Forums » Sauran hukunce-hukunce

Yadda ake warware sihiri

  • Moderator
  • 81 posts
  October 16, 2019 7:01 AM BST

  Tambaya

  Assalamu alaikum

  Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake damuna. Mahaifiyata ce ta je gurin malami don a yi mata naganin ciwon mara da yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun yi scanning sun ce ba komai, to sai malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta, amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan.

  To gaskiya malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne shi yasa na keso ka bani fatawa. Shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen kin biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina da matsala , ta bangaren akida mun banbanta.

  Wassalam na gode malam Allah ya kara basira.

  • Moderator
  • 81 posts
  October 16, 2019 7:02 AM BST

  Amsa

  Wa'alaikumus salam

  To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani. Wasu malaman sun yi bayani cewa, ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta: 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta: 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta: 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai.

  Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.

  Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita cewa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Duk wanda ya je wajen boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba'in," kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2230.

  Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta yarda da ita.

  A wani hadisin kuma yana cewa: "Duk wanda ya je wajen boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi," kamar yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud, hadisi mai lamba ta: 3904, kuma Albani ya inganta shi.

  INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  12\4\2014