Forums » Sallah

Nayi sahu jere da liman. Yaya sallah ta?

  • Moderator
  • 81 posts
  October 16, 2019 6:14 AM BST

  Tambaya                                   

  Assalamu alaikum warahmatullah

  Allah ya karbi ayyukan alkhairan da Mallam yake gudanar wa a matsayin ibadah, amin.

  Tambaya ta anan itace, mutum da ya zo ya samu sahun sallah ya cika, sai ya je ya jera da liman a gaban sahun. Shin hakan ya dace? Ina neman Karin bayani.

  • Moderator
  • 81 posts
  October 16, 2019 6:15 AM BST

  Amsa

  To dan'uwa abin da yake sunna shi ne mamu su yi sahu a bayan liman, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisai ingantattu.

  Sai dai idan aka samu cinkoso aka rasa isashshen wurin, to ya halatta mamu ya yi sahu tare da liman, tun da dama yin wancan din sunna ne.

  Duba: Majmu'u Fatawaa wa rasa'il na Ibnu Uthaimin, lamba ta: 419.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  26\8\2015