Jiddah Washah
Ma sha Allah, hakika na ji daɗin wannan tattaunawar mai cike da ɗunbin hikima na anfanuwa, ina yi maka bangajiya Nur, jiya Network ne ya ruke ni
A wannan satin ma, Maryam Haruna da Hauwa'u Muhammad, cikin shirinsu na 'Filin Bakonmu Na Mako,' za su tattauna ne tare da wani hazikin marubuci, Nuraddeen Isma'il.
Ku biyo mu a cikin shirin ranar Talata 23 March 2021 da karfe 7 zuwa 10 na yamma.
Ummyter Abdallah
(owner)
Madam din Dana kewa aiki jiya ta aikeni na sayo mata semo 2kg,danaje shagon sai na tarar sai 1 kg,so na dawo ban sayo ba shine tace min ni Wawa ne bana amfani da hankalina na sayo 1kg guda biyu ya zama 2kg Kennan idan an hada,na bata hakuri dai ta hakura,yau kuma tace na sayo mata slippers number 8,danaje babu sai lamba 4 shine na sayo lamba 4 guda biyu,na kawo batace komai ba Naga tana hada mini kayana cikin jaka,shine nake tambaya ko wanki zatayimin koko daki zata canjamin🤪🤪🤪
Attending
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham
Cinikin mutum ake kamar yanda ake cinikayya a kasuwa,farashi suke yanke wa kamar yanda ake yi a super market,basa yin ragi balle su nuna alamar sauki,idan ka biya kudi su baka,idan ka ki biya su kasheshi.
Basa tsoron kowa,balle su yi tunanin akwai wanda zai iya tunkararsu,dole akwai abin tsoro fa,kasar nan ta mu akwai firgici sosai,Ya Allah ka karemu daga wannan masifar ta satar mutane.
Allah ka bamu lafiya da zama lafiya amin
Awaiting Reply
faridat sweery
ASSALLAMU ALAIKUM
ƘUNGIYAR TALLAFA WA MARAYU DA NAKKASSASU NA JIHAR BAUCI.
Tana mika Ƙoƙon bararta, na neman sadakan gero da suger ko da kuwa, mudu dayane. domin kai kunun buɗa bakin azumin ramadan wa majinyata marasa ƙarfi da suke asibiti.
Ga waɗanda basa kusa, za su iya turo taimakon su ta wannan ɗin. account number:0027086589.
account name: kungiyar talafawa marayu da nakkassasu. Bank stanbic ibtc.
domin ƙarin bayani:...
Aisha Ahmed:08039344770
Farida Musa:08100564048
Mardiya Afullati...:08062264964.
forwarding ma sadakane. Allah ya ba da ikon taimakawa, sadaƙa bata kaɗan.
Awaiting Reply
hauwa Muhammad
HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION.
Saudat
Na
Hauwa Kele (Maman Sadiq
Page 6
Ba wacce ta kula shi bare ma su ba shi amsa, cigaba da tafiya suka yi, shi kuma ya bisu da kallo, ya aiyana aran sa "Dole ma in nemo gidan su don ina da muradin ki kasan ce mata ta in sha Allah," Juyawa ya yi ya koma gurin motar sa.
Cikin sauri suka shigo rike da hannuwan su, suna shigowa suka tarar da Ummansu tare da Mama a zaune tsakar gida suna fira da sauri suka ƙaraso Umma ce ta fara faɗin, "Kai! Lafiyar ku kuka faɗo gida babu ko sallama? Bisa tabarma suka zauna
Maryam ce taba Umma labarin abin da ya faru.
Sai lokacin Mama ta yi magana, "Shi ne kuka faɗo rike ce haka, tun da har motar ba ta buge ku ba sai ku kiyaye ku riƙa lura da hanya."
Tana gama fadar haka ta ta shi tashiga kicin.
Umma ko cewa ta yi "Alhamdulillah tun da dai bai taɓa ku ba Allah kuma ya kiyaye gaba."
A tare suka amsa da Amin
"Wai Umma su Rashida ba su dawo ba ne? Saudat ce ta yi tambayar.
"E ba su dawo ba, abincin ku na kichin."
