MARUBUTA » Hira da Baki » Filin Bakon Mako: Tattaunawa da Zaidu Ibrahim Barmo

Event Details

 • A cikin shirinsu na ‘Filin Bakon Mako’ na wannan satin, Maryam Haruna da Hauwa'u Muhammad, za su tattauna ne tare da wani hazikin marubuci, Zaidu Ibrahim Barmo, kuma CEO na Mujallar Zauren Marubuta.

  Ku biyo mu a cikin shirin ranar Talata 1st December 2020 da karfe 7 zuwa 10 na yamma in Allah Ya kaimu.

  Ku sauke manhajar Bakandamiya a Play Store ko App Store don bibiyar shirin.
 • Date
  12/1/20
  Time
  7:00 PM - 10:00 PM
 • Where
  Taskar Bakandamiya Map
 • Led by
 • Category
 • RSVPs
  • 12 attending
  • 2 maybe attending
  • 3 not attending
  • 0 awaiting reply

Mahalarta

This event has 17 guests.
 • Attending
 • Ummyter Abdallah Madam din Dana kewa aiki jiya ta aikeni na sayo mata semo 2kg,danaje shagon sai na tarar sai 1 kg,so na dawo ban sayo ba shine tace min ni Wawa ne bana amfani da hankalina na sayo 1kg guda biyu ya zama 2kg Kennan idan an hada,na bata hakuri dai ta hakura,yau kuma tace na sayo mata slippers number 8,danaje babu sai lamba 4 shine na sayo lamba 4 guda biyu,na kawo batace komai ba Naga tana hada mini kayana cikin jaka,shine nake tambaya ko wanki zatayimin koko daki zata canjamin🤪🤪🤪
  Attending
 • Maryam Haruna A rayuwata babu abin da nake so kamar kallon finafinai na tsoro da firgici hakan na min daɗi sosai wanda hakan yasa ko kallo zan yi bana kallon wanda na san babu wani abu da zai firgita mutane. Ko a makaranta abokan karatuna duk sun san wannan hali nawa,wani lokaci su kan bani shawara a kan in bari kada wani abu ya faru da ni amma da rana ɗaya ban taɓa sauraronsu ba tunanina ma yanda zan sa musu son fara kallon irin finafinan da nike yi ƙila hakan zai sa su fahimci abin da nake nufi da son waɗan nan abubuwan. Mu uku muke ɗakinmu na makaranta,kullum cikin hana ƴan ɗakinmu bacci da hayaniya in Ina kallo. Sun yi duk yanda zasu yi don hanani wannan ɗabi'ar amma hakan ya faskara,don bani da lokacin da nake jin daɗin kallon fim ɗin tsoro sai sha biyu na dare. Ashe ƙaddara ce ke bibiyata ban sani ba. Wata rana daga makaranta aka kai mu asibitin mahaukata wacce ke bayan gari kusa da maƙabarta. Na ji daɗi sosai don wasu finafinai da nike kallo yawanci a asibitin mahaukata ake bada tsoro duk tunanina tunda mun zo hakan zata faru ga waɗan da muka zo tare don ni bana saka kaina saboda ni na san na saba kallo to tsoron mi zan ji kuma. Ranar da ba zan manta da ita ba ita ce: bayan satinmu guda a asibitin ranar ina aikin dare sai na dinga jin kamar ana kuka sannan ana jan wani abu kamar ƙarfe cikin wani ɗaki da ke kusa da inda nake zaune. Wata mata ce ciki wacce tun da muka zo asibitin magani ko abinci kawai ke sa a buɗe ɗakin saboda yanda take duk wanda ya shiga ɗakin ƙoƙarin kashe shi take yi hakan yasa aka daina zuwa wajenta sai dole. Da farko na share saboda na san matar da ke ciki zata iya yin komai duba da yanda ciwonta yake amma kuma sai na ji abubuwan sai ƙaruwa suke yi,wata zuciya na cewa na duba wani gefen na gargaɗina a kan kada na je. Da dai na ji abin ya wuce tunanina ƙarar sai damuwata take yi hakan yasa kawai na tashi don zuwa ganin menene. Ina tashi sai wutar ɗakin ta dinga rawa kamar zata