Forums » Sallah

Yaya zan cika sallah idan wasu raka'o'i sun kubuce mini?

    • 8 posts
    December 13, 2018 12:29 PM GMT
    Malamai sun yi mana bayani cewa idan wasu raka'o'i suka kubucewa mutum a sallah, to idan zai kawo su bayan liman ya yi sallama, cikawa zai yi. Misali, idan raka'o'i biyu (wato na karshe) suka kubucewa mutum a sallar Azahar, to idan zai cika, zai dauke su ne tamkar raka'o'i na karshe, wato sai ya karanta Fatiha kawai, bawai zai karanta sura da fatiha ba. Anan ya nuna, duk raka'o'insa hudu sun zama fatiha ne kawai babu sura.

    Tambaya anan shine: Na tashi zan kawo sauran raka'o'i biyu din, da na kawo na farko, sai na manta na karanta Fatiha da sura. Shin idan zan kawo na biyu din (na karshe), zan kawo shi ne babu Fatiha, ko kuwa zan kawo shi da Fatiha da sura don su zama daya da na farko da na kawo?