Forums » Tsarki

Haila ta same ni bayan mijina ya sadu da ni

  • Moderator
  • 81 posts
  September 19, 2019 12:04 PM BST

  Tambaya:

  Assalamu alaykum, Malam ina da tambaya

  Mace ce bayan mijinta ya sadu da ita, kafin ta yi wanka sai jini  ya zo mata. Yaya za ta yi wanka? Shin gaba dai za ta yi niyya ko kuma wannan na biyun za tayi?

  • Moderator
  • 81 posts
  September 19, 2019 12:05 PM BST

  Amsa:

  Wa alaikum assalam

  Za ta jira in ta samu tsarkin haila sai ta yi wanka daya kawai.                           

  Yana daga cikin ka'idojin SHARIA Idan ibadoji guda biyu suka hadu, kuma manufarsu ta zama guda daya, sannan za'a iya hada su a lokaci guda, to sai daya ta shiga cikin dayar.

  Wannan yasa mai janabar da jinin haila ya same ta kafin ta yi wanka, za ta wadatu da WANKAN karshe, saboda saukin Musulunci da kuma daukewa jama'a abin da zai kuntata musu, kamar yadda aya ta karshe a suratul Hajj ta tabbatar da hakan.            

  Allah ne mafi Sani.

  Amsawa:

  Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

  4/11/2016