MARUBUTA » Hira da Baki » Filin Bakon Mako: Tattaunawa da Bello Hamisu Ida

Event Details

 • A cikin shirinsu na ‘Filin Bakon Mako’ na wannan satin, Maryam Haruna da Hauwa'u Muhammad, za su tattauna ne tare da wani hazikin marubuci, Bello Hamisu Ida.

  Ku biyo mu a cikin shirin ranar Talata 24 Novemeber in Allah Ya kaimu.
 • Date
  11/24/20
  Time
  10:00 AM - 6:00 PM
 • Where
  Taskar Bakandamiya Map
 • Led by
 • Category
 • RSVPs
  • 6 attending
  • 1 maybe attending
  • 2 not attending
  • 0 awaiting reply

Mahalarta

This event has 9 guests.
 • Lawan Dalha Just a test post to see that....
  Attending
 • Ummyter Abdallah Madam din Dana kewa aiki jiya ta aikeni na sayo mata semo 2kg,danaje shagon sai na tarar sai 1 kg,so na dawo ban sayo ba shine tace min ni Wawa ne bana amfani da hankalina na sayo 1kg guda biyu ya zama 2kg Kennan idan an hada,na bata hakuri dai ta hakura,yau kuma tace na sayo mata slippers number 8,danaje babu sai lamba 4 shine na sayo lamba 4 guda biyu,na kawo batace komai ba Naga tana hada mini kayana cikin jaka,shine nake tambaya ko wanki zatayimin koko daki zata canjamin🤪🤪🤪
  Attending
 • Maryam Haruna A rayuwata babu abin da nake so kamar kallon finafinai na tsoro da firgici hakan na min daɗi sosai wanda hakan yasa ko kallo zan yi bana kallon wanda na san babu wani abu da zai firgita mutane. Ko a makaranta abokan karatuna duk sun san wannan hali nawa,wani lokaci su kan bani shawara a kan in bari kada wani abu ya faru da ni amma da rana ɗaya ban taɓa sauraronsu ba tunanina ma yanda zan sa musu son fara kallon irin finafinan da nike yi ƙila hakan zai sa su fahimci abin da nake nufi da son waɗan nan abubuwan. Mu uku muke ɗakinmu na makaranta,kullum cikin hana ƴan ɗakinmu bacci da hayaniya in Ina kallo. Sun yi duk yanda zasu yi don hanani wannan ɗabi'ar amma hakan ya faskara,don bani da lokacin da nake jin daɗin kallon fim ɗin tsoro sai sha biyu na dare. Ashe ƙaddara ce ke bibiyata ban sani ba. Wata rana daga makaranta aka kai mu asibitin mahaukata wacce ke bayan gari kusa da maƙabarta. Na ji daɗi sosai don wasu finafinai da nike kallo yawanci a asibitin mahaukata ake bada tsoro duk tunanina tunda mun zo hakan zata faru ga waɗan da muka zo tare don ni bana saka kaina saboda ni na san na saba kallo to tsoron mi zan ji kuma. Ranar da ba zan manta da ita ba ita ce: bayan satinmu guda a asibitin ranar ina aikin dare sai na dinga jin kamar ana kuka sannan ana jan wani abu kamar ƙarfe cikin wani ɗaki da ke kusa da inda nake zaune. Wata mata ce ciki wacce tun da muka zo asibitin magani ko abinci kawai ke sa a buɗe ɗakin saboda yanda take duk wanda ya shiga ɗakin ƙoƙarin kashe shi take yi hakan yasa aka daina zuwa wajenta sai dole. Da farko na share saboda na san matar da ke ciki zata iya yin komai duba da yanda ciwonta yake amma kuma sai na ji abubuwan sai ƙaruwa suke yi,wata zuciya na cewa na duba wani gefen na gargaɗina a kan kada na je. Da dai na ji abin ya wuce tunanina ƙarar sai damuwata take yi hakan yasa kawai na tashi don zuwa ganin menene. Ina tashi sai wutar ɗakin ta dinga rawa kamar zata ɗauke. Ban damu ba na kunna fitilar wayata don in gani da kyau. Tura ƙofar ɗakin na faɗa ba tare da jiran wani abu ba,abin da na gani ne ya kusan sani sumewa. Wata halitta ce kusa da matar nan tana mata wani abu da na kasa gane meye matar dai kwance