July 21, 2019 9:31 AM BST
To, Malam akwai irin littafi guda biyu. Na farko dai littattafan addini. Sun shiga ?asar Hausa tare da zuwan addinin musulmanci wato tare da zuwan larabawa. Na biyu fa akwai littattafan da ake rubuta da ba?a??en turawa. An fara rubuta su a shekara 1854. Sunan wannan littafi "Polyglotta africana" na Sigismund Kölle. A wannan littafi ake samun kalmomin hausa. Cikin 1885 an wallafa "Magana Hausa" na James Frederic Schön. Akwai tatsunyoyi da karim magana da sauransun da ya rubuta a harshen Hausa a ciki. Cikin 1934 Muhammad Bello Kagora ya rubuto littafi (novel) "Gandoki". Shi ne farkon novel ?in da aka rubuta a harshen Hausa. Shi ke nan.