Forums » Azumi

Tambaya akan azumin watan Rajab

  • 4 posts
  March 21, 2019 8:20 PM GMT
  Assalam alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu malaman wannan gidan,

  Mene ne ingancin azumin da ake yi a watan Rajab domin kima da darajar wannan watan? Shin sunna ne, ko kuwa? Don Allah a taimaka malamai da amsar wannan tambaya da kuma hujja
  This post was edited by Rahmatu Lawan at March 21, 2019 8:28 PM GMT
  • 1 posts
  March 22, 2019 9:52 PM GMT
  KARIN BAYANI AKAN AZUMIN RAJAB.DOMIN AN SHIGAR DA BID'O'I CIKI.
  Amma ware ai nufin shi watan rajab d’in da nufin fifita shi ko bashi wata matsayi ta musammam?haqiqa
  wannan ba daidai bane.
  Nana Aisha (RA) ta ce:
  “Manzon Allah (SAW) ya kasance yakan yi
  Azumi, harsai mun ce ba zai ajiye ba, kuma
  yakan ajiye azumi har sai mun ce ba zai yi
  azumin ba, kuma ban tabaganin Manzon Allah ya
  cika azumin wata ba face Ramadan, sannan ban
  ga watan da Manzon Allah yake yawaitaazumi a
  cikinsa ba kamar sha’aban”.
  [Ahmad ya ruwaito

  Shehun muslunci Ibn Taymiyya yace acikin
  littafinsa Majmoo’ al-Fataawa
  Akan maganar azumtar Rajab, gabad’ayan
  hadisan da suke magana akan haka daeefai ne,
  sanan kuma maudooai domin ma’abota sani basu
  dogara daga d’aya daga cikinsu ba. Basa daga
  cikin hadisai daeefai da suke magana akan
  falala. Bayaga kawai mafi yawa daga cikinsu
  qarya ce da qage kawai.
  Acikin al-Musnad da sauran wurare da akwai
  hadisi dake cewa Manzon Allah (s.a.w) yana jin
  dadin azumtar watanni masu falala, sune:Rajab,
  Dhu’l-Qa’dah, Dhu’l-Hijjah daMuharram, kuma
  wannan sai ya had’a da sauran watannin bawai
  ware rajab shikad’ai ba.

  Ibn al-Qayyim (Allah yaqara masa yarda) yace:
  Gabad’ayan hadisin dake magana akan azumtar
  watan rajab da yin sallah acikin wasu daga cikin
  dararen sa duk qarya ne da qage.
  Daga littafin al-Manaar al-Muneef,
  Haafiz ibn Hajar yace acikin Tabyeen al-‘Ajab

  Babu wani saheehin hadeethi da za’a qirga a
  matsayin hujja akan falalar azumtar watan rajab,
  ko wani vangare nashi ko kuma sallace tsawon
  wani dare nashi.
  Shaykh Sayyid Saabiq (Allah ya qara masa
  yarda) yace acikin Fiqh al-Sunnah
  Azumtar rajab baifi azumtar sauran watanni ba,
  face kawai yanadaga cikin watanni mai falala. To
  babu wani bayani acikin saheeh sunna dake nuna
  wani abu muhimmi akan azumtar watan, haka
  duk wani abu da aka ruwaito dangane da wannan
  to baikai daidai da za’a daukeshi a matsayin
  hujja ba.

  Shaykh Ibn ‘Uthaymeen (Allah ya qara masa
  yarda) an tambaye shi game da azumtar ashirin
  da bakwai na watan Rajab da sallatar wanan
  dararen sai yace:
  Azumi a ishirin da bakwai d’in watan rajab da
  sallatan daren bidi’ah ce sanan dukkan bidi’ah
  kuma vata ce.
  Allah ya taimakwmu.
  • 4 posts
  March 22, 2019 10:11 PM GMT
  Masha Allah! Madallah da wannan amsar ta ka, Mal. Farook. Allah Ya kara basira Ya kuma sa mu a hanya madaidaicoya. JazakAllah khair