A wannan satin ma, Maryam Haruna da Hauwa'u Muhammad, cikin shirinsu na 'Filin Bakonmu Na Mako,' za su tattauna ne tare da wani hazikin marubuci, Muntasir Shehu.
Ku biyo mu a cikin shirin ranar Talata 19 January 2021 da karfe 7 zuwa 10 na yamma.
Rahmatu Lawan
GORON JUMMA’A
MANUFOFIN DA SUKA SA AKA HARAMTA ZINA
Tambaya:
Assalamu alaikum malam Ina son karin bayani game da manufofin sharia akan haramta zina.
Amsa:
Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya zo don ya kare tsatson Dan'adam da mutuncinsa, don haka ya shar'anta aure kuma ya haramta zina, ga wasu daga cikin hikimomin da haramta zina ya kunsa :
1. Katange mutane daga keta alfarmar shari'a.
2. Samar da Dan'adam ta hanya mai kyau, ta yadda za'a samu wanda zai kula da shi, saboda duk wanda aka same shi ta hanyar zina, to ba za'a samu wanda zai kula da shi ba yadda ya kamata.
3. Saboda kada nasabar mutane ta cakudu da juna.
4. Katange mace daga cutarwa, ita da danginta, saboda zina tana keta alfarmar mace, ta zamar da ita ba ta da daraja.
5. Kare mutane daga cututtuka, kamar yadda hakan yake a bayyane.
6. Toshe hanyar faruwar manyan laifuka, miji zai iya kashe matarsa, idan ya ga tana zina, kamar yadda mace za ta iya kashe kwartuwar mijinta, daga nan sai a samu daukar fansa, sai fitintinu, su yawaita.
7. Zina tana kawo gaba da kiyayya a tsakanin mutane.
8. Kare mutuncin yaron da za'a Haifa, domin duk yaron da aka Haifa ta wannan hanyar zai rayu cikin kunci.
WANNAN YA SA BABU WANI ZUNUBI BAYAN SHIRKA DA YA FI ZINA.
Allah ne mafi sani
Amsawa✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
21/4/2013
Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Awaiting Reply
Lawan Dalha
Ya Allah Ka sada mu da alkhairan da ke cikin wannan rana; ka tsare mu daga sharri duniya da lahira. #JummaaMubarak
Ummyter Abdallah
(owner)
Madam din Dana kewa aiki jiya ta aikeni na sayo mata semo 2kg,danaje shagon sai na tarar sai 1 kg,so na dawo ban sayo ba shine tace min ni Wawa ne bana amfani da hankalina na sayo 1kg guda biyu ya zama 2kg Kennan idan an hada,na bata hakuri dai ta hakura,yau kuma tace na sayo mata slippers number 8,danaje babu sai lamba 4 shine na sayo lamba 4 guda biyu,na kawo batace komai ba Naga tana hada mini kayana cikin jaka,shine nake tambaya ko wanki zatayimin koko daki zata canjamin🤪🤪🤪
Attending
Maryam Haruna
A rayuwata babu abin da nake so kamar kallon finafinai na tsoro da firgici hakan na min daɗi sosai wanda hakan yasa ko kallo zan yi bana kallon wanda na san babu wani abu da zai firgita mutane. Ko a makaranta abokan karatuna duk sun san wannan hali nawa,wani lokaci su kan bani shawara a kan in bari kada wani abu ya faru da ni amma da rana ɗaya ban taɓa sauraronsu ba tunanina ma yanda zan sa musu son fara kallon irin finafinan da nike yi ƙila hakan zai sa su fahimci abin da nake nufi da son waɗan nan abubuwan. Mu uku muke ɗakinmu na makaranta,kullum cikin hana ƴan ɗakinmu bacci da hayaniya in Ina kallo. Sun yi duk yanda zasu yi don hanani wannan ɗabi'ar amma hakan ya faskara,don bani da lokacin da nake jin daɗin kallon fim ɗin tsoro sai sha biyu na dare.
