Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Gudummawar Mazhabar Prague (the Prague School) a fagen ilmin harsuna

Gudummawar Mazhabar Prague (the Prague School) a fagen ilmin harsuna

 • Mazhabar Prague (the Prague school) Wannan mazhaba ce da aka ?ir?ira a shekara 1926 a Café Derby na Prague da niyyar ha?aka harshe domin muhimmancinsa. Wannan mazhaba ta ha?a manyan masana harsuna. Daga cikin hanyoyin da suka tsara wajen gudanar da ayyukansu akwai na tsarinci na li’irabin abin da ya shafi adabi (Structuralist literary analysis) da kuma ra’in daidaitaccen harshe (the theory of the standard language) a shekarar 1928-1939.

  Daga cikin manbobinta da suka taimaka a wannan mazhaba akwai: Vilem Mathesius (1882-1945) da Roman Jacobson (1896-1982) da Prince Nikolai S. Trubetzkoy (1890-1938) da Bronislaw Malinowski (1884-1942) da J. R Firth (1890-1960) da M.A.K Halliday da R.A Hudson da sauransu. To wa?annan su ne masana a wannan mazhabar kuma sun ?o?arta wajen ?aga martabar harshe.

  Gudummawar Mazhabar Prague a fagen ilmin harsuna

  Taruwar wa?annan mutane wuri guda ba zai yi a banza ba, dole ne a samu sun taimaka wanda kuwa shi ne kudurinsu ta farko a cikin zuciyarsu. Amma babban kudurinsu shi ne: ?abbaka ayyukan masu a?idar tsarin bai-?aya tare da la’akari da ayyukan shaihin malami Ferdinand de Saussure. Ayyukansu na farko ya ta?o ilmin sautin harshe (phonology) ne wanda tunanin Trubetzkoy ne na kwatanci sauti ya samar da bambanci tsakanin ilmin tsarin sauti (phonetics) da kuma ilmin sautin harshe (phonology). Ya kuma ?ir?iro da wasu tsarin bambance su wanda Jacobson ya yi gyra a kai daga baya kuma Halle da Noam Chomsky suka yi nasu gyarar a fannin ilmin sautin harshe.

  Haka kuma sun ?ara fito da wata hanya da ta shafi tsarin ga?a (syllable structure) da karin sauti (tone) da rausayar murya (intonation) da yanayin murya (Suprasegmental Features) da kuma ilmin ginin kalma (morphology) da kuma tsarin ilmin sautin harshe da kalma (Morphophonology) da sauransu.

  Wa?annan kadan ke nan daga cikin ayyuka da gudummawar da wa?annan masana suka bayar a fagen ilmi musamman ma abin da ya shafi harshe.

  Kuna iya duba irin gudummawa da ayyuka irin wadannan na wasu daga cikin masana ilmin harsuna kamar su,  Kenneth Lee Pike, da Leonard Bloomfield, da Ferdinand de Saussure da Noam Chomsky da kuma P??ini

Comments

0 comments