Amsa
Wa'alaikum assalam, Mutukar diyyar kisan kuskure ne, to dangi na wajan uba su ne za su biya, saboda hakan zai sa şu hana wawayen cikinsu sakaci da yin abin da bai kamata ba, sannan dangin wanda aka kashe musibar za ta musu sauki, sannan akwai koyawa mutane taimakekeniya a ciki.
Amma Idan kisan ganganci ne to diyyar za ta kasance a dukiyar mai laifin, in har dangin wanda aka kashe sun yarda a biya diyya.
Don neman karin bayani Duba: Makasidussharia Indassa'ady na Dr. Jamilu Zarewa shafi na: 303.
Allah mafi sani.
Amsawa:
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
12/03/2016