Ashe ƙaddara ce ke bibiyata ban sani ba. Wata rana daga makaranta aka kai mu asibitin mahaukata wacce ke bayan gari kusa da maƙabarta.
Na ji daɗi sosai don wasu finafinai da nike kallo yawanci a asibitin mahaukata ake bada tsoro duk tunanina tunda mun zo hakan zata faru ga waɗan da muka zo tare don ni bana saka kaina saboda ni na san na saba kallo to tsoron mi zan ji kuma.
Ranar da ba zan manta da ita ba ita ce: bayan satinmu guda a asibitin ranar ina aikin dare sai na dinga jin kamar ana kuka sannan ana jan wani abu kamar ƙarfe cikin wani ɗaki da ke kusa da inda nake zaune. Wata mata ce ciki wacce tun da muka zo asibitin magani ko abinci kawai ke sa a buɗe ɗakin saboda yanda take duk wanda ya shiga ɗakin ƙoƙarin kashe shi take yi hakan yasa aka daina zuwa wajenta sai dole. Da farko na share saboda na san matar da ke ciki zata iya yin komai duba da yanda ciwonta yake amma kuma sai na ji abubuwan sai ƙaruwa suke yi,wata zuciya na cewa na duba wani gefen na gargaɗina a kan kada na je. Da dai na ji abin ya wuce tunanina ƙarar sai damuwata take yi hakan yasa kawai na tashi don zuwa ganin menene.
Ina tashi sai wutar ɗakin ta dinga rawa kamar zata ɗauke. Ban damu ba na kunna fitilar wayata don in gani da kyau. Tura ƙofar ɗakin na faɗa ba tare da jiran wani abu ba,abin da na gani ne ya kusan sani sumewa. Wata halitta ce kusa da matar nan tana mata wani abu da na kasa gane meye matar dai kwance take kamar babu rai tare da ita wannan halittar sai zuƙar jinin jikinta dake ta malala ƙasa kamar ruwa .
Hakan da na gani ya mugun tsoratani har ban san na saki wayata ba ashe dai duk rashin ganin tsoron da nake cewa bana shaci daɗi ne don ban gani a zahiri bane, ƙarar faɗuwar wayar yasa wannan halittar ta juyo inda nake cikin sakan ɗin da bai wuce goma ba na ƙare mata kallo. Ƙaton kai ne da ita kamar ƙwllo,wuya kuma ba kauri sai kace mariƙar lema. Ido guda gareta kuma a tsakiyar kai yake, ƙafafuwanta sun kusan shida ga wani gashi da ya rufe mata jiki wanda ya ƙara maidata abin tsoro.
Ganin ta juyo inda nake yasa da sauri na zabura da gudu zan bar ɗakin ai kafin ƙyaftawar ido na ga ta kusa zuwa inda nake ban yi ƙasa a guiwa ba na ƙara azama wajen gudun da nake son yi. Ita ma kokarinta ta zo inda nake don lahanta rayuwata na yi gudu sosai kaɗan ya rage in buɗe ƙofar fita baƙi ɗaya sai kawai na ga kare bakin ƙofar gashi ya buɗe baki da alama jira yake na ƙaraso wajen shima ya illatani. Ganin haka na yi shahada tare da canja waje zuwa makewayin dake ɗakin sai dai me kafin in kai na hango wani mutum mai mugun tsawon da duk iya ganina na kasa ganin ƙarshensa,gashi kayan jikinsa baƙi wuluƙ da dai na rasa yanda zan yi kawai sai na rufe idona ina jiran mai faruwa ta faru. Ban san me ya faru ba sai dai na buɗe ido na ganeni kwance saman gado an ɗaureni da igiyoyi a yanda na ji ana magana wai sati na guda kenan da haukacewa kuma duka nake yi don haka aka ɗaureni yanzu haka mafita nake nema yanda zan faɗa musu cewar ba hauka nake ba.