yabon Ubangiji ga misalin ka?an daga cikin baitocin kamar haka a inda ya ke cewa kamar haka:

  Ya mallaki dukkan talikai,

              Na kwari da tudu da samaniya.

  Da mutum aljan da mala’ika,

              Dabbar sarari da ta maliya.

  Mulki iko daula duka,

              Na ga sarki Allah shi ?aya.

  Shi yake ba wanda ya so duka,

              Ya sarauta a lardi duniya.

  Shi yake kar?e ta ga talikai,

              Don ya ?an?ani wahalar duniya.

  Shi ka cusa dare a cikin wuni,

              Kuma ya zaro hasken safiya.

  Shi ka rayarwa mamaci duka,

              Shi ke kashe mai rai shi ?aya.

  Ikonsa a kan komai yake,

              A ruwa da tudu da samaniya.

  Alwakilu mu dogara duk ga rai,

              Zahirinmu a ?oye  a zuciya.

  Mu amince zai mana taimako,

              Na ha?i?a inda mazajiya.

  To wannan ne jigo na yabon yana ?aya ne daga cikin jigogin wannan wa?ar a inda ya bayyana yabonsa ga Allah subahanahu wa ta’ala a ciki. Babban jigon wannan wa?ar ta Sa’adu Zungur mai taken Arewa jumhuriya ko mulukiya ita ce “gaskiya” shi ya hori sarakunanmu da yin gaskiya a yanayin gudanar da mulkinsu kamar yadda za mu gani a nan kamar haka:

  In za ka fa?i fa?i gaskiya,

              Komi taka ja maka ka biya.

  Haka ne Editanmu na gaskiya,

              Wanda ta fi dubun zinariya.

  Sai mu gode Allah shi ?aya,

             Don shi ne sarkin gaskiya.

   Ya jikokin Shehu biyu,

              Sai ku ?au tutarku ta gaskiya.

  Shehu Abdullahi ha?i?atan,

              Ya bar mana gadon gaskiya.

  Hijira da ta iske alwali,

              Sai ta ?arfafa tushen gaskiya.

  Ai Suleiman shi ne ja gaba,

              Kuma Dabo ya bi shi da gaskiya.

  Ga sarauta ga ilmi ciki,

              Ga adala shari’ar gaskiya.

  Arna da musulman Bauchi duk,

              Sun yi caffa don su ga gaskiya.

  Mallawa su da Barebari,

              Sun ga adalcinka da gaskiya.

  Duka sun san kai ne shugaba,

              Ka ri?e zarafinsu da gaskiya.

  A ?asar Adamawa da Ahmadu,

              Lami?o fitillun gaskiya

  Jikan modibbo Shuba?o sai,

              Ka tsare daularka da gaskiya.

  Ga Umaru Sanda da Gundiri,

              Malami ne ya san gaskiya.

  Ko ?awo yana shakka tasa,

              Ya gaje tutar gaskiya.

  Wa ya gaji maza suna gwamutse?

              Sarkin Sudanin gaskiya.

  Kar?e shi Abdul?adiri,

              Ka ri?e tutarka da gaskiya.

  Hakkin jama’a na kan su duk,

              Su ri?e igiyarsa da gaskiya.

  Farta ganda makairci duka,

              Sai a bar ta a binciki gaskiya.

  Dariyarku ta zam kuka gaba,

              Don nadamar mai ?in gaskiya.

  Gaskiya ba ta neman ado,

              Ko na za?in mryar zabiya.

  ‘yan  Arewa ku daina gaganiya,

              Ku ri?e daularku da gaskiya.

  Zaku rera fa?ar da-na-sani,

              Da na bi jawabin gaskiya.

  Insha Allahu mu tsarkake,

              Bisa fatan za mu bi gaskiya.

  Babu mai aiki bisa hankali,

              Da basira don ya ga gaskiya.

  To sarakai sai fa ku fargaga,

              Don ku gyara ?asarku da gaskiya.

  Mun gode Allah shi ?aya,

              Don shi ne sarkin gaskiya.

  A zahirin gaskiya, duk wa?annan baituka da muka kawo su a nan za a ga cewa dukkansu suna ambaton kalmar gaskiya, shi ya sa muka ce babban jigon wannan wa?ar shi ne yin gaskiya.