take kamar babu rai tare da ita wannan halittar sai zuƙar jinin jikinta dake ta malala ƙasa kamar ruwa . Hakan da na gani ya mugun tsoratani har ban san na saki wayata ba ashe dai duk rashin ganin tsoron da nake cewa bana shaci daɗi ne don ban gani a zahiri bane, ƙarar faɗuwar wayar yasa wannan halittar ta juyo inda nake cikin sakan ɗin da bai wuce goma ba na ƙare mata kallo. Ƙaton kai ne da ita kamar ƙwllo,wuya kuma ba kauri sai kace mariƙar lema. Ido guda gareta kuma a tsakiyar kai yake, ƙafafuwanta sun kusan shida ga wani gashi da ya rufe mata jiki wanda ya ƙara maidata abin tsoro. Ganin ta juyo inda nake yasa da sauri na zabura da gudu zan bar ɗakin ai kafin ƙyaftawar ido na ga ta kusa zuwa inda nake ban yi ƙasa a guiwa ba na ƙara azama wajen gudun da nake son yi. Ita ma kokarinta ta zo inda nake don lahanta rayuwata na yi gudu sosai kaɗan ya rage in buɗe ƙofar fita baƙi ɗaya sai kawai na ga kare bakin ƙofar gashi ya buɗe baki da alama jira yake na ƙaraso wajen shima ya illatani. Ganin haka na yi shahada tare da canja waje zuwa makewayin dake ɗakin sai dai me kafin in kai na hango wani mutum mai mugun tsawon da duk iya ganina na kasa ganin ƙarshensa,gashi kayan jikinsa baƙi wuluƙ da dai na rasa yanda zan yi kawai sai na rufe idona ina jiran mai faruwa ta faru. Ban san me ya faru ba sai dai na buɗe ido na ganeni kwance saman gado an ɗaureni da igiyoyi a yanda na ji ana magana wai sati na guda kenan da haukacewa kuma duka nake yi don haka aka ɗaureni yanzu haka mafita nake nema yanda zan faɗa musu cewar ba hauka nake ba.
  Attending
 • lawal usman SLM barkanmu da ranar juma'a mai albarka Allah yakarbi ibadunmu kuma yasaukaka mana kuncin rayuwa
  Not Attending
 • Sadik *_SAKON TA'AZIYYA DAGA PEN WRITERS ASSOCIATION._* *_Assalama alaikum warahamatullahi wabarakatuh._* *INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN!!!* _A madadin daukacin mambobin kungiyar marubuta ta *PEN WRITERS*, ina amfani da wannan dama wajen mika sakon gaisuwar ta'aziyya ga 'yar uwarmu Asma'u Abdullahi *(Ummyter Bingyel)* wacce ta yi rashin mahaifinta. Babu shakka wannan babban rashi ne da ba za'a taba mantawa ba, muna taya ki alhini._ _Muna addu'ar Allah Ubangiji ya jaddada rahama a kabarinsa, Allah ya yafe masa dukkan kura-kuransa. Allah ya kyautata makwancinsa ya sa Aljannar Fiddausi ce makomarsa da mu baki daya._ _Bayansa da ya bari muna rokon Allah ya ba su hakuri da juriya bisa wannan rashin da suka yi. Allah ya yi musu albarka Allah ya kara inganta rayuwarsu._ _Wasaalam alaikum!_ ```Signed:``` *_Pen Writers_*
  Attending
 • Jidda Washa Shahararriyar matashiyar marubuciya, mai suna Adam Hauwa'u Suleiman wacce duniyar Marubuta ta san ta da Jidda washa. Ta zage ta zazzago wani sabon littafi mai suna MUMTAZ. Littafi da ya kunshi soyayya madararsa, tausayi, Amana, Rudani, Rikici, da dai sauransu. Ga Masu son wannan Littafi da zai dunga zuwa muku a saukake Wanda ba sai mun wahalar da Masu karantawa ba, don haka muka fitar da hanya saukakka. Ta hanyar Sauti a cikin Shafin mu Na YouTube channel mai suna JIDDA TV Channel. Kuna shiga Shafin ku danna alamar kararrawa wato ku yi mana subscribe gami da Like. Muna alfahari da ku masoyan mu. TALLA "A Lami! Ina zuwa haka cikin wannan rana mai kuna da zafi na ganki ga ba daya a birkice, dubi takalmin ki wari da wari ko dai ba lafiya