ɗauke. Ban damu ba na kunna fitilar wayata don in gani da kyau. Tura ƙofar ɗakin na faɗa ba tare da jiran wani abu ba,abin da na gani ne ya kusan sani sumewa. Wata halitta ce kusa da matar nan tana mata wani abu da na kasa gane meye matar dai kwance take kamar babu rai tare da ita wannan halittar sai zuƙar jinin jikinta dake ta malala ƙasa kamar ruwa . Hakan da na gani ya mugun tsoratani har ban san na saki wayata ba ashe dai duk rashin ganin tsoron da nake cewa bana shaci daɗi ne don ban gani a zahiri bane, ƙarar faɗuwar wayar yasa wannan halittar ta juyo inda nake cikin sakan ɗin da bai wuce goma ba na ƙare mata kallo. Ƙaton kai ne da ita kamar ƙwllo,wuya kuma ba kauri sai kace mariƙar lema. Ido guda gareta kuma a tsakiyar kai yake, ƙafafuwanta sun kusan shida ga wani gashi da ya rufe mata jiki wanda ya ƙara maidata abin tsoro. Ganin ta juyo inda nake yasa da sauri na zabura da gudu zan bar ɗakin ai kafin ƙyaftawar ido na ga ta kusa zuwa inda nake ban yi ƙasa a guiwa ba na ƙara azama wajen gudun da nake son yi. Ita ma kokarinta ta zo inda nake don lahanta rayuwata na yi gudu sosai kaɗan ya rage in buɗe ƙofar fita baƙi ɗaya sai kawai na ga kare bakin ƙofar gashi ya buɗe baki da alama jira yake na ƙaraso wajen shima ya illatani. Ganin haka na yi shahada tare da canja waje zuwa makewayin dake ɗakin sai dai me kafin in kai na hango wani mutum mai mugun tsawon da duk iya ganina na kasa ganin ƙarshensa,gashi kayan jikinsa baƙi wuluƙ da dai na rasa yanda zan yi kawai sai na rufe idona ina jiran mai faruwa ta faru. Ban san me ya faru ba sai dai na buɗe ido na ganeni kwance saman gado an ɗaureni da igiyoyi a yanda na ji ana magana wai sati na guda kenan da haukacewa kuma duka nake yi don haka aka ɗaureni yanzu haka mafita nake nema yanda zan faɗa musu cewar ba hauka nake ba.
  Attending
 • lawal usman SLM barkanmu da ranar juma'a mai albarka Allah yakarbi ibadunmu kuma yasaukaka mana kuncin rayuwa
  Not Attending
 • Sadik *_SAKON TA'AZIYYA DAGA PEN WRITERS ASSOCIATION._* *_Assalama alaikum warahamatullahi wabarakatuh._* *INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN!!!* _A madadin daukacin mambobin kungiyar marubuta ta *PEN WRITERS*, ina amfani da wannan dama wajen mika sakon gaisuwar ta'aziyya ga 'yar uwarmu Asma'u Abdullahi *(Ummyter Bingyel)* wacce ta yi rashin mahaifinta. Babu shakka wannan babban rashi ne da ba za'a taba mantawa ba, muna taya ki alhini._ _Muna addu'ar Allah Ubangiji ya jaddada rahama a kabarinsa, Allah ya yafe masa dukkan kura-kuransa. Allah ya kyautata makwancinsa ya sa Aljannar Fiddausi ce makomarsa da mu baki daya._ _Bayansa da ya bari muna rokon Allah ya ba su hakuri da juriya bisa wannan rashin da suka yi. Allah ya yi musu albarka Allah ya kara inganta rayuwarsu._ _Wasaalam alaikum!_ ```Signed:``` *_Pen Writers_*
  Attending
