Noam Chomsky na daga cikin manya-manyan masana da wannan karni ko kuma wadanda duniya ke ikirari da su a halin yanzu. Makalarmu ta yau zata yi nazari ne bisa tarihinsa da kuma ire-iren ayyukan da ya gudanar kana har yanzu yake gudanarwa a fanninsa na ilmin harshe, wato linguistics.
An haifi Noam Chomsky a ranar 7/12/1928 a garin Pennsylvania na ?asar Amurka. Ya yi karatun digiri na ?aya B.A da na biyu M.A da na uku Ph.D a Jami’ar Pennsylvania na Amurka bai jima da fara aiki ba ya zama shaharraren Masani a ?angaren harshe wanda shahararsa ce ta sa ake masa la?abi da ‘Uban masana na ?angaren harshe na zamani’ sannan kuma shi jigo ne a fagen Falsafa wanda ya sadau?ar da duk lokutansa wajen neman ilmi. Hakan ta sa ya wallafa littattafai da adadinsu ya kai ?ari (100) wanda hakan ya sa aka ba shi lambar yabo tare da bayyana shi a matsyin jigo a ?angaren al’ada, kuma an za?e shi a sahun gaba cikin masana masu wallafe-wallafe a 2005.
Gudummawar Noam Chomsky a fagen harshe
Kasancewar Chomsky masani ne a fagen harshe, kuma idan aka yi la’akari da irin tarihin rayuwarsa kama daga karatunsa zuwa rubuce-rubucensa za a fahinci cewa akwai gudummawar da ya ba da daman gaske ga al’umma musamman a ?angaren harshe wa?andaba za iya kididdige adadinsu ba amma an binciko wasu daga cikin irin gudummawar da ya ba da kamar haka:
Ayyuka da Noam Chomsky ya gudanar a fannin ilmin harshe har ma da sauran fannoni irin su siyasa baza su tattaunu a wannan yar karamar makala tawa ba, don haka zan dakata anan, kuma in Allah Ya so zan kawo muku cigaban wannan aiki a wata makalar.
Sai dai kuna iya karanta wasu makalu irin wadannan da suka rigaya suka gabata game da tarihi da gudummawar masana harshe, misali, tarihin Kenneth Lee Pike wanda shima masanin harshe ne da kuma tarihin Leonard Bloomfield har ma da Ferdinand de Saussure. Akwai yan mazhabar Prague suma sun bada gudummawa mai yawa a fagen ilmin harshe.
No Stickers to Show