Saudat na kwance sai juyi take yi, hankalin ta da tunanin ta yana gun Affan, irin mijin da take so kenan, adu'ar ta Allah yasa ita yake so.
********
"Na rantse da Allah sai an ba ni kuɗi na ba in da za ni sai kin ba ni don bance kici min awara ba ba ki da kuɗi."
Riƙe take da kunkuru tana karkaɗa shi sai wani murguɗa baki take yi wai ita masifaffiya.
Wata dattijuwa dake zaune bakin kan tabarma cikin rumfa ta ce "Haba dije! ke wai kowa bazaki ragama ba, sai masifa sai ka ce masifa abin kwarai ce."
dattijuwar zata yi shekaru hamsin da biyar, wani barmaɗa ido Dije ta yi sannan ta ce "Ai sai ki biya mata tun da masifa ta kike gani, duk wanda yaci kayana dole ya biya ni, inba haka ba inshuka ma mutum rashin mutunci ehe." Takara she maganar tana gyara daurin ɗamarar ta.
"Wai ke laure meyakaiki cin bashin wannan yarinyar? Bayan kin san Halin ta."
"Gwago ni ba bashi na ɗauka ba jiya na saye awara ta ashirin, na ba ta dari biyu ba ta da chanji shi ne ta ce min indauka inta dawo daga talla ta zo ta karbi kuɗin ta, jiya ta zo ba ta same ni ba shine fa yanzu tabugo min wannan sammako a kan naira ashirin."
Tana gama bayanin Bello na shigowa, da ma shi ta aika ya siyo mata shuga.
"Kar bi ga kuɗin ki marar mutun ci kawai."
Ba kunya ta karba tana faɗin "Zaki saya anjima in kawo miki? Ɗaki tashiga ba ta ma tsaya jin abin da take faɗa ba, gwago ko cemata ta yi "Ko kafar ki nagani gidan nan sai na karya ki marar kunya kawai."
"Wai ke Shafa baki girka komi ba ne yau?
"Ba sai ka kawo ba zan girka" komai ba ni da shi a cikin gidan nan."
"Kinga kije gidan Yaya Umaru ki samo ko wake ne ki dafa mana." Bata kula shi ba gyara kwanciyar ta kawai ta yi.
"Wai bazaki ba ne ki ka wani gyara kwanciya."
"Ba za ni ko ina ba Iro idan kana fitar da kuɗi ka fitar, yau Iya Mariya kwananta biyu, ko koko bamu kai mata ba, ka dai ji kunya wallahi." Tashi ta yi ta koma ɗaki tabar shi nan sai faman hamma ya ke yi saboda yunwa ga kuɗi amma bazai ci ba.
Kele
Awaiting Reply
Maryam Haruna
A rayuwata babu abin da nake so kamar kallon finafinai na tsoro da firgici hakan na min daɗi sosai wanda hakan yasa ko kallo zan yi bana kallon wanda na san babu wani abu da zai firgita mutane. Ko a makaranta abokan karatuna duk sun san wannan hali nawa,wani lokaci su kan bani shawara a kan in bari kada wani abu ya faru da ni amma da rana ɗaya ban taɓa sauraronsu ba tunanina ma yanda zan sa musu son fara kallon irin finafinan da nike yi ƙila hakan zai sa su fahimci abin da nake nufi da son waɗan nan abubuwan. Mu uku muke ɗakinmu na makaranta,kullum cikin hana ƴan ɗakinmu bacci da hayaniya in Ina kallo. Sun yi duk yanda zasu yi don hanani wannan ɗabi'ar amma hakan ya faskara,don bani da lokacin da nake jin daɗin kallon fim ɗin tsoro sai sha biyu na dare.
Ashe ƙaddara ce ke bibiyata ban sani ba. Wata rana daga makaranta aka kai mu asibitin mahaukata wacce ke bayan gari kusa da maƙabarta.
Na ji daɗi sosai don wasu finafinai da nike kallo yawanci a asibitin mahaukata ake bada tsoro duk tunanina tunda mun zo hakan zata faru ga waɗan da muka zo tare don ni bana saka kaina saboda ni na san na saba kallo to tsoron mi zan ji kuma.
