Makalu

Shin ko ka san da tsatsa ake kera kamera?

 • Kimiyya da fasaha a kulli yaumin kara ci gaba ta ke yi kuma wannan ci gaba na faruwa ne a fannuka daban daban da ke cikinta. A yau bangarenmu na kimiyya da fasaha za mu yi dubi ne ga al'amarin keran na'uran daukan hoto wato camera a turance. Mai karatu na iya duba makalarmu da ta yi dubi ga kirkiran mutum mutumin tsuntsu da aka yi.  

  Ka dauka cewa tsatsan dake fitowa a jikin kwano ko karfe bayada amfani ko? To ka kasa kunne ka ji, duk wata camera a duniya da tsatsa ake sarrafawa kama daga kamera na waya da duk wata kamera na daukan hoto. Kada ka raba dayan biyu, duk haduwar kameran wayarka da tsatsa aka hada shi.

  Ana kiran wannan kamera da suna CMOS camera. "C" yana nufin complementary, "M" na nufin metal, sannan "O" na nufin oxide, kana "S" kuwa yana nufin semiconductor. Lafazin complementary ainihi an samo ne daga kalmar complement wanda yana nufin some thing which is complete, wato cikakke. Shi kuwa kalmar metal ba sai na fassara shi, kowa ya san karfe ake nufi. Kalmar oxide kuwa ainihin kalmar daga oxygen ne, wato iskan da muke shaka kenan.

  Babu shakka yau nazo da abinda sai mutum ya gamsu da ire-iren bincike da nake yi, ko kuma wanda ya san chemistry zai iya yadda da bayanin da zan yi yanzu.

  Idan aka ce metal oxide to ana nufin karfe da oxygen sun yi reaction da juna, wato sun hadu. A duk lokacin da ruwa ya taba jikin wani karfe zaka ga tsatsa ta fito, saboda a cikin ruwa akwai oxygen, wannan oxygen din shi zai yi reaction da wannan karfen. Bayan dan kwanaki kadan sai ka ga tsatsa ya fara fitowa, haka kuma shi yasa idan ruwa ya taba karfe, idan iska ya hura wannan karfen za ka ga tsatsa zai biyo baya. Kuma shi yasa ake so ayi maza a saka wani mai ko abinda zai hana tsatsan fitowa.

  Shi tsatsa idan ya fito yana hana karfe karban wutan lantarki, koda ya karbi wannan wutan kuwa to zai karba ne amma bawai da kyau ba kamar yadda karfen da baida tsatsa zai karba ba. To sai karfen da yakeda tsatsan yarikide yazama semi conductor, wato semi ana nufin matsakaici, shi ba good conductor ba kuma shi ba bad conductor ba, wato yana tsaka-tsaki.

  Ita kuwa na'urar komfuta shi tsatsar take so wajen tsara kwakwalwar kamera na waya da sauran kamerori dake jikin wasu na'uran. Dalilin da ya sa ake kiran wannan kamera da ake hadawa da tsatsan da suna complementary metal oxide semi conductor.

  Ina fatan masu karatu sun gane sirrin yadda abin yake. Har ila yau, ba kawai kameran waya ne ake hadawa da tsatsa ba, har ma da RAM na komfuta da shi ake hadawa. Sai dai akan sarrafa tsatsan yadawo normal one bawai yadda yake ake ganinshi a jikin karfe ba. Hoton dake sama misali ne na kwakwalwan kamera wanda aka hada shi da tsatsa. Zaka ga alamanun tsatsan a cikin gilas.

  Ashe dai tsatsa ma yana da amfani wa dan adam. Don karin bayani sai a duba littafin nan mai suna: The circuit design and simulation, third edition, shafi na 770, da kuma littafin The introduction to VLSI system, shafi na 840.

  Allah Shi kara mana imani da kuma tauhidi, amin. Sannan mai karatu na iya duba makalarmu da ta yi bayani kan kimiyyar batiri (battery): kirkiro shi, ci gabarsa da kuma inda aka kwana.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

View All