Skip to content

Dalilan da ke sa maza gujewa mata masu dogaro da kansu

Share |

Tun farko Allah ya halicci maza da son su ga cewa a komi sune kan gaba. Musamman a Arewa inda aka fi sanin cewa a komi namiji ne kan yi jagoranci. Ba kasafai a kan samu macen da ta fi namiji kudi ba, ko a fannonin aikin gwamnati mazan ne kan yi shugabanci, haka a bangarori na siyasa ba kasafai ake samun mata ba. Har ya zamo kamar abin kunya ne a samu mace da harkar siyasa. 

A wannan karnin, mata basa bukatar izinin namiji don daukar dawainiyar rayuwar su da kuma cin buri a kanta.  Abun takaici, akwai wasu mazan wadanda mata masu dogaro da kansu ba su daukar hankalin su sosai har ta kai wasu kan ji tsoron tunkarar matan. 

Ita mace mai dogaro da kai ba ta bukatar yardar wani saboda ta yarda da kanta. Tana kula da kanta sosai ta kowane fanni, a zahirance, a hankalce, a ruhinta da zamantakewa, kuma ba ta dogara da wani ya yabe ta don ita ta yarda da kanta. 

A bincike da tattaunawar da na yi da wasu daga cikin maza da mata, sun bayyana mun ra’ayoyin su kamar haka;

Sheik Sheik yace, “Hakkin ciyarwa, shayarwa, tufatarwa Allah ya dora su akan maza ne, shiyasa Allah ko wajen rabon gado ya fifita rabon maza akan na mata.

Mafi yawancin mata kudinsu nasu ne koda kuwa mijinsu yana cikin halin kunci basu iya taimaka masa, wasu kuwa in har sun taimaka sai sun yi gori. Hakan ina ga yana cikin dalilin da yasa wasu mazan basu so matansu su fisu a komai na rayuwa”.

Sadiq ya bayyana mana ra’ayin shi inda yace “Idan mace ta samu kudi tana jin cewa, bata da bukatar kulawar namiji. Ai shi ne raunin nasu”.

Usman yace “Ai gaskiya ko ni kaina bana son ganin matata ta fi ni kudi, a taƙaice sai dai idan Allah yaso ba yadda zan yi, amma in dai da amincewa ta ba zan bari ba”.

Mata ma ba a bar su a baya ba wajen fadinra’ayoyinsu.

Malama Maryam ta shaida mana cewa, “Wallahi haka ne, hassada ce kawai don nima ya faru dani muna tare shekara biyu ya samu aiki a banki. Nima bayan yan shekaru ƙalilan na samu aiki. Wallahi har iyaye sai da suka shiga shi ba zai aure ni ina aiki ba. Cikin yardar Allah babana ya tsaya min yace mishi aiki dole. Yanzu zamu yi aure wata mai zuwa In Shaa Allah”.

Ita kuwa Aysha cewa ta yi “Wani namijin ko yafi ki arzikin ma baya so ko yan canji ya ga yana gilmawa a hannunki sai ya raba ki da su, ya fi so ya ganki kullum Tass! Talauci kamar beran masallaci idan ya ga babu tayi yawa ya dan sammiki (karbi karki rasa) wai shi a tunanin sa za a fi zama lafiya, ke da shi kullum a hakan, Allah ka shirya maza masu wannan hali”.

Mun tattauna da Asma’u wacce irin hakan ya faru da ita. Ta bayyana mana irin halin da ta shiga. 

“Gidanmu gidan yan boko ne, mahaifina baya aurar da mace sai ta yi digiri, akwai yayyena mata da har digiri na biyu sun yi kafin su yi aure. Nima bayan na kammala digiri na samu aiki kuma albashina na da tsoka ya wuce dubu dari, kuma ina sana’ar siye da siyarwa. Har ta kai ina zuwa Dubai saro kaya har na bude shago. Na hadu da maza da dama wadanda sai tafiya ta mika sai su ce nafi karfinsu. Wasu su ce ai ni matar manya ce. Na fuskanci ƙalubale da dama kafin Allah ya sa inyi aure”. 

Kadan kenan daga cikin tattaunawar da na yi da wasu dangane da ra’ayinsu a kan wannan maudu’i. 

A wannan zamanin da ake ciki da wuya mutum ya je ma’aikatu ya iske maza kadai, wasu ma’aikatun za a iske 40% mata, wasu kuwa 50/50 ne. Yanzu ta kai babu bangaren aikin da ba za a iske mace a ciki ba, har wadanda a ka san da maza kadai ake samu a irin wadannan ayyuka. Misali tukin babbar mota, keke mai kafa uku duk ana samun mata a ciki. Duk suna hakan ne don su dogara da kansu.

An wuce zamanin da mata kan kunshe kansu a cikin gidaje, ba su sana’ar komi, miji shi ne jagaba a komi, sai abinda ya kawo za a yi amfani da shi.