 • Jibrin Adamu Rano ZOBENA 02 ©Jibrin Adamu Rano Bayan ta sa ƙaninta ya ɗakko mana tabarma ta shimfina mana a rumfar ƙofar gidan su mun zauna ne na fara bata labarin BABI NA FARKO    "A wata makaranta ce ta 'ya'yan masu yatsu da yawa al'amarin ya faru, yau kimanin shekaru shida zuwa bakwai da bamu labarin..."    "Su waye kuma masu yatsu da yawa?" Nafisa ta tari numfashina.    "Masu hannu da shuni mana." Na yi maganar cikin yanayi na murmushi da mamakin yadda aka yi ta kasa ganewa. Abin da ya ƙara bani mamaki shi ne shima hannu mai shunin bata san me ake nufi da shi ba, don haka ne na yi mata ta yaren gwari.    "Masu kuɗi nake nufi to." Na ɗan tsahirta kana na ci gaba.    "Makaranta ce sakandire ta mata zalla, makaranta ce ta jeki ki dawo. Amma fa kamar yadda na faɗa miki duk yarinyar da kika gani a cikin wannan makarantar ko dai 'yar mai kuɗi ce ko kuma wani ne ya tsaya mata.    To a ajin manyan ɗalibai na makarantar ne wasu ɗalibai su biyu Salima da Rufaida suna zaune suna rubutu kamar da wasa Rufaida ta ƙyalla ido a kan yatsan Salima wanda ta hangi wani zobe na gwal mai matukar ƙyalli a jiki. Cikin wani yanayi na murna, ɗoki da kuma zumuɗin ganin zoben ta fara yiwa ƙawar tata magana.    " 'Yar rainin wayo! Dama ke kika ɗaukar min zobena kina ji ina ta cikiya kika yimin kunnen uwar shegu? To asirin ki ya tonu na gan shi sai ki bani abuna." Ta yi maganar ne cikin dariya, don haka Salima ta yi tunanin cewa zoben ne ya burgeta shi ya sa take tsokanarta. Kawai sai itama ta yi dariya bacin ta fakaici idon malamin da yake yi musu darasi a wannan lokacin kar ya hangosu suna surutu, ta yi magana cikin raɗa-raɗa.    "Kema zoben ya yi miki kyau kenan?" Bata jira ta amsa ba ta ci gaba.    "Wallahi Muttaƙa ne ya bani shi jiya da daddare da ya zo gidanmu zance, kowa dai yana yabawa da zoben." Jin haka ne ya sa Rufaida haɗe rai, tunaninta ta yaya Salima za ta raina mata hankali, ta sace mata zoben da saurayinta Kamal ya bata tana cewa itama wai saurayinta Muttaƙa ne ya bata. Don haka rai a ɓace ta sake jaddada ƙudirinta cewa lallai nata ne.    "Don Allah ba na son wasa ki bani zobena tunda dai na riga na gan shi. Wallahi zoben nan da kike gani tun daga Indiya Kamal ya kawo min, shi ya sa kika ga na damu sosai da ɓatan shi saboda nasan halin Kamal cewa zai yi ban damu da shi ba ne shi ya sa har na yi sakaci da zoben shi ya ɓata." Ta ƙarasa maganar ta na mai miƙa hannunta kan yatsan na Salima da niyyar ta cire zobenta kamar yadda zuciyarta take raya mata ta yi.      "Mtwsss..!" Salima ta ja tsaki ganin yadda Rufaida ta wani daƙumi zoben zata fusge mata shi.    " Bana son iskanci. Don Allah sakar min zobena ni kar ki sa ya yi datti, don Wallahi ina ji da Zoben nan kamar yadda nake ji da Muttaƙana, shi kuwa Muttaƙana ina ji da shi kamar yadda na ke ji da raina. Kinga kuwa bai kamata ki yi min irin wannan wasan ba don gudun kar a samu matsala." Ta ƙarasa da dariya dai dai lokacin da ta fusge hannunta daga cikin na ƙawar tata tana mai bin zoben da kallo tare da yabawa da yadda yake ta faman wani sheƙi da walwali.    Rufaida fuska a ɗaure ta ce    "Wasa!" Ta maimaita kalmar ne tana kallonta da alamun mamaki.    "Ban gane me kike nufi da wasa ba? Ko an faɗa miki yadda ba kya wasa da abin da ya shafi Muttaƙa nima ina yin wasa da duk abin da ya shafi Kamal ne? Don Allah ni ki cire min zobena ki bani bana son iskanci da wulaƙanci." Ta ƙare tana turɓune fuska, a wannan karon yanayinta ya fi koyaushe nuna cewa lallai da gaske take furucin zoben nata ne.    