Tambaya
Assalamu Alaiykum
Malam matata ta haihu sati biyu kenan, to Malam yanzu takan wuni Jini bai zoba sai da daddare in ta kwanta sai Jinin yazo. To shin Malam za ta iya yin wanka/tsarki da safe tayi sallolin Azahar zuwa Isha'i? Kokuma yaya zatayi?
Nagode Allah Yaqara illimi mai albarka.
Amsa
To dan'uwa a zance mafi inganci duk yinin da ta ga jini to yana daukar hukuncin jinin biki ne, haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk yinin da ba ta ga jini ba, Saidai idan yana yayyankewa kusa-kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba ta ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: "Bai sanya muku kunci a cikin addini ba" Suratu Hajj 78.
Don neman karin bayani, duba Almugni na Ibnu Khudaamah 1\214.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
22\2\2015