Ranar da ba zan manta da ita ba ita ce: bayan satinmu guda a asibitin ranar ina aikin dare sai na dinga jin kamar ana kuka sannan ana jan wani abu kamar ƙarfe cikin wani ɗaki da ke kusa da inda nake zaune. Wata mata ce ciki wacce tun da muka zo asibitin magani ko abinci kawai ke sa a buɗe ɗakin saboda yanda take duk wanda ya shiga ɗakin ƙoƙarin kashe shi take yi hakan yasa aka daina zuwa wajenta sai dole. Da farko na share saboda na san matar da ke ciki zata iya yin komai duba da yanda ciwonta yake amma kuma sai na ji abubuwan sai ƙaruwa suke yi,wata zuciya na cewa na duba wani gefen na gargaɗina a kan kada na je. Da dai na ji abin ya wuce tunanina ƙarar sai damuwata take yi hakan yasa kawai na tashi don zuwa ganin menene.
Ina tashi sai wutar ɗakin ta dinga rawa kamar zata ɗauke. Ban damu ba na kunna fitilar wayata don in gani da kyau. Tura ƙofar ɗakin na faɗa ba tare da jiran wani abu ba,abin da na gani ne ya kusan sani sumewa. Wata halitta ce kusa da matar nan tana mata wani abu da na kasa gane meye matar dai kwance take kamar babu rai tare da ita wannan halittar sai zuƙar jinin jikinta dake ta malala ƙasa kamar ruwa .
Hakan da na gani ya mugun tsoratani har ban san na saki wayata ba ashe dai duk rashin ganin tsoron da nake cewa bana shaci daɗi ne don ban gani a zahiri bane, ƙarar faɗuwar wayar yasa wannan halittar ta juyo inda nake cikin sakan ɗin da bai wuce goma ba na ƙare mata kallo. Ƙaton kai ne da ita kamar ƙwllo,wuya kuma ba kauri sai kace mariƙar lema. Ido guda gareta kuma a tsakiyar kai yake, ƙafafuwanta sun kusan shida ga wani gashi da ya rufe mata jiki wanda ya ƙara maidata abin tsoro.
Ganin ta juyo inda nake yasa da sauri na zabura da gudu zan bar ɗakin ai kafin ƙyaftawar ido na ga ta kusa zuwa inda nake ban yi ƙasa a guiwa ba na ƙara azama wajen gudun da nake son yi. Ita ma kokarinta ta zo inda nake don lahanta rayuwata na yi gudu sosai kaɗan ya rage in buɗe ƙofar fita baƙi ɗaya sai kawai na ga kare bakin ƙofar gashi ya buɗe baki da alama jira yake na ƙaraso wajen shima ya illatani. Ganin haka na yi shahada tare da canja waje zuwa makewayin dake ɗakin sai dai me kafin in kai na hango wani mutum mai mugun tsawon da duk iya ganina na kasa ganin ƙarshensa,gashi kayan jikinsa baƙi wuluƙ da dai na rasa yanda zan yi kawai sai na rufe idona ina jiran mai faruwa ta faru. Ban san me ya faru ba sai dai na buɗe ido na ganeni kwance saman gado an ɗaureni da igiyoyi a yanda na ji ana magana wai sati na guda kenan da haukacewa kuma duka nake yi don haka aka ɗaureni yanzu haka mafita nake nema yanda zan faɗa musu cewar ba hauka nake ba.
Awaiting Reply
Auwalu Adamu Sabongida
Assalamu alaikum
Da fatan dukkan jama'ar wannan gida su lafiya?
Mun shigo don karuwar Ilimi.
Awaiting Reply
Abubakar Saleh (Zamani Writers Ass.)
*Baby Khausar Complete Document*
_Na Layuza Kabir Adam_
Domin sauke littafin a wayarku Danna Kan hoto ko blue din rubutu dake kasa
👇🏼👇🏼👇🏼
http://www.aihausanovels.com.ng/2021/02/baby-khausar-complete-document.html
Like our Facebook page Fb.me/Aihausanovels