Abin na ƙawayen biyu kamar da wasa haka ya fara, kafin daga bisani da kowaccen su ta fahimci ashe fa da gaske ƙawar tata take yi. Ita Rufaida kallon ɓarauniya take yiwa Salima wacce ta sace mata zobenta da ta daɗe tana nema, zobenta da ɓatan shi har bacci ya hanata yi. Yayin da ita kuma Salima take kallo Rufaida a matsayin wata hamshaƙiyar 'yar rainin hankali wacce tana ji tana gani Muttaƙanta ya bata zobe amma zata dinga da'awar wai nata ne har tana daƙumar mata shi. Wannan shi ne abin da ya sa rigima ta kacamewa ƙawayen biyu a cikin ajin ta yadda dole sai da Malamin ya fahimta, rigimar da ta yi ƙarfin da ta fi ƙarfin malamin har ta je gaban shugabar makarantar Hajiya Rukuba Maryama (Kamar yadda take amfani da sunan). Hajiya Maryam cikin takaici da ɓacin rai take tambayarsu abin da ya haɗa su har suke faɗa a gaban malam, sanadin da ya sa malamin mai amsa suna malam Nasir ya ɗakko zoben kenan yake nunawa shugabar makarantar akan abin da suke faɗan. Hajiya Maryama ta karɓi kyakkyawan zoben da ya burgeta bisa ganin yadda yake ta faman wani sheƙi da walwali tana jujjuya shi a hannunta cikin ƙare masa kallo da tunanin lallai zoben kam ya cancanta a yi rigima a kan shi saboda kyan tsarin shi da alamar da ke nuna tsadar shi. Aikuwa kafin ta bud'i baki ta yi magana yarinyarta budurwa sa'ar matasan 'yan-matan biyu Salima da Rufaida mai amsa suna Hajara da take zaune a kan kujerar gaban teburinta ta yi farat ta miƙe tsaye tare da bararo idanuwanta waje cikin ƙarewa zoben kallo tare da alamun da ke nuna mamakinta ƙarara ta ce. "Wallahi Umma zobena ne ba nasu ba ne! Wallahi Umma zobena ne wanda nake ta faɗa miki cewa ya ɓata ɗinnan tun kwanaki." Ta furta hakan jikinta har wani rawa-rawa yake yi tana ƙoƙarin fusge zoben a hannun mahaifiyarta. Ba mahaifiyar tata da ta bita da kallo ba, hatta aminan biyu Salima da Rufaida da kuma shi kansa malam Nasir da kallo kawai suka bita kowa zuciyar shi a cunkushe da mamakin yadda daga ganin sarkin fawa zaisa har miyarta ta yi zaƙi haka, daga ganin zobe kawai sai ta ce zobenta ne?"
  Attending
 • Jidda Washa Shahararriyar matashiyar marubuciya, mai suna Adam Hauwa'u Suleiman wacce duniyar Marubuta ta san ta da Jidda washa. Ta zage ta zazzago wani sabon littafi mai suna MUMTAZ. Littafi da ya kunshi soyayya madararsa, tausayi, Amana, Rudani, Rikici, da dai sauransu. Ga Masu son wannan Littafi da zai dunga zuwa muku a saukake Wanda ba sai mun wahalar da Masu karantawa ba, don haka muka fitar da hanya saukakka. Ta hanyar Sauti a cikin Shafin mu Na YouTube channel mai suna JIDDA TV Channel. Kuna shiga Shafin ku danna alamar kararrawa wato ku yi mana subscribe gami da Like. Muna alfahari da ku masoyan mu. TALLA "A Lami! Ina zuwa haka cikin wannan rana mai kuna da zafi na ganki ga ba daya a birkice, dubi takalmin ki wari da wari ko dai ba lafiya ne?" "Uhmm Tabawa kenan ki bar ni garau nake, shahararriyar matashiyar marubuciya wacce aka fi sani da Jidda washa, ce ta saki sabon littafinta Wanda nake ba ki labari" "To fa! Wannan wani littafi ne haka da ya sa kika rude kamar Wanda a ka biya wa kujerar Hajji da umara?" "Tabawa ba dole na rude ba kin san iya tsahon lokutan da na kai ina dakon wannan littafin?" "Lami ta ya ya zan sani" Hhhhhhhh lallai fa "to ai na dade