Forums » Tsarki

Na ga wandona a jike da maniyyi bayan na kammala sallar la'asar

  • Moderator
  • 81 posts
  September 14, 2019 10:23 AM BST

  Tambaya:

  Aslamualaikum Malam

  Na tashi da janaba nayi sallar asuba da azahar da kuma la’asar, duk nayi sallah. Sai bayan na je wanka da yamma na ga wandona da alamun maniyyi. Shin sallalina n abaya sun inganta? Na gode.

  • Moderator
  • 81 posts
  September 14, 2019 10:24 AM BST

  Amsa:

  Wa'alaikum assalam

  Mutukar ka tabbatar a baccin asuba maniyyin ya fito, to ya wajaba ka sake asuba da azahar da la'asar din.

  In har ka yi wani baccin bayan azahar to za ka danganta janabar ne zuwa ga baccin karshe da ka yi, ta yadda sallar da ka yi bayan baccin karshe ita za ka sake, kamar yadda Imamu Malik ya rawaito a Muwadda daga Sayyady Umar.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa:

  Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

  13/11/2017