Forums » Sauran hukunce-hukunce

Idan aka yi kisan kuskure, wa zai biya diyya?

  • Moderator
  • 81 posts
  October 23, 2019 9:34 PM BST

  Tambaya

  Assalamu Alaikum, Dr.

  Ina da tambaya. Wai lalle ne idan mutum ya kade wani ya mutu idan za'a biya diyya wai duk kudinsa ba'a yarda ya biya shi kadai ba sai an bi dangi an harhado kudin sannan za'a biya?

  • Moderator
  • 81 posts
  October 23, 2019 9:34 PM BST

  Amsa

  Wa'alaikum assalam, Mutukar diyyar kisan kuskure ne, to dangi na wajan uba su ne za su biya, saboda hakan zai sa ?u hana wawayen cikinsu sakaci da yin abin da bai kamata ba, sannan dangin wanda aka kashe musibar za ta musu sauki, sannan akwai koyawa mutane taimakekeniya a ciki.

  Amma Idan kisan ganganci ne to diyyar za ta kasance a dukiyar mai laifin, in har dangin wanda aka kashe sun yarda a biya diyya.

  Don neman karin bayani Duba: Makasidussharia Indassa'ady na Dr. Jamilu Zarewa shafi na: 303.

   

  Allah mafi sani.

  Amsawa:

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  12/03/2016