ina jiran in ga fitowar wannan littafi, Sai ga shi rana tsaka ta fitar da shi " "to fa ni fa har yanzu kin sa ni a duhu wai mai sunan littafin kuma wani darasi yake dauke da shi?" "Yanzu ko zan fayyace miki sunan littafin da darasin da yake dauke da shi, wannan littafi mai suna MUMTAZ" "keeeee yanzu wannan littafin ne ya fito?" "Kwarai kuwa" " to ai Lami ki ce faduwa ce ta zo daidai da zama ni kai na dakon fitowar littafin nake, yadda kika san kin min albushir da Auren Gwamna" hhhhhhhh "lallai kina budurin ki" "ai ina ga yanzu binki zan yi cikin azama nima in sayi littafin tunda naga akwai darasuka a ciki" "babu shakka ya kunshi ilmantarwa fadakarwa, nishadantarwa Rikici, yarda, amana, soyayya madararsa, ke kar na cika ki da surutu zaki gani abin da ke ciki" "ke mu je in sayi nawa" hhhhhhhhhhh "to ai Tabawa kin fini rudewa dubi fa yadda kika maida daurin zanin ki a hannun hagu" "ke dai bari Kawai banga laifinki ba na sako takalmi wari da wari ni dai mu je" "A'a wannan littafi ba sayansa zaki yi ba, wannan shahararriyar matashiyar marubuciya, ta saukakawa masoya karatun littafinta, Kawai ki Hau YouTube ki binciki shafinta mai suna Jidda Tv channel, ki danna kararrawa wato subscribe sannan ki danna like, Sai ki dauko sa cikin sauki ta hanyar sauti" "wayyo dadi kashe ni Kamar kin sani zuwa zan yi na yi abin da kika ce Kawai na dauko ina wanki ina saurara" "wallahi kuwa abu dan sauki, tsab zaki gama wanki baki san kin gama ba" "To Lami kamar na ji kin ce Episode ko sasi ko?" Hhhhhhhh "ke fa Tabawa matsala ta dake kanki baya ja da wuri, Episode na ce ma'ana tsari na daya, kin san zata dunga sakin littafin a ko wace mako ranar laraba Karfe 7:00am na safe" "ke na gudu zan je in sawo kati in Sai data kar a barni a baya" hhhhhhhhh Ku bi mu a dandalin mu Na YouTube mai suna Jidda TV channel Ranar laraba Ku yi mana subscribe da like.
  Not Attending
 • Fadima He who loves the world injuries his hereafter
  Maybe Attending
 • Rabee'atou A Oumar (Pinky) 🌖 *BAMBANCIN HALITTA* 🌖 ©️℘ıŋƙყ wattpad😛inkylady222 Email😲umarrabiatu@gmail.com 02 *Kyanko* *2001* ƙaton fili ne da ya ke cike maƙil da jama'a, a na ta hayaniya a na maida yadda akai. tsawon lokaci kafin wasu murguza murguzan mutane da babu komai a jikinsu sai 'dan fantare da su ke a k'ugunsu, su ka buɗe ƙatuwar muryar da Allah yai masu su ka fara kwarara ihu da ke shaidawa jama'ar wurin Ambarama ta iso. A take kowanne yaja bakinshi ya rufe suka sunkuya cike da girmamawa har ta ƙaraso ta zauna a kujerar da ta ke ta ƙaton dutse ce aka lanƙwasa sannan akai mata ado. Wurin ya ɗau wani kalar shirun da ko allurar ka ta faɗi zaka iya jin sautin faɗuwarta. Bayan yan daƙiƙu da zaman ta waɗannan margaza-margazan mutanen su ka iso filin jaye da wani tsoho da ke ɗaure da kaca ya na tafiya daƙyar jikin shi duk ya farfashe. A ka Duƙar dashi gaban Ambarama ya sadda kanshi ƙasa Ɗaya da ga cikin mutanen Ambarama ya fara jawabi. "Kamar yadda kuwa ya sani game da zunibin da Ayuroro ya aikata a nahiyar nan da sauran nahiyoyi maƙwabtanmu, wanda sanadiyyar hakan ta jawo ɓarna da sanadiyyar rayuka aruaru ta kuma jaza tarzomar da ba a daɗe da kwantar da ita ba." "..a yanzu bayan shekaru ukku kamar yadda