Forums » Alwala

Zan cire hakorin Makka saboda kaucewa lam'a a alwalata?

  • Moderator
  • 81 posts
  October 16, 2019 6:36 AM BST

  Tambaya

  Malam, da gaske ne da ake cewa hakorin Makka lam'a ne, saboda ruwan alwala ba ya taba ainihin hakorin mutum?

  • Moderator
  • 81 posts
  October 16, 2019 6:39 AM BST

  Amsa

  To malam a zance mafi inganci, bai zama dole ruwan kurkure Baki sai ya game dukkan hakora ba, saboda abin da ake nufi da kurkure baki shi ne zagaya ruwa a baki a fito da shi, don haka hakorin Makka ba zai kawo lam'a ba, amma kuma wasu malaman suna ganin kurkure baki ba zai cika ba sai ruwan ya game, don haka barin sanya hakorin Makka Shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai abin so ne.

  Ya wajaba ga maza su guji sanya hakorin zinare, saboda Allah ya haramta zinare ga mazan al'umar Annabi Muhammad ? kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a Sunan dinsa a hadisi mai lamba ta: 1720.

  Don neman karin bayani duba Alminhaj sharhin Müslim na Nawawy 3/105.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  12/11/2015