MARUBUTA » Hira da Baki » Bakonmu Na Mako: Tattaunawa da Farida Musa SWEERY

Event Details

Mahalarta

This event has 5 guests.
 • Attending
 • Mukhtar Musa Karami Abu Hisham Cinikin mutum ake kamar yanda ake cinikayya a kasuwa,farashi suke yanke wa kamar yanda ake yi a super market,basa yin ragi balle su nuna alamar sauki,idan ka biya kudi su baka,idan ka ki biya su kasheshi. Basa tsoron kowa,balle su yi tunanin akwai wanda zai iya tunkararsu,dole akwai abin tsoro fa,kasar nan ta mu akwai firgici sosai,Ya Allah ka karemu daga wannan masifar ta satar mutane. Allah ka bamu lafiya da zama lafiya amin
  Attending
 • Hauwa'u Muhammad *MUNA YIWA BAKUWARMU BARKA DA ZUWA* *_GA WASU DAGA CIKIN TAMBAYOYINMU GA BAKUWA_* 1_ *Menene sunan baƙuwar mu?tare da ɗan taƙaitaccen tarihi* 2_ *Me ya ja hankalinki ga sha'awar fara rubutu*? 3_ *A wace shekara ki ka fara rubutu?kuma wane littafin ki ka fara rubutawa*? 4_ *Nawa ne adadin litattafan ki?Kuma wanne ne Bakandamiyarki*? 5_ *Wane ƙalubale ki ka taɓa fuskanta a harkar rubutu*? 6_ *A cikin litattafan da kika rubuta, wanne ne yafi ba ki wahala wajen rubutawa?kuma wanne ne yafi yi miki sauƙi wajen rubutawa*? 7_ *Ta ya kike samun Jigo wajen rubutu? Sannan menene yafi ba ki wahala idan za ki yi rubutu*? 8_ *kina da Uban gida a rubutu?ko wanda ya koya miki rubutu ko ya ke duba miki bayan kin kammala*? 9_ *Ya za ki bayyana tasirin da Marubuta su ke da shi a cikin al'umma?shin saƙon da su ke rubutawa yana isa ga al'umma kuwa*? 10_ *A duniyar Marubuta wanene Tauraron ki,ko tauraruwar ki? ko kuma wanene/wacece Madubin dubawarki*? 11_ *Wace Shawara za ki ba wa marubuta a kan harkokin bunƙasar rubutu da cigaban Marubuta*? 12_ *A cikin wannan gida na Bakandamiya wane shiri ne yafi burge ki a cikin waɗan da aka fara gabatarwa?Sannan idan a ka ba ki zaɓi su wa za ki zaɓa a matsayin taurarinki masu burgeki*?
  Attending
 • Sadik *_SAKON TA'AZIYYA DAGA PEN WRITERS ASSOCIATION._* *_Assalama alaikum warahamatullahi wabarakatuh._* *INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN!!!* _A madadin daukacin mambobin kungiyar marubuta ta *PEN WRITERS*, ina amfani da wannan dama wajen mika sakon gaisuwar ta'aziyya ga 'yar uwarmu Asma'u Abdullahi *(Ummyter Bingyel)* wacce ta yi rashin mahaifinta. Babu shakka wannan babban rashi ne da ba za'a taba mantawa ba, muna taya ki alhini._ _Muna addu'ar Allah Ubangiji ya jaddada rahama a kabarinsa, Allah ya yafe masa dukkan kura-kuransa. Allah ya kyautata makwancinsa ya sa Aljannar Fiddausi ce makomarsa da mu baki daya._ _Bayansa da ya bari muna rokon Allah ya ba su hakuri da juriya bisa wannan rashin da suka yi. Allah ya yi musu albarka Allah ya kara inganta rayuwarsu._ _Wasaalam alaikum!_ ```Signed:``` *_Pen Writers_*
  Attending
 • Muttaka A. Hassan Ga ta nan ga ta nan ku!
  Attending