shari'a da doka ta tsara tare kuma da taimakon sarauniya mai girma Abin kwatance Ambarama ta tanada, hukun cin Ayuroro na farko zai hau kan shi." "Lafiya, tsayon rai Ambarw" "lafiya mai girma Ambara" jama'ar wurin ke faɗi cikin amanna da duk wani hukuncin ta. Mutanen ta suka ɗaga hannu akai shiru. Ɗaya da ga jikin su ya taho da wani ƙoƙo ya aje gaban ayuroro. "Dakata!" Ambarama ta faɗi akaron farko ta na kallon Ayuroro da ke niyyar ɗaukar ƙoƙon. Ya tsaya jikin shi na ɓari hawayen shi duk sun bushe. A yanzu bai da sauran hawayen da zasu kuma zubowa kuma, ya riga da yasan abin da zai faru a ƙarshe kenan. Ahalin shi sun zama cutuwa a gareshi, sun jefashi cikin bala'en da bai isa ya fidda kan shi ba. "Ka koma a salin halittarta kafin ɗaukar hukunci." Maganar ta ta katse tunanin shi. Ta na rufe baki ya haɗe hannuwanshi wuri ɗaya tare da girgiza sai ga ƙaton maciji sharɓeɓe ya bayyana. An riga an gama duk wani bayanin da za ai, kowa yasan hukuncin abin da ya aikata. Ya sulala ya kafa kanshi a ƙoƙon ya ruza halshenshi ya surɓe abin da ke ciki. Dandanan ya fara yamutsewa ya na komawa ɗan ƙarami kamar sabon macijin da aka haifa. A cikin jinga jingan nan wasu suka taho da wani abu mai saƙa-saƙa mai shara-sharar da ana hangen abin da ke ciki tamkar gilas, suka aje gaban macijin sannan suka ɗauke shi su ka saka a ciki suka maida marfin suka rufe. Ambarama ta kalli abun wani abu kamar walƙiya ya fito da ga bakin ta ya bugi abun ƙara ta karaɗe wurin har ana toshe kunnuwa. Daga nan sai ta bada umar nin a ɗauke abun ta tashi. Kowa ya watse, wasu fuskarsu da alhini. ***** ****** ***** Ambara na komawa gida ta shige ɗakin ta tare da sallamar masu hidimta mata ta buga ƙara, ihu da kukan baƙin ciki. Ta saka ranta da bayyanar duk gaskiyar da ta ke son sani ga lamarin nan ko dan ta san yadda zata bullowa lamarin ta haɗa iyalanta. A matsayinta na shugaba a yanzu amma ace ba ta da kowa nata bata da jinin da zata kalla ta ji daɗi. Kuka ta ke mai cin rai, kukan kaɗaici. Ta ɗauki lokaci mai tsawo ta na wannan kukan kafin ta gaji ta bari sannan ta bada dokar ba zata ga kowa ba har tsawon kwana bakwai. *Mafarin komai* *1999* Zaune ta ke bisa ƙaton dutse ta zura ƙafafuwanta cikin makeken ruwan da ke wucewa, ta kuma zuba mashi idanuwa a zahiri. A kai-akai ta ke jefa ƙananun duwatsun da ke dumtse a hannunta cikin ruwan. Kusan Sati biyu kenan amma ta kasa mantawa da maganar mahaifiyarta 'maima' _idon ki ya rufe da ganin gaskiyar kalamaina 'Farfar', kin makance da soyayyar da ba zata amfane ki ba._ _ya zama dole kuma ki goyi bayana na mulki *kyanko!*_ ta saka hannu ta gyara gashin kanta da iska ke kaɗowa a fuskarta. Ta sunkuya ta sake dumtso duwatsun saboda ƙarewar da na hannunta sukai. Tunani ta ke son yi, mafita ta ke so. Amma ta yaya? wanda ya ke bata dukkan mafita a yawan lokutta,yanzu matsalar da ga nan ta fito. Jikinta ya bata kallonta ake, dutsen da ta ware za ta jefa ta fasa. "Idan ka ci gaba da tsayuwa a nan, kwarjininka zai iya saka tunani na gushewa" ya tako a hankali cikin tafiyarshi ta cikakkun maza masu jini a jika. Ya saka hannunshi ya tattare gashinta ya maida shi gefen wuyanta. Sannan ya leƙo da kan shi ta ɗayan ɓarin har ta na shakar numfashin