Idan mutum ya manta bai wanke wata cikin gabobin alwala ba, to in ya tuna a kusa zai wanke wannan gabar da sauran kabobi bayan sa. Misali: Mutum ne yayi alwala, sai ya manta bai wanke hannun hagu ba, amma ya wanke na dama, ya shafa kai da kunnuwa, ya kuma wanke kafa, sai ya tuna bayan wanke kafafunsa. To zai koma ya wanke hannun hugun, ya shafa kai da kunnuwa, sa'an nan ya wanke kafafunsa.
Idan kuma bai tuna ba har lokaci ya tsawaita, to zai sake alwalar ne gaba daya.