March 30, 2019 11:28 PM GMT
Assalamu alaikum.
Dan Allah inason insan yadda zanyi posting saboda inason in dinga yi Domin taimako junan mu.Nagode
March 31, 2019 5:39 PM BST
Wa'alaikum Assalam Abubakar,
Kamar yadda ka gani, anan sashen Tambayoyi kowa na iya posting tambaya ko amsa tambayar wani. Kawai saidai ka dubi Topic da ya fi dacewa da tambayarka ko kuma bayananka. Game da posting na makalu ko bidiyo da kuma makamantansu, zaka iya aiko mana da sako ta hanyar zuwa bangarenmu na "Tuntube mu." Idan editocinmu suka duba to za su yi posting maka ko su baka damar ka yi posting. Mun gode.
April 1, 2019 5:40 PM BST
Yauwa madallah. Mu ma mun gode.