Events » Hira da Baki » BAKONMU NA MAKO: Tattaunawa da Hashim Abdallah

Event Details

 • A wannan satin ma, Maryam Haruna da Hauwa'u Muhammad, cikin shirinsu na 'Filin Bakonmu Na Mako,' za su tattauna ne tare da wani hazikin marubuci, Hashim Abdallah.

  Ku biyo mu a cikin shirin ranar Talata 6 April 2021 da karfe 7 zuwa 10 na yamma.
 • 4/6/21 at 5:00 PM -
  4/10/21 at 12:00 PM
 • Where
  Taskar Bakandamiya Map
 • Host
  Zauren Marubuta
 • Led by
 • Category
 • RSVPs
  • 4 attending
  • 2 maybe attending
  • 0 not attending
  • 720 awaiting reply

Updates

 • musa Idrisjakara
  musa Idrisjakara joined the event BAKONMU NA MAKO: Tattaunawa da Hashim Abdallah
  Mon at 4:25 PM
 • Usama Shuaibu Goma
  Usama Shuaibu Goma joined the event BAKONMU NA MAKO: Tattaunawa da Hashim Abdallah
  Apr 23
 • Mukhtar Musa Karami Abu Hisham
  Mukhtar Musa Karami Abu Hisham joined the event BAKONMU NA MAKO: Tattaunawa da Hashim Abdallah
  Apr 8
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  Alhamdulillah! Duk wasu tambayoyi da aka yiwa baƙo ya samu damar amsawa cikin ƙwarewar basira, mun ji daɗin haka sosai. Yanzu idan akwai waɗan da ke kusa kuma suke da tambaya ga baƙo a shirye yake don amsawa.
  Apr 7
 • Rahmatu Lawan
  Rahmatu Lawan joined the event BAKONMU NA MAKO: Tattaunawa da Hashim Abdallah
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  25. WACE SHAWARA ZAKA IYA BA ƘANANAN MARUBUTA MASU TASOWA YANZU?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  24. KO KANA DA WATA GUDUNMAWAR DA KAKE GANIN ZAKA IYA BAYARWA DON INGANTA RUBUTUN LITTAFAI?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  23. WANNE IRIN CI GABA NE KAKE GANIN AN SAMU TA FUSKAR ADABIN HAUSA WANNAN ZAMANIN?
  Apr 6
  • Maryam Haruna
   Hashim Abdallah Yanzu ana samun gasanni, ana yin fina-finai da labarai wadda harka ce da ta fi kawo abin kashewa. Masu ilimi mai dan zurfi suna yin rubutu, wadanda suka karanci Turanci suna fuskantar fara rubutun Hausa din, wanda a baya ba su damu da shi ba.
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  22. AKWAI WATA ILLA DA KAKE GANIN AN SAMU SANADIYYAR RUBUTUN LITTAFAI?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  21. AKWAI WATA HANYA DA KAKE GANI ZA A IYA BI DON GANIN AN ƘARA SAMUN CI GABA A RUBUTU?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  20. AKWAI BANBANCI TSAKANIN MARUBUTA NA YANAR GIZO DA KUMA NA KASUWA?
  Apr 6
  • Ummyter Abdallah likes this.
  • Maryam Haruna
   Hashim Abdallah Wadancan a kasuwa suke yi, wadannan kuma a yanar gizo. Wadancan ba tacewa wadancan hukuma takan tace. 'Yancin yanar gizo yana da yawa, wadancan sai an tace musu basirar ta daidaita da al'umar da suke cikinta wadancan ruwansu ne.
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  19. A MATSAYINKA NA MARUBUCI, SHIN AKWAI WASU MATAKAI DA MUTUM YA KAMATA YA BI IDAN YANA SON ZAMA MARUBUCI?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  18. KA TAƁA HALARTA WANI TARO NA MARUBUTA?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  17. WAƊAN NE IRIN TARIN NASARORI NE KA SAMU SANADIYYAR RUBUTU?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  16. KANA DA UBAN GIDA A RUBUTU?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  15. ONLINE WRITER NE KAI KO KUWA?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  14. YANA ƊAUKAR KA TSAWON WANE LOKACI KAFIN KA KAMMALA LITTAFI?
  Apr 6
  • Ummyter Abdallah like this.
  • Maryam Haruna
   Hashim Abdallah Ya danganta da irin wanda na dauko rubutawa. Gajeren labari dai a rana daya ne. Amma gyare-gyare da fadadawa da kammalawa ba su da lokaci takamaimai har sai na gamsu ko da kuwa zai dauki lokaci mai tsayi sosai.
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  13. A CIKIN LITTAFI ME YA FI MAKA WAHALAR ƘIRƘIROWA? SUNAYE, GARURUWA, SIFFOFIN MUTANE DA SAURANSU?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  12. SHIN DAGA INA KAKE SAMUN IDEAS NA ƘIRƘIRAR LABARI?
  Apr 6
 • Maryam Haruna
  Maryam Haruna:
  11. KA TAƁA FUSKANTAR WANI ƘALUBALE A FARA RUBUTUNKA?
  Apr 6
  • Ummyter Abdallah like this.
  • Maryam Haruna
   Hashim Abdallah Da yawa; rashin kudin bugu, kasa yin littafi na farko bisa yadda ya dace bayan na san yadda ya dace saboda rashin kudi. Ina nufin na kasa saka ISBN da samar da hakkin mallaka a hukumance. Rashin samun horo ko wanda zai ba ni horon kan rubutu da sauransu...