Forums » Sallah

Ina so na yi tsayuwar dare, ammma na gaza?

  • Moderator
  • 63 posts
  September 14, 2019 10:08 AM BST

  Tambaya:

  Assalamu Alaikum

  Malam ina sha'awar yin tsayuwar dare saboda dimbin falalar da ta kunsa, saidai a lokuta da yawa, na kan so na tashi, amma sai na kasa, ko malam zai taimaka min da shawarwari akan abin da zai taimake ni wajan yin wannan babban aikin, Allah ya karawa malam daukaka, amin.

  • Moderator
  • 63 posts
  September 14, 2019 10:09 AM BST

  Amsa:

  Wa'alaikum assalam

  To dan'uwa ina fatan Allah ya datar da mu gaba daya zuwa wannan ibada mai girma, akwai abubuwa da malamai suka yi bayanin cewa, suna taimakawa wajan samun damar tsayuwar dare, ga wasu daga ciki:

  1. Baccin rana: Hasanul Basary ya wuce wasu mutane a kasuwa da rana, sai ya ce wadannan ba za su yi bacci ba, sai aka ce masa E, sai ya ce ina ganin darensu ba zai yi kyau ba".
  2. Yin bacci da wuri, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karhanta bacci kafin sallar isha da kuma yin hira bayanta, kamar yadda ya zo a hadisin Muslim mai lamba ta: 647, kuma dalilin da ya sa ya karhanta hin hira bayanta saboda hakan zai iya hana mutum tsayuwar dare.
  3. Aikata ladubban bacci yayin kwanciya, ta yadda zai karanta abin da ya zo a cikin sunna na ladubban bacci.
  4. Umartar wani ya tashe shi kamar matarsa ko wanda suke tare.
  5. Rashin cika ciki da abinci.
  6. Nisantar yin aiki mai wahala da rana.
  7. Nisantar abin da zai kawo maka fargaba a cikin zuciya, ta hanyar rage burirrika da tunanin abin da ya wuce
  8. Nisantar zunubai, Fudhail bn Iyadh yana cewa: "idan ka ga ba ka iya tsayuwar dare, to ka tabbatar zunubai ne suka dabaibaye ka

  Allah ne mafi sani

  Amsawa:

  Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

  25/11/2014


  This post was edited by Bakandamiya at September 14, 2019 10:12 AM BST