Forums » Sallah

Zan iya sallar nafila a lokacin tafiya?

  • Moderator
  • 81 posts
  September 14, 2019 1:02 PM BST

  Tambaya:

  Assalamu alaikum.

  Malam tambaya ta ita ce yaya hukuncin yin nafila yayin da mutum a halin tafiya wato yanayin kasaru, naji wasu malaman suna cewa ba'ayin nafila a yanayin kasaru don Allah malam ina bukatar amsa da gaggawa.

  Na gode.

  • Moderator
  • 81 posts
  September 14, 2019 1:03 PM BST

  Amsa:

  To dan'uwa, abin da aka rawaito idan Annabi ? ya yi tafiya, yana barin nafiloli, in ba wutiri da raka'atanil fijr ba, kamar yadda Ibnul-kayyim ya ambata a littafinsa na Zadul-ma'ad 1\456.

  Wasu malaman suna ganin nafilolin da suke da alaka da sallolin farilla su ake bari, amma wadanda ba su da alaka da sallolin farilla kamar tsayuwar dare an iya yinta, an samu halaccin hakan daga Imamu Ahmad. Zadul-ma'ad 1\457.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa:

  Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

  14/09/2019

  • 1 posts
  September 18, 2019 11:08 AM BST
  ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI MALAM