ne?" "Uhmm Tabawa kenan ki bar ni garau nake, shahararriyar matashiyar marubuciya wacce aka fi sani da Jidda washa, ce ta saki sabon littafinta Wanda nake ba ki labari" "To fa! Wannan wani littafi ne haka da ya sa kika rude kamar Wanda a ka biya wa kujerar Hajji da umara?" "Tabawa ba dole na rude ba kin san iya tsahon lokutan da na kai ina dakon wannan littafin?" "Lami ta ya ya zan sani" Hhhhhhhh lallai fa "to ai na dade ina jiran in ga fitowar wannan littafi, Sai ga shi rana tsaka ta fitar da shi " "to fa ni fa har yanzu kin sa ni a duhu wai mai sunan littafin kuma wani darasi yake dauke da shi?" "Yanzu ko zan fayyace miki sunan littafin da darasin da yake dauke da shi, wannan littafi mai suna MUMTAZ" "keeeee yanzu wannan littafin ne ya fito?" "Kwarai kuwa" " to ai Lami ki ce faduwa ce ta zo daidai da zama ni kai na dakon fitowar littafin nake, yadda kika san kin min albushir da Auren Gwamna" hhhhhhhh "lallai kina budurin ki" "ai ina ga yanzu binki zan yi cikin azama nima in sayi littafin tunda naga akwai darasuka a ciki" "babu shakka ya kunshi ilmantarwa fadakarwa, nishadantarwa Rikici, yarda, amana, soyayya madararsa, ke kar na cika ki da surutu zaki gani abin da ke ciki" "ke mu je in sayi nawa" hhhhhhhhhhh "to ai Tabawa kin fini rudewa dubi fa yadda kika maida daurin zanin ki a hannun hagu" "ke dai bari Kawai banga laifinki ba na sako takalmi wari da wari ni dai mu je" "A'a wannan littafi ba sayansa zaki yi ba, wannan shahararriyar matashiyar marubuciya, ta saukakawa masoya karatun littafinta, Kawai ki Hau YouTube ki binciki shafinta mai suna Jidda Tv channel, ki danna kararrawa wato subscribe sannan ki danna like, Sai ki dauko sa cikin sauki ta hanyar sauti" "wayyo dadi kashe ni Kamar kin sani zuwa zan yi na yi abin da kika ce Kawai na dauko ina wanki ina saurara" "wallahi kuwa abu dan sauki, tsab zaki gama wanki baki san kin gama ba" "To Lami kamar na ji kin ce Episode ko sasi ko?" Hhhhhhhh "ke fa Tabawa matsala ta dake kanki baya ja da wuri, Episode na ce ma'ana tsari na daya, kin san zata dunga sakin littafin a ko wace mako ranar laraba Karfe 7:00am na safe" "ke na gudu zan je in sawo kati in Sai data kar a barni a baya" hhhhhhhhh Ku bi mu a dandalin mu Na YouTube mai suna Jidda TV channel Ranar laraba Ku yi mana subscribe da like.
  Not Attending
 • Muntasir Shehu I just published "BABI NA TAKWAS" of my story "FATIMA ZAHRA SA'EED". https://my.w.tt/SNa1Mp0qfbb
  Maybe Attending
 • nafisa lawal [11/29, 7😸9 PM] Anty Naphy: Nafisa lawal shuaibu Ga amsoshin tambayoyin wanan mako Q1 kurma Q2. Farko Annabi Adam Karshe yajuju da majuju mutuwa. Q3. Gimun da ra’un Q4. Itatuwa Q5 Q6a. Duste ne Q6b. Madina yake kusada kabarin sayyidina Hamza [Q7a. Bakiya wurine kusada masallacin manzo S.A.W 7b. Bakiya wurine wanda ake binne ahlul baiti a madina bakiya take. Q9 zul hulaifa Juhfah Yalamlam Qarnal manazil Zatul irqi Q8 sau daya ran Talata 10. Hajji ya kasu kashi ukku (3) 1. Ifradi 2. Tumattu’i 3. Qirani [11/29, 7:42 PM] Haupha: 👍🏻
  Attending
 • Dan Malam Koko Jama'a ku Sanya Yar uwa Hauwa'u Salisu ( Haupha ) Marubuciya a shafin Nan na Bakandamiya a Addu'ar ku Yau An samata Ledar Ruwa kwananta b2 ba lafiya, Sorry Sister Ubangiji Allah ya kara baki lafiya🙏 Sister Hauwa Ina Rokon Allah yakara Mana Lafiya, Da Zaman Lafiya A Qasarmu Nigeria Baki Da Ya🙏👏
  Attending