Forums » Sauran hukunce-hukunce

Hukuncin yin huduba ga yaron da aka haifa

  • Moderator
  • 81 posts
  September 14, 2019 9:45 AM BST
  Tambaya:

  Assalamu alaikum malam

  Dan Allah ina neman karin bayani akan hudubar suna da yadda ake yi.
  • Moderator
  • 81 posts
  September 14, 2019 9:48 AM BST
  Amsa:

  Wa alaikum assalamu

  Game da kiran sallah da ikama a kunnen yaron da aka haifa wannan bai inganta ba, saboda hadisin kiran sallah Tirmizi ya rawaito shi da sanadi mai rauni.

  Baihaki kuma ya rawaito shi a Shu'abul-imani sai dai a sanadinsa akwai maruwaita guda biyu wadanda ake tuhumar su da karya, amma hadisin da ya zo akan yin ikama kuwa, to malamai sun ce hadisi ne na karya.

  SAI DAI YA TABBATA A SUNNAH ANA TAUNA DABINO A SAWA YARO A BAKI.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa:

  DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
  31/12/2013