shi ya ce "A mabiya kyanko ne kawai challa ke da kwarjini. A wurin ki kuma tamkar jaririn da ki ka haifa ne" ta lumshe idanuwanta ta buɗesu a hankali. Sannan ta kamo hannunshi ya zagayo ya zauna gefen ta. "Sai ki ka zo ke ɗaya, ki ka baro ni ko. mai ya sa?" Ya faɗi sa'ilin da ya sauke jikkar da ke rataye a wuyanshi. "Ha ka kawai yau na riga ka zuwa kafin cikar lokaci" "To shikenan in dai ba laifi na yi ba da sauƙi" ya ɗebo duwatsun ya fara jefawa. Ta kalli yawan ruwan yadda suke tafiya har ba a iya ganin ƙarshe su. Ta ce "Challa" "uhm?" ya amsa ya na kallonta. "Ni ina son na tsallake ruwan nan ina son shiga.." Sai ta ɗan yi shiru ta na tunani "Ya sunan nahiyar?" "Mwagbo" ya bata amsa ya na murmushi. "Yauwa mwagbo.. ina son ganin yadda su ke rayuwarsu. Wai ba irin ta mu ba? addininsu daban?" ya gyaɗa mata kai. "ina son shiga" "kar ki damu babu in da ba zaki zagaya ba ma idan lokaci ya yi _Boidi_ (princess)" Sai ta yi murmushi ta ce "wa ne kalar addini suke?" "kayya dai! Ba ni da ikon gaya maki akan hakan Boidi a yanzu" Ta tsuke fuskarta ta mik'e ta na had'e rai, maganar maima na dawo mata. ' _ke fa ba za ki ta b'a samun cikakken 'yancin da za ki ziyarci dukkan inda kike so ba Matuk'ar mulkin kyanko ba naki ba ne_ ' Ta cije leb'en ta na k'asa ta na jin haushin challa, mo ba komai ai an riga an masu baiko, zuwa yanzu ya ka mata ace tasan duk wani abu da ta ke son sani gane da ko wace nahiya. Ya ruk'o hannunta. Ta juya mashi ba ya ta na k'in kallin shi. "haba Boidin challa, bai kyautu mu samu sab'ani a kan abin da kin riga kin sani ba. Babu wanda ya ke da damar tsallake nahiyarmu ko jin halin da wata nahiya ta ke ciki nusamman mwagbo, sai jinin mulkin kyanko. Ke kuma duka mai ya rage? Da ga munyi aurenmu kin haihu shikenan fa zaki san koma miye. Ki bar damuwar nan kin ji?" Ta gyad'a kai. "yauwa yimun murmushin nan in gani" Ta murmusa ba dan ta so ba. Ta na son challa sosai a gefe d'aya kuma ta fara kwad'ayin abin da mahaifiyarta ke kwad'aita mata gaje kyanko gaba d'aya. Ya jawo jikkar da ya zo da ita ya d'akko k'aton ganyen da ya nad'o gasasshen nama a ciki. K'amshin naman ya bugi hancinta, yawunta ya tsinke ya zarce mak'ogoron ta. Idan akwai abin da ta fi so gasasshen nama ne. Kasancewar a gaba d'aya nayihar babu mai ikon cin naman da aka dafa sai masu mulkin nahiyar, duk kuwa da naman shine abincin su kawai a ko yaushe, hakan kuma bai dame su ba tun da haka tsarin yake haka kowa ya tashi ya ga a nayi. Idan kana da wani had'i da su ko wani a ciki ya baka za ka iya ci amman kai ba ka da damar gasa nama. "mu ci abincin nan kar yai sanyi" Ta matsa kusa da shi ta zauna su ka fara Cin abincin, su na yi yana mata fira har suka gama. Sai da duhu ya fara sannan su ka bar wurin har gida ya raka ta inda ko ina zagaye ya ke da duwatse da su ake zagaye ko ina afidda gida je a cijin gidan ma dasu ake fidda d'akuna. A gaba gudansu sun dad'e suna fira kafin yai nata sallama ya tafi. "ni dai ban ga amfanin soyayyar nan ba farfar" Tai dariya ta zauna kusa da ita. "mama kenan, kin san challa ya na so na sosai Ni ma kuma ina son shi. Bayan nan ana darajamu da girmama mu mama gashi zan shiga gidan shugaba amatsayin suruka, challa zai zama