Forums » Sallah

Daga ina sahu yake farawa?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 4, 2019 6:52 PM GMT

  Tambaya

  Assalamu alaikum malam

  Ya gida ya kuma aiki? Mal don Allah ina da tambaya. Mal sahun sallah kan ta dama za'a fara ne ko ta hagu?

  • Moderator
  • 81 posts
  November 4, 2019 6:52 PM GMT

  Amsa

  Wa'alaikum assalamu

  To dan'uwa sahun da yake bin liman zai fara ne daga bayan liman ma'ana a sanya liman a tsakiya, saboda fadin Annabi ? "Masu hankali daga cikinku, su bi bayana" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 116. Sannan da fadin Anas R.A lokacin da yake bada labarin ziyarar da Annabi ? ya kai gidansu: "Sai muka tsaya ni da marayan a bayansa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 694, daga nan kuma sai a cigaba da cika shi ta bangaren dama.

  Haka nan ake so sahu na biyu shi ma ya kasance, ya fara daga tsakiya ya tafi zuwa dama, saboda fadin Bara'u dan Azib R.A "Mun kasance idan muka yi sahu a bayan Annabi ? mu kan so mu kasance a damansa, ya fuskanto mu da fuskarsa "Muslim a hadisi mai lamba ta: 709.

  Allah ne mafi sani.

  Amsawa

  Dr Jamilu Yusuf Zarewa

  21\2\2015