  Zubi da tsari 

  Salon garga?i, misalin baitocin salon garga?i malam Sa’adu Zungur ya garga?i ‘yan  Arewa da sarakunansu bisa ga hangen nesa da ya ji bisa kan mulkin Nijeriya kamar haka: 

  An sha bamban kan nufi,

              Na shirin mulkin Nijeriya.

  Niyar kudu in suka ?aukaka,

              Duk ?asa ta zamo jumhuriya.

  Ku fahaimci shiri na mulukiya,

              Da yawan ha?ari jumhoriya.

  Mulki na wakilan gurguzu,

              Babu sarki babu sarauniya.

  Sai ‘yan  sanda sai soja sai,

              Oda ita ce jumhuriya

  Fatanmu Arewa ta farga duk,

              Don ta gane lamarin duniya.

  Farfaganda makirci duka,

              Sai a bar ta a binciki gaskiya.

  Hudubobin kini bibi duka,

              Dangin zance na falaniya.

  Da sarakai sun fi ?ari biyar,

              Duka sun watse ba ko ?aya.

  Sai ka ce da dai ba a yi su ba,

              Kun ji sharrorin jumhuriya.

  Duk misalan nan na Amerika,

              babu mai kyau na shirin jumhuriya.

  ‘yan  Arewa ku daina ganganciniya,

              Ku ri?e daularku da gaskiya.

  To sarakai sai ku yi tattali,

              Na adala ban da haramiya.

  Sun yi ta kau bisa kanmu ko,

              Mun ro?i zumuntar duniya.

  Kar ku ru?u da zancen ja’iran,

              Masu son halakar Nijeriya.

  Za mu bika ka ja mu zuwa ga,

              Kar ka yarda Arewa ta wuya.

  Matu?ar Arewa da karuwai,

              Wallahi za mu ji kunyar duniya.

  Daga wa?annan baituka wa?ar Sa’adu Zungur ya yi maganganu na garga?i musamman a kan jamhuriya da ‘yan  Arewa da ya kawo misalan a rubuce. Dangane da nazarin wa?ar Sa’adu Zungur a cikin ?ananan jigon akwai “zaman banza ko sharholiya” yanzu za mu karkata akalarmu mu binciki yadda ya wa?e masu sharholiya da zaman banza (zaman kashe wando) musamman ma ga al’ummar Hausawa. Inda yake cewa:

  Matu?ar ‘yan  iska na gari,

              ‘yan  daudu da su da magajiya.

  Kai Bahaushe ba shi da zuciya,

              Za ya sha kunya nan duniya.

  Arewa zumunta ta mutu,

              Sai nisha?i sai sharholiya.

  Ire-iren wannan jawabin da ya yi duk zaman banza yake kawo su, sannan ga inda ya yi maganan karuwai da ‘yan  daudu, idan mutum yana da ?wa??waran sana’a ba zai shiga irin wa?annan hargitsi ba don mutum shi yak enema wa kansa mutunci.

  Shi kuma wannan jigo na wa’azi yana tafiya ne tare da maganar gaskiya ?in inda yah ore mu da gudanar da gaskiya a duk inda muka tsinci kanmu don hu?ubar yin gaskiya ma ai wa’azi ne ga misalin ka?an daga cikin wa?ar kamar haka:

  Ilimi, hikima addini duka,

              Da dabarar sarrafa duniya.

  Da aminci babu gwagwarmaya,

              Babu zalunci da hatsaniya.

  Hakki na ?abiloli duka,

              Na wuyanku ku sau?e lafiya.

  Daularku a kayin mumini,

              Da wasunsu taw aye lafiya.

  Wa’azi ne mulkin Indiya,

  Da ta zam daular jumhuriya.

  Wannan ka?an kenan daga cikin baitoci a kan jigon wa’azi.

  Zubi da tsari 

  Ya ?unshi labarin gaba?ayansa ne musamman muhimman abubuwa da suka faru a cikin labarin, wa?anda za a iya tunawa da su, kamar sunayen taurari manya da ?anana, wurare da garuruwa a cikin labari da yadda wannan marubucin ya sa?o wa?annan wuraren da kuma abubuwan da suka faru manya da ?anana.