Maza ba sa son mata masu son dogaro da kansu saboda matsayinsu ba zai rayu ba idan babu gimbiyar da za ta nemi taimako. Saboda haka, maza suna buƙatar macen da zasu shagwaba, wacce take a karkashin ikonsu, ba wacce zata iya yi ma kanta komi ba.

Yanzu, ga manya-manyan dalilai da kan sa namiji ya gujewa mace mai dogaro da kai.

– Mata ma su dogaro da kansu na da kudinsu.

Matan wannan zamanin suna da ƙwarewa fiye da kowane lokaci, musamman bangaren na aiki na cikakken lokaci da wajen tallafawa kanta da kuɗi shiyasa wasu ke ganin ba su bukatar tallafawar wani, duk da haka yana da kyau a matsayin ki na mace a ce yau ga mijinki ya ba ki kyauta ko ya  biya ma ki wasu bukatunki na kudi, hakan zai sa ya ji cewa shi ma namiji ne kamar sauran maza. Su fa maza suna son a buƙace su, don haka nunawa namiji cewa ki na da karfin tattalin arziki da kan ki abin tsoro ne.  Sai ya fara tunanin mi zai iya ba ki wanda ba za ki iya samarwa kanki ba?

– Mata masu dogaro da kai su kan nuna wayewa da gogewa a fannoni da dama.

Maza suna son a ce sune ma su fifiko fiye da mata. Su na son su ga cewa su ne su ka koyawa mace abu, duk wata gogewa a wajensu ta koye ta. Kuma su na son a ce komi suka yi daidai ne, ko da hakan ba gaskiya bane. Ta bangaren mata masu dogaro da kansu suma su kan nuna wannan isar ta cewa komi suka yo daidai ne, kuma yawanci zasu yi amfani da duk wata hanyar da ta dace don tabbatar da hakan. Wannan yana da matukar wahala a cikin dangantaka saboda maza suna ƙin jinin ƙaranta kuma galibi ba sa son a ce mace ta fi su wayo. Amma ya kamata mu fahimci cewa wani lokacin idan muka fita daga hanyarmu don tabbatar da cewa ba daidai suke ba, yana sa su ji kaskanci babu wanda yake so a mai da shi wawa. 

Idan har mace za ta kiyaye hakan tsab za su zauna lafiya da namiji. 

– Mace ta nuna ba ta bukatar namiji.

Tana son namiji, amma ba ta BUKATAR shi. Mata masu dogaro da kansu suna aiki tuƙuru, suna wadatar da kansu, kuma suna iya samun duk abin da suke so na buƙata don kansu. Wannan yana matukar tsoratar da maza.  Maza suna son jin cewa ana buƙatar su. Suna son lokacin da mace ke buƙatar su, musamman a irin ayyukan da maza a ka sani da yin su. Suna son jin kamar suna da abin da zasu ba mace wanda ba za ta iya yi ko samu da kanta ba. Amma mata masu dogaro da kansu sun bambanta. Suna da amfani. Ta yiwu ta riga ta san yadda ake yin abubuwa da dama kuma tana da wasu dabaru da take amfani da su a lokacin da bukatar hakan ta taso. Za ta ga ai za ta iya yin abubuwa da dama ba tare da ta nemi taimakon kowa ba, wani sa’ilin ma namijin zai nuna bukatar taimakawar sai ita ta nuna cewa ai za ta iya ba wani abu ba ne mai wahala da za ta kasa yi. A dalilin haka sai namiji ya ji cewa shi baida wani amfani a zamantakewar su saboda duk wani abu da zai yi ma ta da ka iya nuna cewa shi ne gaba da ita tana nuna bata da bukata. 

– Abinda yake shine, idan mace ta kasance mai ilimi da gogewa sosai fiye da namiji, to da alama namiji zai iya tambayar kimar sa.

A irin al’ummar da mu ka taso ba abinda a ka koya mana kenan ba. Saboda maza sun ƙi jinin a ce suna shakkar kansu. Akwai imanin cewa mata masu dogaro da kansu da masu nasara suna da halayyar rashin girmamawa.

Wasu mazan na ganin cewa daukar nauyin bukatunsu da matan kan yi  na daga cikin babban dalilin da yasa mata suke ƙin girmama abokan zamansu. Don haka lokacin da mata za su iya biyan waɗannan bukatun ba tare da wani taimako daga namiji ba, sai su fita daga cikin iko, su zama marasa girmamawa kuma ba masu ladabi kamar yadda ya kamata ba. Tabbas, wannan wani ra’ayi ne mara kyau. Ba duk mata masu dogaro da kansu bane ke raina mazajensu. 

A takaice dai, mutane suna buƙatar sanin cewa mata suma suna son su zama masu samun nasara da samun ci gaba a rayuwa kuma a lokaci guda su sami ƙauna ta gaskiya kuma su gina iyalai masu farin ciki kamar maza.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading