Forums » Sallah

Shin zan iya cika sallana ta la'akari da wani mamu kusa da ni?

    • 7 posts
    April 9, 2019 11:47 AM BST
    Na zo ne na tarar da an tsere mini da wasu raka'o'i a sallah. Amma lokacin da na zo akwai wasu ma da muka iso tare.

    Kafin liman ya yi sallama, sai na shiga kokwanton yawan raka'o'in da yakamata na biya bayan liman ya yi sallama.

    Sanin cewan akwai wadanda muka shiga sallan tare da su, shin zan iya la'akari da nawa suka biya don na biya tawa? Misali nake yin dan jinkiri wajen gudanar da nawa gabobin sallar har sai sun yi na su tukun da haka har na kammala tawa?