  A nan tun da namu nazarin a kan wa?a ce to zubi da tsarin ma akan wa?a ce za mu yi kuma ya ?unshi wa?ar gaba?aya wato daga farko har zuwa ?arshe. Yanzu ?ari mu fara da sunayen manyan sarakuna na daular shehu guda goma sha ukun nan kamar su: Sarkin Kano Bayero da Bagauda, Suleiman, Sanusi Ciroma, Umaru Dallaji, sarki Abdullahi da Sarki Alhaji Usman Yakubu Yakubu na Maigari, Jafaru, Jafaru Modibbo Shu?a?o, Muhammadu mai Muri, Nda Yako Etsu, Umaru Sanda a Guddiri, Ahmadu, Abdu na ?adiri, Ibrahim Nagwamutse Kabeji, Abdul?adir, sarkin malamai sarkin Riron, sarkin Jukun, Shehu mujaddadi. Wannan mumin har sunan sojoji da ‘yan  sanda kai har da snan lugaed da su wajen rubuta wa?arsa.

  Malam Sa’adu Zungur ya yi amfani da sunan garuruwa da kuma wasu daga cikin ?asashen waje wa?anda za mu fara da sunayen garuruwan cikin Nijeriya, kamar haka: da farko akwai Bauchi, Kano, Zariya, Birnin Gwandu, Adamawa, Muri Gudduri, Misau, Gombe, ?aura, Ilorin Okene, ?asar Kuza, Abuja, Biron, Akure, Wukari, Binuwai, sannan ya yi magana a kan ‘yan  Arewa da ‘yan  kudu, sanna ya yi amfani da sunayen wasu daga cikin ?asashen waje ga ka?an daga cikinsu akwai: Amerika, Indiya, Pakistan, Ingila, Indonesiya, Sudan, London da Saudi Arebiya.

  Wa?annan su ne ka?an daga cikin sunayen ?asashe da ya Ambato a cikin wannan wa?ar. Sai kuma ?abilun ?asar Nijeriya musammam ?abilun Arewacin Nijeriya, ga ka?an daga cikinsu. Hausawa, Katsinawa, Daurawa, Mallawa, su da Barebari, Zagezagi, Nupawa Jukunawa Igala.

  Dangantakar wa?ar Sa’adu Zungur, mai take Arewa Jumhuriya ko mulukiya da halin da ake ciki a siyasar Arewacin Nijeriya a yau

  To yanzu zan karkata akala ta danganta wannan wa?ar ta malam Sa’adu Zungur mai taken Arewa jamhoriya ko mulukiya da siyasar Arewacin majeriya a yau.

  Da farko dai malam Sa’adu Zungur shi ne wanda ya fara ?afa jam’iyar siyasa a arewacin Nijeriya sannan kuma shi ne fitila na farko da ta fara haskaka jama’ar Arewa a cikin siyasa tun wajen shekarar 1940 ya ba wa abokansa sha’awar da su ?afa jam’iya, saboda haka aka ?afa jam’iyar abokai mai suna (zarias friendly society). Sannan kuma idan muka dubi maganar jam’iyar kuma tana nufin ?an ?ullalliyar ?asa.

  To kafin Arewa kuma ta zama jamhuriya said a manyan ‘yan  siyasa suka babban?aro na ?asa a shekarar (1950) akan cewa za su ci ga?a da zama a dun?ule ne ko da za a raba ?asar daga nan ne aka cim ma matsaya ?aya aka ha?e kar a rabu don ta zama ?asa ?aya.

  Sannan a ?angaren tarihin siyasar ?asar Nijeriya nan kuma za mu iya cewa a zamanin su sardauna wato da farko an yi siyasar gaskiya mai mutunci da kuma tsabta ga kuma ri?on amana, babu hasada kamar na yanzu su ‘yan  siyasa sun yi wa jama’ar su aiki sosai da gaskiya haka kuma sun sadaukar da kan su wajen bya wa jama’ar ?asa bukatunsu irin wa?annan ‘yan  siyasa ba su damu da tara wa kai dukiya ba sai dai su yi suna ba ruwansu da hargitsi dukansu kayukansu a ha?e yake zaka ga cewa akwai ‘yan  siyasar Arewa zancen tara abin duniya bai dame su ba sosai, su da Arewa ce a gabansu haka ma ta ?o?arinsu na kudu su ma kudancin ne kawai a gabansu yadda zasu kawo wa jama’arsu cigaba ba ci baya ba.

