Forums » Al'adun Hausawa

Tarihin shigowar boko kasar Hausa

  • July 16, 2019 6:38 AM BST
    A wani shekara ko kuma karni na nawa ne book ta shigo kasar Hausa
    • 1 posts
    July 21, 2019 9:31 AM BST

    To, Malam akwai irin littafi guda biyu. Na farko dai littattafan addini. Sun shiga kasar Hausa tare da zuwan addinin musulmanci wato tare da zuwan larabawa. Na biyu fa akwai littattafan da aka rubuta da bakaken Turawa. An fara rubuta su a shekara 1854. Sunan wannan littafi "Polyglotta africana" na Sigismund K lle. A wannan littafi ake samun kalmomin hausa. Cikin 1885 an wallafa "Magana Hausa" na James Frederic Schon. Akwai tatsunyoyi da karim magana da sauransun da ya rubuta a harshen Hausa a ciki. Cikin 1934 Muhammad Bello Kagora ya rubuto littafi (novel) "Gandoki". Shi ne farkon novel din da aka rubuta a harshen Hausa. Shi ke nan.


    This post was edited by Bakandamiya at April 16, 2021 12:35 PM BST
    • 7 posts
    August 18, 2019 9:36 AM BST
    Mashaa Allah! Mun ko karu matuka da wannan tambaya da kuma bayani. Allah Ya saka da alkhairi.