shugaba.." "ke ni rufe mani baki" Ta katse ta. "kibar ganin kamar zaki samu duk ikon da kike tunani. Eh zaki samu sosai amma ba komai ba, idan ki na ganin abin da na ke gaya maki k'arya ne ki jira ki auri challan. Ina nai rantse maki da mahaifinki sai kin yi nadamar k'in bani had'in kai da ki kai" Farfar tai shiru ta na juya maganar mahaifiyarta a ranta. Ita ma maima ba ta ce mata komai ba ta barta tai tunanin da zai fisshesu su duka. Tunanin yai mata yawa ta kasa karkata ga b'angare d'aya sai kawai ta tashi ta shige d'akin da babanta ke had'a magungunan shi. Ya na zaune ya juya baya ya na duba wasu shafukan takardu rubutun ciki mai haske. Ya na dubawa ya na had'a magungunan shi. Tsaye ta yi har ya gama ya rufe maganin acikin k'atuwar kwalba sannan ya juyo ya fuskance ta. "a rayuwa ba komai kake so kake samu ba duk kuwa ga yadda ka so abunnan. Hakuri da yadda tsarin rayuwa ya zo maka shi zai sa ka tayu cikin farinciki da kwanciyar hankali" Ta sadda kanta k'asa ta na murmushi Ta ce "to baba, nagode k'warai" Ya jinjina kai, sanna ya ciga ba da yi mata nasiha mai hannun ka mai sanda ga me da k'udirin da mahaifiyarta ta saka a gaba Wanda ba ya jin hakan mai bulle masu ne su dukan su. **** ***** Challa na tsaye farfar ta shige gida sannan ya juya ga fadarsu. Duk inda ya wuce sai an sunkuya cike da girmamawa har ya isa. Kai tsaye ya shiga falon mahaifiyarshi, idan ta na da uzuri yasan ba zai sameta a falon ba ta na can cikin ƙuryar ɗakin ta. A yanzun ma bai ganta ba sai ya samu wuri ya zauna kafin ta ji alamun zuwanshi ta fito. Ta na zaune ta lanƙwashe ƙafafuwa hannuwanta biyu duk a saman cinyoyin ta ta jirkitasu ta sama, kan ta a duƙu. Gefe da gefenta hayaƙi na tashi a hankali ya na karaɗe ɗakin. Kusan awwnni biyu kenan da zamanta wurin. Ta buɗe idanunta a hankali da sukai kore shar ta ɗaura a kan mijinta da ke ɗan nesa kaɗan da ita, na wani lokaci kafin ta ƙara rufe idon. "Da kyau Amba!" ya faɗi da murmushi kwance a fuskarshi. Ita ma ta mai da mashi martanin murmushi sannan ta miƙe. "Ɗana ya zo ya na jira na" ya gyaɗa mata kai ta fice da ga ɗakin. Inda ta adana mashi abincin shi ta nufa ta fara ɗakko mashi ta aje a gaban shi sannan ita ma ta zauna. Ya taso ta shafa kanshi sanna ya koma ya zauna. Ta buɗe gasashshen nama da kayan marmari ta tura a gabanshi. Duk da ta san ya ci abinci, asalima ita ke haɗa mashi abincin ya tafi da shi duk idan zai tafi bakin ruwa, hakan ba zai hana ya na dawowa ta umarce shi da cin wani ba. A kwai soyayya sosai a tsakanin ɗa da uwar. ****** ********
  Attending
 • nafisa lawal [11/29, 7😸9 PM] Anty Naphy: Nafisa lawal shuaibu Ga amsoshin tambayoyin wanan mako Q1 kurma Q2. Farko Annabi Adam Karshe yajuju da majuju mutuwa. Q3. Gimun da ra’un Q4. Itatuwa Q5 Q6a. Duste ne Q6b. Madina yake kusada kabarin sayyidina Hamza [Q7a. Bakiya wurine kusada masallacin manzo S.A.W 7b. Bakiya wurine wanda ake binne ahlul baiti a madina bakiya take. Q9 zul hulaifa Juhfah Yalamlam Qarnal manazil Zatul irqi Q8 sau daya ran Talata 10. Hajji ya kasu kashi ukku (3) 1. Ifradi 2. Tumattu’i 3. Qirani [11/29, 7:42 PM] Haupha: 👍🏻
  Attending
 • Maybe Attending
 • Bibah Musa💗💅 رب حبلي من لدك زرية طيبة إنك سميع الدعاء 🙏🙏
  Attending