Guest Responses
-
-
Haleema Hassan Leemat
day 4
Allah ka yafemana Allah ka jikanmu Allah kazama gatanmu
Allah ga bayinka Allah kadafa musu
Maybe Attending
-
-
Jannat
Allah ni har yanzu ban gane kan bakandamiyar nan baπ°
Attending
-
Sadik Abubakar
Assalama Alaikum.
Bakandamiya, don Allah mene ne amfanin "My credit"?
Attending
-
Abubakar Saleh (Zamani Writers Ass.)
*Baby Khausar Complete Document*
_Na Layuza Kabir Adam_
Domin sauke littafin a wayarku Danna Kan hoto ko blue din rubutu dake kasa
ππΌππΌππΌ
http://www.aihausanovels.com.ng/2021/02/baby-khausar-complete-document.html
Like our Facebook page Fb.me/Aihausanovels
Attending
-
Yusuf Yahaya Gumel
MAGE CE AJALINA.
Marubuci.
Yusif Yahaya Gumel.
Cigaba
6.
D'ansandan ya nuna yarinyar.
"Ke kuma fa ya sunanki?"
"Sunana Mimi"
"Me ye alakar ki da wannan?
Ya nuna Habu cuwa-cuwa.
"Yaya ne, amma ba cikakke ba"
D'a sandan ya kara girman mamakinsa, a lokacin da Habu ya cigaba da dubanta yana huci.
"Kamar ya ba cikakke ba me ki ke nufi?
"Ina nufin Uba kawai mu ka had'a ban da uwa."
Ya kalli Habu cuwa-cuwa.
"Hakane?
" I hakane."
Akwai alamar takaici a amsarsa.
"Da kyau kin ji dai duk bayanin da ya yi bisa kararki da ya kawo da tuhuma me za ki iya cewa."
"Duk abin da ya fada kusan hakane."
"Me yasa ya zamo kusan?"
"Saboda abu biyu ba gaskiya ba ne"
Ta ba shi amsa.
"Abu biyu dame- dame"
"Sunana Mimi ba Amina ba, sai kuma d'an da yace na b'atar ba ni na batar ba"
Habu cuwa-cuwa da ke gefe ya cigaba da ciza yatsa irin yanayin fuskarsa kawai za ka kalla kasan taf yake da ita.
"To idan ba ke ki ka batar ba ya a ka yi?
"Na fita da shi tabbas, amma sace shi a ka yi"
"Sata kuma kamar wani tsanar roba, kar ki zo da rainin hankali mana nan fa ba gurin wasa ba ne, ki shiga taitayinki kafin na jefa ki a cell, na rufe."
D'ansandan yace a fusace.
"Ofisa ka daina wahalar da kanka fa wannan shegiyar yarinyar nan babu abin da ba za ta iya aikatawa."
Ya bude baki da niyyar mayar da magana sai ga wani kurtun d'ansanda ya shigo.
Tare da wasu mutane uku, mata biyu da kuma namiji d'aya.
Ya kame tare da sara masa yace.
"Oga wannan matar kara ta kawo "
Ofisan da ke kanta ya kalli matar da ke tsaye tana kuka ta birkice duk kammaninta ya canja a shekaru za ta iya kai wa arba'in da takwas ko hamsin da motsi.
"Ya dai me ya faru?
" Na kawo karar tsinannniyar yarinyar nan, ina so a kasheta kawai."
Matar ta fad'a cike da yanayi na zaucewa da fusatar zuwa."
Habu cuwa-cuwa da kanwarsa Amina, ko Mimi kamar yadda tace suka mayar da hankulansu.
"Me ta yi da za a kasheta."
Cikin sautin murya tace.
"Kisan kai ta yi"
"Kisan kai fa ki ka ce?"
Akwai alamun razana a fuskarsa.
Su kansu su Habu sun gyara tsayuwa suna kallon yarinyar da a ka ambata ta yi kisan kai.
"Kafin nan, ki nutsu ki fadamana me ya faru ya sunanki, kuma menene adirishenki ki mana bayanin yadda abun ya faru"
Sauran 'yansandan guda biyu suma sun shiga rudani cike har da mai daukan (statament) na abin da ya faru.
"Sunana hajiya Binta, ina zaune ne a babban layi, wannan yarinyar da na kira shegiya kuma tsinann..."
"Dakata hajiya ki kaucewa aibatata har sai an tabbatar da laifinta tunda zargi ki ke ko?"
"Ba wani zargi ofisa a gabana a cikin taron al'umma ta yi kisan."
Ya jinjina kai cike da mamakin yadda mai kisa zai yi a bayyanar mutane, kuma ma wannan yarinyar karama.
" To muna jin ki cigaba."
"Na fito a kan idona da karfe ta yi amfani har sau biyu ta kashe mun mage ta, wallahi yarinyar nan sai ta mutu ta karasa maganar tare da rushewa da kuka.
"Mage fa ki ka ce, idan na ji."
"I ita ko mage ko kyanwa, ko kuliya, koma ya ku ke kiranta ita ta kasheta akwai tulin shaidu a waje da ba su samu shigowa ba idan an bukata a gabansu komai ya faru."
Duka jami'an tsaron uku sun cika da mamaki, sun fi shekaru goma suna aikin nan, ba su taba cin karo da k'ara makamancin wannan ba.
Ya juya ga yarinyar da a ke tuhuma wadda hawaye ke sintiri a fuskarta ba ta damu da gogewa ba.
" Ya sunanki?
"Sunana Maryam."
"A ina ki ke?"
"A babban layi na ke nima."
"Da kyau kina ji duk abin da wannan matar ta ambata a kan ki me za ki iya cewa da gaske kin kashe mata mage?"
"I na kasheta."
"Meyasa laifin me ta mu ki?
"Ba wani laifi, kawai kashe ta na yi, saboda na tsani mage duk inda na ganta sai na kasheta."
"Ka ji ko ofisa ka ji abin da ta ke fada da kanta wallahi idan garin nan duk gatanta ne, itama sai an kasheta."
Hajiya Binta ta hayyako da masifa da hargagi."
Attending