  A yanzu kuwa ga irin siyasar da suke yi shi ne ?azamar siyasa irin na danniya da mur?iya, misali idan ka tsaya takara ko da Allah ya baka nasara ba dole ne a baka ba in baka da ?an uwa a mulki sai a mur?a a ?auka a ba wa wanda yake da uwa a murhu. Sannan ga siyasar uban gida ga kuma cin hanci da rashawa wanda ta yi mana katut a kasarmu duk ya na?a ya daka cikin abin da yake hana ruwa gudu a siyasar arewacin Nijeriya. Sannan har yanzu akwai wani sabon abu da ‘yan  siyasa suka kawo misali kamar siyasar bangaranci wanda a da ?in ma akwai amma bai yi tasiri sosai kamar yanzu bat un da dai su Awolowo ya fito ne daga ?angaren yorubawa akwai Azikwe shi kuma Iyamuri ne  ga malam Aminu Kano daga Arewa amma duk bai hana su su ha?a kais u yi wa ?asa aiki ba. Sannan yanzu an kawo siyasa ta addini wanda a da babu shi, sannan ga ?abilanci kusan duk wannan a siyasan yanzu ne a ka ?ir?iro shi tun da dai babu shi a siyasar zamanin su sardauna.

  Idan aka danganta wannan wa?ar da siyasar Arewa a yanzu za a ga cewa lallai malam Sa’adu Zungur mutum ne mai hange nesa wanda tun tuninsa da basirarsa ta taimaka gaya. Inda yake yi wa jama’ar Arewa garga?i da su yi taka tsan-tsan a kan lamarin ‘yan  kudu. Da ma tun farko ma shi ma kansa sardauna sai da ya garga?i ‘yan  Arewa a kan mulkin ‘yan  kudu sannan kuma ‘yan  Arewa su gayara halayyarsu sannan kuma su ha?e kawunansu don su gudanar da mulki mai tsabta. Ga ka?an daga cikin baitocin da malam sa’adu ya yi bayani kan mulki misali.

  Addu’armu da musiba jimlatan,

  Ka kiyaye Arewa gaba?aya.

  Ilmi addini hikima duka,

              Da dabarun sarrafa duniya.

  Jahilci ya ci lakarmu duk,

  Da dabarar sarrafa gaskiya.

  Addu’armu ga Allah Rahimi,

              Ya kiyaye Arewa gaba?aya.

  Bamu da tsuntsu ba tarko duka,

              Wallah mun yi hasarar duniya.

  Jahilci ya ci lakarmu duk,

  Ya sa mana sar?a har wuya.

  Duk misalan nana na amerika ko,

              Mai kyau na shirin jamhuriya.

  in sun ka sake jama’ar kudu

              Suka hau mulkin Nijeriya”

   da?a ba mai sauran tambaya,

              Kowa ya san zai sha wuya

  An sha bamban bisa kan nufi,

              Na shirin mulkin Nijeriya.

  Niyar kudu in suka ?aukaka,

  Duk ?asa ta zamo jumhuriya.

  Mukam niyarmu a karkasa,

              Don Arewa ta za?i mulukiya.

  Ka fahimci shiri na mulukiya,

              Da yawan ha?ari jamhuriya.

  Mulki na wakilan gurguzu,

              Ba sarki babu sarauniya.

  Fatarmu Arewa ta fargaga,

              Don ta gane lamarin duniya.

  Domin fa Arewa da hargitsi,

              Da yawan ?arna ba kariya.

  Babu shakka ‘yan  kudu za su hau,

              Dokin mulkin Nijeriya.

  Wa?annan su ne baitocin da ya kawo a cikin wa?arsa, abin da yake faruwa a yanzu kenan kamar yana tsaye ne a wurin, amma duk abin da yake faruwa na mulkin ‘yan  gurguzu Allah zai iya maganinsa. 

  Sannan mai karatu na iya karanta: Tarihin wakokin baka na Hausa da wanzuwarsu

Comments

1 comment