Forums » Doughnuts

Mene ne ke hana doughnuts tashi da laushi?

  • Moderator
  • 1 posts
  April 8, 2019 5:59 AM BST


  Assalamu alaikum

  Ga dalilan da ke sa doughnut ya ki tashi ko ya lalace kamar haka:

  1. Saka sugar da yawa yana hana dough din doughnut tashi.

  2. Amfani da yeast wanda ya lalace ba tare da kin yi proof na yeast din ba yana lalata dough ya ki tashi (ga 'yan Nigeria, Royal Yeast ya fi ko wane kyau).

  3. Ajiye yeast ya dade yana sa activeness din shi ya fita.

  4. Saka butter da yawa yana lalata dough. Za ki iya skipping saka butter dan kar ya lalace maki

  5. Saka dough a rana yana sa ya yi tsami duk da zai yi saurin tashi, ki ajiye dough din ki ko na miye a cikin wuri mai dumi kawai.

  Za a iya duba yadda ake doughnuts ta hanyar latsa link mai zuwa:

  https://www.bakandamiya.com/blogs/1434/1154/yadda-ake-hadin-doughnuts