A wata makalarmu ta baya mun yi matashiya akan tarihin manyan masana harshe da kuma irin gudumawa da suka bayar a fagen bincike da bunkasa ilimin harshe. Daya daga cikin wadannan masana shine Kenneth Lee Pike. A yau zamu kawo muku cikakken tarihinsa da kuma irin gudumawar da ya bayar a wannan fanni na kimiyyar harsuna.
An haifi Kenneth Lee Pike ranar 9 ga watan Yuni, 1912 a ?asar woodstok sannan kuma ya yi karatun addinin kirista wato Theology a kwalejin Gordon India ya yi digirinsa na farko a shekarar 1933. Kudirinsa ta farko ita ce ya yi aikin mishon a ?asar china. Lokacin da wannan damar ba ta samu ba sai ya wuce zuwa cibiyar nazarin harsuna summer institute of Linguistics) a Mexico domin nazarin harsuna a 1935 inda ya yi nazarin harshen Mixtec daga wurin asalin masu harshen. Bayan ya yi makarantarsa ne ya shiga aikin wallafe-wallafe litattafai a fannin harshe
A 1937 ne Pike ya tafi zuwa jami’ar Michigan, domin samun digirinsa na uku Ph.D. a 1942 ?ar?ashin jagorancin mai kula da aikinsa Charles C. Fries. Sannan binciken nasa da ya gudanar ya shafi harshen Mixtec ne, bayan kammalawarsa ne shi da matarsa Evelyn suka ?ir?iro da wata hanya ta rubutun harshen Mixtec. Daga wannan ne ya zama shugaban wannan cibiyar ta farko wato Summer Institute in Linguistics (SIL), babban ?udirin wannan cibiyar ita ce ta fassara littafin Injila zuwa harsunan da babu rubuce-rubuce a kai, wanda a 1951 ne ya wallafa wani littafinsa mai taken Mixtec New Testament. Wato sabon al?awari a harshen Mixtec.
Gudummawar Kenneth Lee Pike a fagen ilmin harshe
Wadannan sune kadan daga cikin irin ayyukan da Kenneth Lee Pike ya aiwatar a lokacin rayuwarsa.
Kuna iya karanta tarihin Leonard Bloomfield da irin gudumar da shima ya bayar a fagen ilmin harshe, ko kuma masan
in ilmin harsunan nan Noam Chomsky da kuma P??ini wanda shima ya gawurtacce ne a wannan fanni a tsohuwar kasar India, inda yayi rubutu masu tasiri akan nahwun Sanskrit, shararre daga cikin rubutunsa shine: A???dhy?y?. Sai kuma irin ayyuka da gudummawar mazhabar Prague.
No Stickers to Show